← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 50

Sashe 46

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Danbaturena ya kwashe da dariya tunda yaga Dr,Mum ta daki Ice a baya Ina ruwanka sashi to Babban banza,Saddiqa Kam sanyi taji a ranta tana Allah yasa ya huce, Bayan Ice da Mum ta duka na Shiga Sosa Masa Ina dariya nace sannu, Dr Bai kula kowa ba Mum kawai ya gaisar ya dauki Saddiqa cak ya zauna a kujerarta ta Dinning sannan ya daurata saman cinyarsa ya fara cin abincinta Yana Bata,Dani da Saddiqa kadai ne kunya ta kamamu kamar zamu nutse Amma Mum da yaranta ko a jikinsu sabo da dabiarsu ta turawa kenan ba kunya ba Kara wannan a jininsu yake.
Ana Gama cin abinci yace Mum mu tafi gida yau ko? Mum tace saifa tayi 1wk wlh kaji na rantse,Ok Mum to ai dai zata rakani mota ko? Ae rako ban hanata ba Amma 3mnt na Bata ta dawo gida nasan ba mutunci gareka ba,dariya mukayi Baki daya,Saddiqa ta mike ta rakashi mota,suna zuwa ya far kalallameta da dadin Baki cewar ta Shiga mota suyi a ciki sharp sharp zaiyi ya tafi Yana cikin wani Hali a matse yake,yanda taga yanayinsa taso ta yarda Amma sai Mum ta danno Kira ta shigo gida,Dole Haka ta bashi hakuri ta tafi ciki,shima ya dawo,Mum tace ka tafi mana ya Naga ka dawo,Baki ya turo gaba yace bazan tafi ba Nima anan Zan kwana na fasa,Nayi mamakin nacin Dr haka, da kyar Mum ta koreshi ya tafi ya sake cewa bazai Kuma zuwa ba gidan har abada,Saddiqa harda kukan tausayin mijinta.

Mum Kuma tace ko me zata yi sai ta Gama gyaran da take mana.
Kwana Nan Kuma yawan zazzabin dare nakeyi,kullum da dare da kyar muke yin bacci da zazzabin nake kwana sosai sai Asuba nake samun lfy.

AsmaBaffa
[9/4, 10:26 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕

86-90

Official

By
AsmaBaffa

Ina matukar Godiya da jinjina muku...
Maman Nusy,Aisha h kunji,Hassana Danja,Mr Mubarak,Ummu sadeeq, Aeesha A Salim,Maman Ameer,Ishkee,Maman Fati,Aishatu Musa gidalo,Deexu,oum Naufal.

Page naku ne
Aisha Humairah,Fancy Honey,Maman Yuseef,Hafsat, Oums Zara and Wasila.

Da sauri na kwaci kaina Ina harararsa da Wasa nace idan aka Kama mu fa? Wai ya akayi alkalin Nan yayi Saurin yanke hukunci haka Kuma yayi me sauki nayi mamaki fa,Murmushi ya saki tare da cewa aiki nane kin San kasar Nan sai da kudi sannan yasan Daddy shi yasa ya saukaka lamarin Amma da har Nanee sai tayi prison wlh bazai daga kafa ba.
Numfashi naja nace Kai duniya Wai Nanee guda,karki ga laifinta Mum ce da laifi ita tasa Daddy koma me ya aikata,ita Kuma Nanee zuciyarta ta fara bushewa da nasan hakan zata faru wlh gidansu Zan Bari ta tafi kawai gashi abin ya girmama, yanzu wanne Namiji ne zai iya Zama da macen da tayi yunkurin kasheshi? Ko ya hakura bazai saki jiki da ita ba,yanzu ban San wanne hukunci Daddy zai dauka ba da nine gaba daya sakin su zanyi.

