← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 50

Sashe 44

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da safe Ina da schl da kansa ya kaini tare da saukeni sannan ya wuce Office,2:30pm muka tashi na yi take away na abinci na wuce Prison inda Mum take,dama na fadawa Ice zanje maybe, ban Sha wahala ba aka kirawota inda masu ganin Wanda aka Kama musu suke Zama,Allah sarki ta bani tausayi wlh yanda ta rame gata a wani hargitse tun ba a je koina ba gashi sanadiyar bacin ran an kulleta Hawan jini ya shigeta kullum sai Likita yaje ya duba lafiyarta, tana ganina ta fadada faraarta tana kallo na ta zauna,na durkusa tare da gaisheta,sannan nace Ya jikin Mum? Tace Alhmdllh Fadila,ledojin na Mika Mata nace gashi Mum daga schl nake shi yasa bani na dafa ba,Ba komai Fadila hakanma na gode Kuma kin kyauta,Ya zaman naku da Aliyu Amma dai lfy ko? Alhmdllh Mum,na gode Fadila da kika alkinta rayuwar Dana lokacin da idona ya rufe da son duniya,nayi Dana sani Fadila ku tayani Addua Allah ya yafe min, Inshallah Mum Addua munayi ba tun yau ba,Haka ma Ice kullum Addua yake Miki Kuma gashi Allah ya amsa,shi yasa ake son Da ya dinga yiwa iyayensa Addua suma iyaye suyiwa yaransu a hankali sai Allah ya amsa.
Da sauri Mum tace Fadila da gaske Aliyu Yana min Addua? Ashe Yana Sona har Haka? Murmushi nayi tare da riko hannun mum nace wlh Aliyu yafi kowa sonki Mum,kullum burinsa Allah yasa ki gane,Kuma gashi.

Mamaki ya Kama Mum tace ko saurata baya yi fa Fadila,tunda aka kawoni sau daya yazo shima Bai kulani ba abinci ya bayar a kawo min yayi tafiyarsa.
Dan Allah Fadila ki tayani Aliyu ya hukura ya daina fushi dani,ki sa ya yafe min na tuba.
Karki damu Mum inshallah ya Dade da yafe Miki Kuma zai dawo Yana kula dake yanda Baki tsammani, Aliyu yayi dacen mace kici gaba da kular min dashi Allah ya Miki albarka,Ameen na Furta tare da cewa Amma Dr who suna zuwa ko? Sosai ma ai sun maida Nan gidansu kullum suna hanya Babu fashi,to Alhmdllh Bari na tafi gida, sallama mukayi aka komar da ita ciki Ni Kuma na fito Zan tafi kenan sai ga Driver da mota dalleliya yace Ice yace nazo na maida ki gida,ba matsala na Shiga kawai,Ni dai ban sanshi ba Driver din nasan Ice Drivers dinsa da yawa har na gidansu Amma tunda yace Ice kawai nasan ya sanshi.

Tafiya ya dinga yi Dani ga hanya Amma yaki sai zage gari yakeyi Dani,nace Baba ya Naga an Dade Kuma har ka fita daga gari ma,Ina zaka kaini ka bar hanyarmu a baya? Ai yau goslow akeyi a garin Dole sai nabi ta barauniyar hanya,tsoro naji nace Kai Malam kaji tsoron Allah mu hanyarmu ba a goslow muna unguwar masu kudi zaka ce wani goslow to saukeni a Nan na Shiga taxi kawai.
Kara gudun motar yayi sosai abin fa ya tsorata Ni sai na zaro waya a jakata na fara Kiran Ice,shuri Bai daga ba Ina ta Kira ban fasa ba lokacin Kuma wannan Driver yayi hanyar wani daji Dani,munyi Nisa ya tsaya da motar a wani Dan karamin gida sai ga wasu zaratan maza masu mummunar suffa tsoro ya kamani da sauri jikina na rawa na turawa DanBature text abinda yake Faruwa Dani Allah yasa Ina Gama turawa suka kwace wayata tare da farfasata suka cire layin gaba daya .

