← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 50

Sashe 5

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan naji sauki na kwaso shardarsa tare da Singlet da boxers Dana kwaso na bashi na Ya Salman ya Sa,Sabulun wanki da Omo na dauka a tsakar gidan na zage na fara wankewa,gashi yamma tayi kowa Yana gida Musa da Salman tare da su Hajiyarmu mamaki ya kamasu, yanda na zage nake dirzar kayan Mahaukaci,Su Salman da Anty suka Shiga sheka min Dariya irin Nima na haukace,Abbu ne ya shigo yaga na wanke farar shadda fari tas Malam tana daukan Ido, faraarsa ta fadada yace ah Lallai yau Ashe Ladan mahaifi ake nema harda yi min wankin Kaya,Ya Musa suka kwashe da dariya tare da cewa Abbu kayan saurayinta ne Mahaukaci take wankewa ta bashi kayan Ya Salman ya canja take wanke nasa,kalli Singlet din da Boxers kalarsu daban,Amma duk inda wannan guy din ya fito masu hannu da shuni ne.

Nan take Abbu ya Bata fuska yace Allah wadaran naka ya lalace ya mace daya tal ta buwayi mutane,Sha shashar banza, na kusa maganinki ya shige daki Yana fada ba ji ba gani,Ni kuwa naci gaba da wankina har Waka nake rerawa.

Bayan kayan sun bushe daf da Magrib na goge su tas,Kuma kamshin turarensa suna jiki Bai fita ba duk sun bulle gidanmu da kamshi, da dare na saci jiki na Kai rigar shagon tela inda kamar kusa ta yaga na bada hamsin aka dinke Dan wurin sannan na gyara ninkin na saka kayan a akwatuna.

Washe gari wajen Ya Musa naje nace ya ranta min dari biyar, da kyar ya bani,na fita na siyi sabulun wanka Giv da soson wanka sabo na saci jiki da kayansa a Leda har brush da komai,Ina fita waje ikon Allah na hangoshi a kofar gidan mu nesa kadan ya zauna a jikin bishiya abin tausayi sai kallonsa akeyi kamar watan Ramadan, Yana ganina ya saki wani Murmushi Wanda bani kadai ba har mazan ya sumar dasu dimple dinsa ya loba kyawawan hakoransa suka bayyana,cike da takunsa na gadara ya nufo inda nake Nima Murmushi na Shiga yi ba tare da na sani ba,kamar me hankali ya karbi ledar Hannuna ya bude ya duba sai Naga ya hade Rai tare da turo Dan lips dinsa, Yunwa kake ji? Na tambaya Kai ya daga min Alamar yaji me nace,Hannuna zai rike na boye hannun nace ba kyau zo mu tafi na Masa da Maganar kurame,Muka jera gwanin birgewa sai labari nake Masa Amma kamar da dutse nakeyi.

Ban tsaya ko Ina ba sai bakin titi shagon aski muka je dashi,da kyar na lallaba ya Shiga Haka Zama a kujerar ma Nasha fama dashi,nace me aski na Yan gayu Zaka Masa Dan kadan zaka rage Masa sumar ka Masa gyaran fuska sosai haka kuwa akayi sai gashi ya Kara wani mugun kyau, nace nawa? Me aski yace kyauta nayi Masa sabo da taimako ne tunda bashi da hankali kuje kawai.

Cike da masifa nace Kai kiyayi kanka Kar ka Kara cewa bashi da hankali wannan da kake gani ya fika hankali da baiwa,yanzu idan da Kaine a matsayinsa ai dukan mutane zakayi Dan kayi Masa aski kyauta shine zaka zage shi ga hamsin Dinka Nan bama son kyautar.