Kadan na dukesa a kirji baka da kirki kawai yayi hakuri Kar ya sakesu,ka tafi gida kawai sai Gobe,kin ma Isa yarinya tare zamu tafi,nifa bazan bika ba,kwana na nawa rabona dake Dan Allah kizo mu tafi,Hajiyarmu tana Nan Ina so muyi Hira da uwata Ni bazan bika ba,takura min yayi Dole sai na bishi Ni kuwa na sakar Masa kukan shagwaba ba shiri yace ya hakura Amma shima a nan zai kwana gobe sai mu tafi gaba daya. Farin ciki ya kamani nace na gode na gudu ciki na barshi a Nan Yana kirana Amma naki zuwa,yace hmm zaki bayani.

Muna zaune a dakin da aka bawa Hajiyarmu muna Hira wayata ta Shiga ruri na duba Naga sabuwar Number na kirana,banyi niyyar dagawa ba Hajiyarmu tace ki daga mana Dole na daga naji wata Muryar Namiji Yana amsa sallamata,waye pls? Wani masoyinki ne Wanda ya Dade cikin matsanancin kaunarki,Malam wrong number ne Ni Ina da aure, Hmm ai na sani ba kece Fadila ba matar Ice? Nace ae itace,to nafi Ice sonki a sannu sai kin zamo matata Nan da kankanin lokaci zanyi sanadiyar mutuwar aurenki Ni kuma na aureki,Wlh Fadila da gaske kaunarki nake tun farkon ganina dake.
To Ni Kuma bana sonka bana kaunarka wlh ka kiyayeni Dan Babu Wanda nake so ko zanso a duniya sama da Ice,kafin yayi magana na datse wayata na kasheta Baki daya.

Hajiyarmu ta kalleni lfy Fadila? Waye Haka? Wlh ban sanshi ba,kiyi ta Addua to Allah kiyaye sannan ki sanarwa mijinki da wuri Kar ya hada Miki sharrin da za a kasa warwarewa,boyewa mazaje shi ke jawowa a samu babbar matsala ki sanar Masa da wuri.
Hajiyarmu duniya ce ta lalace yanzu da yawa ba tsoron Allah wasu ma su basa harkar nemen Mata sai da masu aure,wasu Matan Kuma basa neman maza sai Sunyi aure yanzu zamanin Nan Allah ne kadai yasan yaran da ake haifarwa wasu mazan suna rikesu a matsayin nasu Wanda Kuma ba nasu bane,
Hajiyarmu tace Ke Kam Fadila kinyi Dace Allah ya taimakeki da samun Miji irin wannan,ki daure ki kula dashi sosai ki Masa biyayya,mijine na gari Aliyu, ki Zama me hakuri da juriya,ki rike addininki, munga rayuwa munji abinda bamu taba sani ba a duniya kamar a film rayuwar wannan gida wlh munyi darasi sosai,naso ace anzo da Anty Amarya itama ta koyi darasi mu hadu mu Kara gyara halayenmu Dan muma muna da laifuka da dama Wanda inshallah zamu gyara mun koyi darasin rayuwa.
Farin ciki ya kamani nace Allah yasa Hajiyarmu,Ameen tace sannan ta Miko min katuwar Leda na kayan gyaran jiki ta fada min yanda zanyi Amfani dasu.

