← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 50

Sashe 22

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waya ta latsa tare da Kiran Ak tace Ak ko wace Matarsa ayi min duba a gano ta,sannan pls a daure Mata mahaifa karta haihu har abada.
Ak yace aiki da tsada,tace Zan biya,yace ai tun Allurar da akayi Masa idan ya dawo hayyacinsa to Matarsa baza ta haihu ba, good Anty ta furta Amma gano min matar.
Da dare Ak ya kirata yace yarinyar tana kusa daku sosai Amma anyi anyi Dodo ya kasa nuna ta ko sunanta babu wani alamarta da za a gane, Anty ta fashe da kuka tace asirana zai tonu Ak pls helf me, gobe Zan turo yarona da kayan aikin.
Godiya ta Masa ta zauna hankalinta ya kasa kwanciya .

Washe gari da yamma naci kwalliyata sannan na fito zuwa part din Hajjo, tana zaune Ana matsa Mata kafafu kamar Babar sarki, Shekara tana zaune ta kawo Mata tsegumi Banda gulma ba abinda sukeyi, Hajjo tace Wai Alhaji Nasiru shi zaiyi gogaggaya da Dana Sulaiman, Shekara tace Wai Alhj Nasiru makwafcin mu? Hajjo tace shifa nawa ya Tara Dan ubansa,abinda motocinsa basa wuce na million biyar duk irinsu yaransa ke Hawa,shi Kuma ta million takwas,waye shi a kasar Nan sai ciki kamar an kifa kwarya cewar Shekara, Dariya Hajjo tayi tare da furta ai gani yake yafi kowa arziki musamman Yar Nan tasa Layula matsiyaciya,Ina zaune Ina jinsu suna ta zagin mutanen gida da makwafta, Shekara ta mike ta bar Palon tana waya,sai ga Yar Misisi ta zo ta zauna Nan ma ita da Hajjo suka Fara gulmar Shekara ai ta Zama Karuwa Shekara talatin da biyar taki aure waye waye,yi suke Naga abin bana karewa bane nace Hajjo na tafi to Algunguma saura naji kinyi gulmarmu ba tsoro nake ji ba ki fadawa Asiya nayi zancenta,dama itace ta aikoki na sani,ban ce komai ba nayi waje Misisi tana cewa Ni na tsani Yar Nan wlh Sam hankalina Bai kwanta da ita ba.

Hmm yarinyar data Fadi halin uwarta Wai Masifaffiya ce ai daga ji ba mutanen arziki bane ko daga Ina suke oho sai wani iyayi take a gidan Nan Wai ita me kyau cewar Hajjo.
Part din dangin Daddy naje duk basa Nan maza da Mata Wai sun tafi biki wasu suna cenema, part dinmu Zan koma motocin Ya Aliyu guda biyu rada radan gaske sun hadu masu Masifar tsada suka shararo suka wuceni har kofar part dinsa Naga an tsaya sai da ya Gama Izza sannan ya fito cikin Shadda light blue yasha kyau kamar ka sace shi,ko wacce Shiga hawansa take ya iya wanka, labewa nayi Bayan flowers na dinga kallonsa Ina samun nishadi da farin ciki,har ya kule ciki sannan na tafi Ina Jin wani farin ciki.

Tunani na kusa kwana yau inayi akan ya zanyi Kar na Bari 2wks tayi suyiwa Danbature wata Allurar daban Kuma,ban San ya Zan bullo ba gashi lokaci na ja,Dole na rage zuwa schl,Ina Gama aikina Zan tafi part din Anty Maryam duk da basa kulani shaye shaye kullum shine aikinsu,wani mutum ne kazamin Arne yayi Sallama da bakar Leda a hannunsa,lokacin Ina zaune kusa da Anty daga Ni sai ita su Linda gaba daya basa Nan,sama suka hau suna wani nuku nuku,suna Shiga bedroom tasa key tace ya Haka? Ak yace tun last WK zai Aiko Kaya Shuru,da sauri na labe a jikin kofar, Maryam Anty tace yaushe za a yi Masa Allurar? Saurayin yace Nan da 3days karki Bari ya wuce 3days ba ayi ba,sannan sharadi Zaki bamu sperm naki Wanda ba na sex ba,Ok tace ya za ayi a baka Taya sperm ba sex, ya Ciro wani dogon roba ja yace da wannan zakiyi Amfani da kanki har kiyi realising ki bani na tafi dashi yanzu,ba kunya tace Shiga toilet,ya Shiga tasa key yanda bazai ganta ba,ita kuma ta bargaje a saman gado tayi amfani da kanta ta samu abinda take nema sannan ta budeshi ta sallameshi,tuni na bar part din cike da alajabi.