Keyata suka tasa sun sani gaba ogansu yace muje ciki kinci saa Oga yace Kar ayi Miki komai,jiki na rawa na bisu har cikin wannan Dan gidan muna Shiga wani Palo ne ya gaji da haduwa saman 2seater wani saurayi ne yasha wanka Yana kamshi kansa ya dago mamaki ya kamani ganin Alamin abokin Ice Wanda suke zaune tare dasu Ya Salman a palon Ice suna hira,sai lokacin na tuno lokacin Dana Shiga Yana ta kallona har na zauna a tsakiyar Yan Uwana Ya Salman da Musa.
Alamin Right? Na tambaya kwarai kuwa Ashe kin gane masoyin naki,Da mamaki nace dama Kaine ke kirana a waya Ina ka Samu number ta? Mikewa tsaye yayi tare da Furta kina mamaki ko? Ae nace,hmm to Kinga kamar yanda na mallaki number dinki Haka Zan mallakeki ba tare da wahala ba,a wayar Mijin naki na dauki number dinki ba tare daya sani ba,Ni kaina banso zanyiwa Ice Haka ba Amma idan na bar masa ke to Zan cutu nafi son kaina da Ice,Zan iya aikata komai akan na mallakeki Kuma ta hanyar aure nake bukata wacce zamu rayu har abada,Ni ba Fasiki bane, da balai nace to Ni bana sonka ban taba son wani a duniya ba sai mijina Dan Allah ka maidani gida ko ka Bari na tafi akwai Mata da yawa Wanda suka fini,Ni wlh nayi zaton ma wani Saad ne shine yayi Kama da halin hakan ba Kai ba.

Sit down ya Furta min cike da Izza,banyi musu ba na zauna kawai,Ido ya zuba min tare da Furta kin hadu da yawa fa,ya ake ciki ki tsara yanda ya Dace ki rabu da Aliyu ko Kuma ki gane shayi ruwana Don wlh sai na Kulla Miki sharrin da Zaki kasa ganewa ke wace.
Baka Isa ka min abinda Allah Bai min ba,Kuma nafi karfinka sai Aliyu ke da wannan matsayin.

Ice kuwa yana Office ya bar wayar a toilet dinsa ya dauki hanyar gida ya tuna ya manta wayoyinsa ya koma Office ya iske kirana barkatai da sakonni har kala uku,budewa yayi tare da karantawa yanda na Masa bayanin halin da nake ciki, hankalinsa yayi mummunar tashi ya Shiga nema na a waya Amma Bata Shiga ba,kawai Office din masu tracking number ya wuce tare da kaiwa Yan sanda report, suka Shiga bincike gaba daya Danbature ya zauce.

Ni kuwa Ina zaune na Shiga yi Masa Nasiha na kawo qabli da Baadi,Allah yasa Kuma waaxin nawa ya Shiga jikinsa dama rashin Imanin nasa baiyi Nisa ba yace tashi a maida ke gida na fasa inshallah Zan auri wata bazan CI Amanar abokina ba Amma Dan Allah ki rufa min asiri karki fada Masa nasan a kanki Aliyu zai iya kasheni ma.
Murmushi nayi kawai nace Inshallah bazan fada ba Zan rufa ma asiri daga Ni sai Kai sai Allah.

Koda suka fito Dani gefen titi suka bani wayata da suka farfasata Haka na lallaba na Kira Danbature lokacin Yana Office din Yan sanda nace gani sun jefar Dani a Hanya ai kawai mota ya Shiga nayi Masa kwatance yazo, da sauri ya fito a Motar Yana duba jikina tare da shashshafa Ni hope ba abinda suka miki?ya tambaya a rude,waye ko kin San wani cikinsu Kai na girgiza Masa nace ban San kowa ba,Allah yayoni da sirri da Kuma cika Alkawari, Nasiha kawai na musu Allah yasa ta shigi jikinsu suka ce a maidani sun daina aikata laifuffuka,sun gane kurensu, Alhmdllh muje gida to Allah ya shiryesu in Allah ya yarda kinfi karfinsu, Ameen Inshallah na Furta,cak ya daukeni tare da sani a gaban mota muka bar wajen,motsi kadan Yana kallona Yana Babu dai matsala ko?karki boye min komai pls,wlh kaji na rantse ko duka ko Hannuna Basu rike ba.
Murmushi yayi tare da shafa fuskata karki Kara Shiga motar Wanda Baki sani ba matukar bani na turo Driver ba,yanzu Driver zai na kaiki ya dakko ki kawai bazan Bari kiyi tukin mota da kanki ba hankalina bazai kwanta ba idan kika fita ke daya.