Nace Hajiyarmu Bari naje wajen su Ya Salman muyi Hira sai na dawo,to sai kin dawo ai su Salman sun samu ci gaba ta sanadin aikin da mijinki ya samo musu Murmushi nayi tare da furta ai na gani tun a jikinsu sunyi kyau da Zama Yan gayu ga daukan wanka Haka Ana ta kamshi,jeki kyaji komai daga bakinsu.
Ina Fitowa na Samu Abbu a part din Daddy suna Hira na Shiga wajensu da ladabi na zauna kusa da Abbu nace Abbu zuwa fa nayi na ganka na tafi,dariya sukayi har Daddy, Abbu ya furta jeki gobe zamu hadu.
Allah ya kaimu nace na fita zuwa bangaren Su Ya Salman suna part din Ice, Ina zuwa na samesu tare da Ice suna ta Hira harma da wasu samarin na gidan da Kuma wani Babban abokin Ice wato Alamin,Dr who ma Yana cikinsu Ana Shan hira.
Da sallama na Shiga suka amsa min na tsallake kowa na Shiga tsakiyar Ya Salman da Ya Musa na zauna dama su kadai ne 3seater.
Kawai sai Naga Danbature ya wani hade rai,kamar ban gani ba na shareshi na riko hannun ya Salman nace Ya Salman kuzo muje muyi Hira Mana ko tunawa Dani bakwa yi ai to yau sai mun kwana muna Hira,Dr who yace to anji masu yayye ba inda zasu duk abinda ma Zaki fada musu ki Adana su sai gobe,Ya Salman yayi Murmushi yace tashi ki tafi Ni bana Jin Hira yau,bare Kuma Ni da zanyi waya da sweetyna yanzu bamu da time naki sai gobe.

Shagwaba na fara yiwa ya Salman dama munfi shiri dashi nace pls Ya Salman tare da daura kaina saman kafadarsa,kefa bakya Jin magana bazan iya surutu yanzu ba na gaji ki tafi kiyi bacci sai gobe Kinga ma kusan goman dare ta wuce.
Mikewa nayi ganin Danbature sai fushi yakeyi Bai ce komai ba nasan da wata a kasa na fita da sauri Ina jinsa yace Bari naje na karbo sako wurin Daddy, basu gane ba suka ce sai ka dawo,ya biyo bayana,lokacin nabi ta Bayan corido lungu Ina jiyowa nayi arba dashi na Danji tsoro sabo da wurin akwai duhu kadan Kuma ban San Yana Bina ba,Fisgo Ni yayi da karfi na Fado jikinsa fuskar sa ba Rahma yace kina so mu Bata,me nayi Kuma na tambaya? Akan me Zaki Shiga tsakiyarsu maza ne fa,sannan Baki wani saurareni ba Ni da nake mijinki Zaki je ki daura kanki a kafadar Ya Salman,ba gwara kizo Ni ki daura kanki a jikina ba Amma ko kulani bakiyi ba dan na barki ki kwana anan wlh kika sake tafiya gida zamuyi yanzu.

Baki bude nake kallonsa nace Haba Danbature kasan fa yanda muke dasu Yan uwanane na jini muharramai na,na sani to Ni bana son Haka na fada Miki ma ki sani Ina da kishi,ai dai Yan uwana na ne kuma a Nan dai bazan daina ba sabo da na shaku dasu sai dai kayi ta fushinka.
Haka kika ce? ah to me zance maka Ni ba Wanda zai rabani da Yan uwana ehe,Ido ya zura min kawai yaga yanda nake Masa tsiwa Good ya furta ya juya ya tafi a fusace.
Nima na tafi Ina mita su maza in kana binsu komai kayi ace kayi laifi Haka kawai Ni bazan dauki Haka ba Yan uwa ma sai anyi kishi dasu mene na laifi a Nan fisabilillah.

Ina zuwa wanka nayi tare da Shirin bacci,Hajiyarmu tuni tayi bacci abinta gefenta na kwanta Bayan nayi Shirin bacci na,Number din dazu ce ake ta kirana da ita na daga nace Malam ka daina damuna na gaji wlh bana soka kiyaye na kashe wayar, Ashe lokacin Danbature ya kirani yaji number busy.
Sai Bayan 20mnt ya sake Kira lokacin nayi bacci ya dinga Kira ina bacci sai ya kule naki daga wayarsa.
Dama gashi da Saurin fushi watarana sai ya tunzira ya fara fushi,wasu da dama Haka suke Ana musu biyayya kullum Amma Rana daya idan aka samu matsala to fa babu Uzuri ba a tuna halayen mutum a baya da abin ki rkin da kayi sai laifinka za a kalla na lokacin da kayi.
Chapter 46 · 0% Book details