Me aski ya taso da masifa kamar zai mareni Yana kamar ba Ke ba Fadila,kin canja ke da kike me hakuri da kunya ga kawaici Amma akan Mahaukaci kin lalata rayuwarki,idan Baki sani ba ki sani kaf garin Nan ba a kallonki da mutunci zaginki akeyi, tsakiya Bature ya Shiga ya kareni wani kallo ya watsawa me aski sai gashi yayi mukus.
Gidan wasu samari na tsaya nace Dan Asabe Dan Allah ku bashi aron bayinku zaiyi wanka Baki bude suke kallona,Rabiu yace Fadila ko dai kema kin zare ne Taya Mahaukaci zaiyi wanka?,a wajen nace idan zaku bashi ku bashi, daya cikinsu yace wlh kika sake sai na fadawa Abbunki kin San dai halinsa,Nan tsoro ya kamani na tuna dukan Dana ci nace Allah baku hakuri naja Bature muka tafi Rafi da ruwa ke zuwa garai garai.

Da kaina na gwada Masa yanda ake wanka Amma yaki yarda sai na bashi sabulun da soso nayi kamar na tafi na labe a Bayan bishiya,ya Dade Yana tunani sai Naga ya cire kayansa kaf daga shi sai Boxers ya Dan Shiga gefen kogin abin mamaki yayi wankansa tas yanda kowa keyi har ta cikin boxers din Bayan ya Gama ya fito kawai sai na rufe idona Allah yasa wajen ba mutane ya buya Bayan bishiya ya Sa boxers dinsa Dana wanke da singlet,sannan yasa shardarsa Tasha wanki da guga.

Ina kallo yayi aswakinsa tas,sai da ya Gama na dawo, na kwashe kayan daya cire na zuba a ledar.sai Hamma yake da alama yunwa yakeji.
Haka na siyo Masa soyayyar doya da kwai da ruwa na dawo na kawo Masa,hayam hayam ya cinye ya shanye ruwan da gani ya Dade rabonsa da abinci tausayinsa ya kamani,na koma na Kara siyo Masa shinkafa da Miya da wake Nan ma ya cinye tas ya watsar da sauran ya Sha ruwa, sannan nace taso muje yawo kaga gona alama na Masa da hannu ya biyo Ni.
Yana Bina muna tafiya Ina ta Masa labari iri Wanda Bai ko kulani ba.

AsmaBaffa
[9/4, 10:25 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕

3

Official

By
AsmaBaffa

MARCYCOOL, FLOWER,AUTA,ASYCOOL and JANNAT TA SALIM page dinku ne fa.ku kwashe min da tafi😆.

Muna tafiya dashi wani munafukin ya ganmu da sauri ya Kira Abbu a waya ya sanar Masa ga Fadila can sun tafi yawo cikin daji da Mahaukaci,ba tare da na sani ba sai ga Ya Musa tare da Ya Salman a fusace, ya Salman bai jira komai ba ya kifa min Mari har biyu,Dan Bature a hasale ya shaki wuyan ya Salman tare da yarfa Masa Mari sai da jini ya fito ta Hancin Ya Salman,Kuka na fara ya Musa da Ya Salman suka hada karfi da karfe suka fara dukan Dan Bature sosai,Gefen kansa ya fashe jini ya fara tsartuwa,Ni Kuma Ina kuka na Kare Dan Bature Ya Musa ya kawo Naushi ya sameni a Hanci Nan take Hanci na ya fashe jini na fita,Dan Bature Yana ganin haka ya Kara haukacewa ya mike ya Shaki Ya Musa da Salman ya gwara kansu,wani Naushi da yayiwa Ya Musa sai da ya zube har kasa,mutane dake kusa suka fara kawo dauki sabo da Dan Bature yayiwa Ya Salman jina jina Haka ya Musa ma tuni yaci dukan kawo wuka,Mutane da yawa suka taru tare da rirrike Dan Bature dake Huci kamar Zaki,Wata girgiza yayi gaba daya ya watsar da mutanen da suka rikeshi sannan ya Fadi a kasa shi kadai ya fara jijjiga kamar me fyarfyadiya sai dai wannan har wani gurnani ya yakeyi ya dafe kansa,Gigicewa nayi Ina uban kuka Ni Sam Bata su Ya Salman nakeyi ba hankalina Yana wajen Dan Bature,Addua na Shiga tofa Masa tun Yana yi da karfi har ya dawo yi a hankali sannan jikinsa ya saki yayi luf a kasa kwance Nan da Nan bacci ya kwashe shi, lokacin na cire gyalena na daure Masa kansa da Gyalena inda jini ke zuba.