Addua kawai nakeyi na rasa ma ya zanyi karfa kwana uku su cika,Ina ta faman tunani na shirya Dining naji kamshin Ya Aliyu Yana baza wajen,Bai ko tsaya ba yace gobe tafiya get ready, da sauri na sha gabansa nace dan Allah Kar kace tare zamuje unguwa,kace Abuja zaka je meeting,Ni Kuma Zan sanarwa Nanee zanje ganin gida sai mu hadu a airport mu wuce ba tare da kowa ya sani ba bare azo Ana Mana wasu tunani daban.

Ashe da ragowar hankalin naki no wahala ya fice abinsa,Nanee na sanarwa gobe zanje kauyenmu Yayana baida lfy jiki yayi zafi,tausaya min tayi tace Allah ya kaimu Idan na shirya na sanar Mata,amma kar na dade,.
Abin murna da dare Ice ya sanarwa Nanee zai je meeting Abuja tace Fadila zata tafi kaima Haka da wa zanyi Hira,dariya kawai yayi yace ai bazai dade ba.
Inda Allah ya taimakemu Ice iya Nanee kawai ya sanarwa zai je Abuja.
Babu wanda ya sani,nayi Shirin sosai kayana kala biyar da tarkacen abin bukata,Shima gogan da nasa ya hada Driver ya kaishi airport ya sallami Driver Dan kar ya ganni,Nanee kudi da atamfa shadda ta bani na Kai gida tsaraba,naji dadi,taxi na Shiga zuwa airport, zaune na hangoshi yana Shan ruwa Eva yaci uwar wanka.

Yaga yanda Nasha kyau ya zuba min Ido kamar ya sanni,tunawa yayi matar aure ce sai ya dauke Kai gefe, Arabian gown nasa black and sky blue nayi kyau karshe kamar zanje Dubai ko wata kasa Haka na cakare,kana Nan Kaya yasa white crazy Jean da shirt sea green yasha kyau babu Wanda zai ce Dan kasar Nan ne ko girman Nan.
Yau Fadila za a Shiga jirgi, Bai ce komai ba yace muje Ina binsa a baya aka Gama screening muka Shiga jirgi,Ina kujerar baya Yana ta gaba Wai sabo da ina da aure bazai zauna kusa Dani ba.

Ni kuwa Dadi kamar ya kashe Ni gani ga Danbature sabo da rashin zuciya irin tawa,sai dai bana nunawa kawai mazewa nayi Ina Danna waya,Abu kadan zai juyo ya kalleni,idan Allah yasa mun hada Ido sai yace daina kallona, kan waye ya juyo Yana kallon matar wani? Banza yamin,Inda muke a jirginma daban ne wajen masu kudi babu Wanda zai ganka ko kaga wani, ,an fara bamu lemo,ruwa,ko tea,da abinci kafin nayi Maganar me nake so sai yace ruwa take Sha a Bata ruwa.
Takaici ya kamani shi Kuma harda kaza da fried rice da wani juice yace a bashi, yawu na hadiya Ina ta cika Ina batsewa ko kallo ban isheshi ba Yana ta ciye ciyensa Ni kuwa yace Kar a bani komai sai ruwa,ko Sha banyi ba.
Sai na tuna sanda Ni nake Nemo Masa abinci ko ta halin Kaka sai yaci,na bashi ma a Baki.