Na matsu ma ki Gama schl din Nan a huta,To masters fa nufinka bazanyi ba?baza kiyi masters ba baza kiyi aiki ba hakan ya Isa kawai,me kike nema ko mene Zan Miki har danginki to me zakiyi da kudin,burina yanzu kawai ki haifo min yara,Nima Haka na matsu na ganni da katon cikina,dariya mukayi gaba daya yace Allah zai kawo ne kinji.
Allah yasa na furta.

Soyayya da Shakuwa me karfi ce ta kullu tsakanin Dr who da Saddiqa,Duk shaye shayensa ya daina har neman matansa ya daina gaba daya sabo da Saddiqa tace Bata sonsa tunda Yana shaye shaye da neman Mata,Haka Yan uwan Alhaji da Dangin matansa kowa yace ta fito da miji Haka mazan su fito da Matan aure zai musu komai ya dau nauyi,yaransa ma Haka sabo da Haka kusan mutum goma Sha ne suka Nemo ma abota zaman rayuwarsu Matan da suka kawo Wanda Basu da aiki ko Sanaa Daddy ya samo musu,har gida an bawa wasu komai randandan,Dr who kuwa ya tsantsala gidansa,Aliyu kuwa sai kokari yake Yana tausar Daddy kan ya dawo da matansa yace bazai iya Zama dasu ba zai auri dattijuwa ta gari.

Yasan Yana son Matansa musamman Mum Amma dukkansu Babu ta kirki zuciya kuma Bata da Kashi Kar yazo ya dawo dasu dukiya tasa su canja halayensu again,yaso ace Asiya Bata aikata Haka ba da zai iya Zama da ita sabo da kyawawan halayenta Amma yanzu ko ya dawo da ita hankalinsa bazai kwanta ba,daga sanda ta caka Masa wuka gaba daya digon sonta a ransa babu, bare Kuma Mum,Karimatu kuwa ko ta shiryu sai ta cuceshi matukar ta dawo hannunsa, Kudi makudai ya fitar ko waccensu Million biyar biyar ya Sa musu a accnt su ja jari dasu,sai gida dankarere ko waccensu guda daya a state dinsu ya Bata,Aunty Maryam Kuma bazai iya siya Mata a turai ba zata kwashi kudi sai ya tura Mata kudaden gidan dai dai dana Su Asiya, Danbature yaje har wajenta ya sanar Mata komai ya nuna Mata kudinta tunda wayarta na hannunsa,Kuka da Nadama Sunyi ba adadi,Daddy ganin da farko ya zalinci Asiya da yawa da kansa yaje wajenta ya nemi yafiyarta again shima ya yafe Mata ya Bata kudin da takardarta saki daya da Kuma takardar gida Allah ya hadata da rabonta.

Kowa baiji Dadi ba Amma sun cancanci hakan,,sannan Kuma ya Zama darasi akansu Nan gaba idan sun auri wani sai su kiyaye sannan ya Zama Izina ga Wanda yaji labarin.
Bikin da za ayi Daddy yace Amare da angwaye Sunyi yawa kawai aure za a daura a Kai amare ba wani biki da Kade Kade da za ayi,yayin da su Ya Salman ma an Sa bikinsu saura wata biyu ayi sai Murna nakeyi zanje nayi sati guda,Mum Kuma waadinta ya kusa karewa saura sati daya ta fito daga Prison.
Chapter 44 · 0% Book details