A matukar fusace Salman da Ya Musa suka mike jikinsu duk jini suka fara cin ubana,Bulala suka Sa suka zaneni tas sannan Musa ya sabani a kafada suka tafi Dani giga,Ni Kuma kuka kawai nake Ina kallon Dan Bature cikin jini ya Dan bude idonsa da kyar Jin muryata Ina kuka Ina kiransa Dan Bature Ina Miko Masa hannu,Ya Salman ya lankwashe Hannun da na Mika sai da yayi Kara,na tsandara ihu,Dan Bature Yana yashe a kasa abin tausayi ya bude idonsa Yana kallona bazai iya tashi ba,shima daga kwance ya Miko min hannu,karfin kukana na Kara.

Muna zuwa gida Abbu yau Bai dakeni ba, meeting din gaggawa ya hada tare da iyayensa,Iyayen Hajiyarmu da kannensa sai Kuma Yan gidan namu kaf yaro da Babba, a tsakiya suka sani Ina Hawaye.

Abbu cikin sanyin murya yace Fadila nace Naam Ina kuka,yace na biki ta lallami na biki ta lumana,na fada Miki a tsaye na fada Miki a zaune,sannan jikinki ya Gaya miki, yanzu gashi Ina fada Miki da sanyi karki kuskura na fada Miki da zafi wannan bazai Miki kyau ba,me na rage ki dashi? Kinki aure yanzu Kuma kina bin Mahaukaci,Yar iska kike nema ki dawo? Kai na girgiza alamar A'a, yace to bakya kaunarmu mu iyayenki da Yan uwanki kike aikata haka Dan ki zubar Mana da mutunci? Kai na girgiza, yace dubi Yan uwanki na jini yanda Dan iskan Mahaukacin da kike bi ya aikata musu yanzu dadi kike ji kenan? A hankali nace a'a Amma ai su suka jama kansu tunda sune suka tsokaneshi,Duka Hajiyarmu ta kai min Ana magana bakya ji ko, Abbu yace ai ke ta gado halinki tayo Hadiza munafukar banza ai ke kike zugata,Wai an tabo Fada Nan Hajiyarmu tace yanzu dai da tayi abin Tsiya sai ace iyaye Mata ke zuga yaro,Amma sanda yaro yayi abin kirki baza a taba godewa uwa ba ace anyi tarbiya me kyau sai marar kyau sannan miji zai dinga ganin laifin mace, Yafendo tace ke rufe mana Baki yo ke har wani halin kirki ne da ke,Anty da ke gefe tace badan Allah yasa an aure Ni ba ai da abinda yaran Hadiza zasu yi sai yafi Haka,nice nake sasu a hanyar kirki.

Abbu yace na sani Sarai Allah Miki Albarka Antyn Yara,Hajiyarmu zatayi magana Ya Salman ya Mata alama da ta kyalesu,Yafendo ce tace to Fadila tunda tsiya kike ji muma mun shiryeki aurenki saura sati biyu da Talle Mai lemo,Abbu yace Kuma wlh kika gudu daga garin Nan ban yafe Miki ba na cireki a yarana.
Ihu na Shiga tsalawa Yafendo tace kyayi Kya Gama Nan kowa dake wajen suka rufeni da fada kowa Yana tofa albarkacin Bakinsa, sai da suka Gama nace Wlh na daina hakuri daga yau na Zama marar hakuri da mutunci,tunda Haka ne tantiriya zan koma,Kuma matukar aka bani Talle sai na zuba Masa shinkafar bera.
Baki Kawu Salisu ya tabe yace munga irinku kun fi Dubu sai anyi aure ajiku luf.
Mikewa nayi na fita abina ba tare da an bani izinin tafiya ba.
Chapter 5 · 0% Book details