Bamu Dade ba jirginmu ya sauka a Kano state, Jakar kayansa ta Yan gayu ya Mika min wai ya gaji ansha tafiya me Nisa bazai iya dauka ba,nasan muguntarsa ce kawai, Aiko Haka na karba ga tawa wata rantsatsiyar mota na gani tayi parking a gabanmu ya Shiga Nima na zauna kusa dashi driver yaja mun kame a baya,muryarsa naji yace matsa can, Ina fa jikin kofa Ina kake so na matsa,rashin kunya zaki min Dan ba a Baki abincin jirgi ba sai fushi kikeyi, Murmushi nayi nace Akan me zanyi fushi,ke kika sani dai.
Tahir guest palace Naga an kaimu Hotel,nace da Rana Haka har zamu tafi masauki ai kamata yayi mu tafi neman Danbature gidajen mahaukatan idan mun Gama sai muje masauki ko?
Duk wannan gajiyar da gwajab jagwab din hanyar Zan iya fita wani neman wani Dan iska can,sai gobe yanzu Ni na gaji Hutawa zanyi,Kai sai kace mace gaka da kirar cikakkun maza Amma sai lalaci, Harara ta yayi dama nasan kallo na kike Kullum, dama Ina so na Miki Nasiha na manta,Sanda na kawo Miki mutane nace ki nuna mijinki,a gabansu kika ci musu fuska sabo da hankalin ki kadan ne,Dan Adam daraja ne dashi,kowa da baiwarsa,Basu sukayi kansu ba Allah yayi su,ki daina aibata mutum halitar Allah ne,kema da kika ganki haka ba Wai kin fisu bane,kin ci musu fuska Wanda a Haka sai da na Basu hakuri sannan na Basu kudade masu yawa,karki sake ganin mutum ko ya yake ki zagi halittarsa.
Nasan Gaskiya ya fada nace to na daina Astagafrllah, Ustaz na gode.bai ce komai ba.

Room biyu ya Kama nawa da nasa Ni tsoron Hotel nakeji Amma Haka na daure,Abinci yayi Mana order me tsada lafiyayye naci na Sha nayi wanka na kwanta saman lafiyayyen bed,bacci ya kwashe Ni ban farka ba sai Magrib,nayi sallah cike da nishadi nayi shirina sosai kamar zani wani party Nasha kyau na fito Zan zaga gari, arba nayi da Danbature ya fito daga mota shi da Driver alamar wani waje yaje, yasha kyau shima,kishi naji ko wajen wata yaje,haushinsa ya kamani na fice fuuu ta gabansa shima Bai nuna ya sanni ba.
Ko Ina ban iya zuwa ba kawai Dan tafiya nayii da kafa na dawowata na kwanta,da dare naji anyi knocking na bude Ashe abinci ya bayar a kawo min.

Washe gari ma 9am sai ga lafiyayyen breakfast, na shirya 11am yace na fito mu tafi,a motar jiya Driver ya kaimu asibitin masu rangwamin hankali.
Nasan ba Wanda Zan gani,aka bude muka Shiga,da yaga fari zai ce wannan ne ko? Nace A'a, Muka Gama zaga har Private hospital na mahaukata babu,yace to muje Hotel Ni na gaji bazan iya zuwa katsina yau ba sai gobe nace to.

Mun sake kwana sannan muka sake Shiga jirgi zuwa katsina, yau ya daure yace mu zaga a yau mu tafi Gombe sai Murna nake zanje gida.
Mun Gama zagaye babu kowa Nan ma motar da aka kawo daban da Driver.
Muna jirgi zuwa Gombe yace Kai kirki da tausayina Sunyi yawa sai taimakonki nakeyi,kudina da lafiyata abin a jinjina min ne,Amma ko yabo na bakiyi ba,sabo da ke na fuskanci raini Ne dake.
Dariya nayi kadan nace sai wani yabon kanka kakeyi Ni me zance tunda kayiwa kanka.
Muna zuwa Gombe na dinga Murna, yace to wannan garin zamu kwana biyu sabo da Dan iskan a Nan zai labe da Alama ma yaudararki yayi ya ganki wawiya.
Chapter 22 · 0% Book details