← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 50

Sashe 16

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Attine ta tafi ta bani dakina hadadden gaske a Palon farko sannan tasa aka kawo min abinci lafiyayye kala biyu,tace gobe da safe Zan fara aikina, a Raina nace Ina wa zai hada gidan Nan Dana Ma ko kusa ko Alama.

Da Asuba na shirya tsab bayan nayi sallah da azkhar na Shiga kitchen Bayan naje na gaisheta da ladabi ta fada min abinda take so da safe tace nayi daga ita sai danta Ice sauran Yara da Yan uwanta masu Dafa musu abinci daban,naji dadi bazan Sha wahala ba,
Girki ne na Yan gayu iri iri ta sani nayi wani abunma sai da na duba YouTube,gani dama na iya girki tuni part din ya dau kamshi ko Ina Wanda yayi sanadiyar jawo hankalin mutanen gidan kowa sai ya nemi a wanne part wannan kamshi ke tashi Haka?
Kafin kace me Sumayya Chakwas ta fasawa gidan labari Nanee ce tayi sabuwar Yar aiki Wai Fadila wata budurwa kamar balarabiya kyau iya kyau wata Yar gayu.

Mamaki munafuncin yakai kunnen kowa dake kowanne part, yau har kunne Kaka Babar Araba Lagos Hajjojo labari ya sameta,jira kowa yakeyi yaga wace ce Fadila me kamshin girki.

Bayan na Gama girki iri iri cikin kankanin lokaci na shirya Dining sannan na gyara kitchen na sanar da Nanee na Gama mamakin saurina ya kamata tace na gode da Alama za a je dake Murmushi nayi na fita abina,dakina na fada toilet na fesa wanka Naga gidan Nan sai da kwalliya in ba Haka ba rainaka Matan zasuyi, lotion Dina na shafa me kamshi na sa wata doguwar Riga ta Arabian dark brown sosai nasan tana min Masifar kyau Kuma Bata dameni ba powder na shafa da man lebe pink kadan na fesa Yan turarena sama sama,wata Yar aiki ce ta buga min kofa lokacin Ina gyara dakina tare da shirya komai nawa, Ina budewa ta harareni sabo da na fita komai tace kije inji Nanee ta juya abinta.

AsmaBaffa
[9/4, 10:25 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕

21-25

Official

By
AsmaBaffa

Asycool, Fancy Honey, Oum Hanan,zulaihat,Queen kk,Jannat, Maman Abba,Maman Fahad.
Ga page dinku mutanena.

Fita nayi na sameta palonta a sama har kasa na Duka nace Nanee gani, tace Haka nake so Fadila Yar aiki tsab ta Zama kamar kowa ba Wai son Kai yasa kaga Yar aiki kamar an tonota daga Rami an maidata kamar dabba, akwai Islamiyya ta Yan aiki daban a gidan Nan,sannan akwai ta yaran masu gida daban,Dan Haka ki dinga zuwa Islamiyyar Yan aiki wacce akeyi da yamma duk ranar Saturday da Sunday,ta masu gida kuma Kullun kullum suke zuwa,murna nayi nace Inshallah Nanee na gode,tace tsaya muje ki gaida kowa Kar abin ya zame min bacin Rai a gidan nan,.

Tana gaba Ina binta a baya misalin 11am muna fita sai ga dalleliyar mota ta alfarma da gudu guard ya bude mata shiga tayi tace na shigo mamaki ya kamani a gidan Nan part ma za a je sai an wani Shiga mota,Haka na Shiga muka tafi,Nanee Tasha wanka cikin atamfa Super Holland, tafiya kadan a mota muka tsaya,na fita da sauri na zaga da gudu na budewa Nanee mota,ba karamin dadi taji ba Ina mutunta ta Haka, wani part muka Shiga wanda ya gaji da haduwa Yan aiki sai sintiri suke yasha gyara, Cikin wani katafaren Palo muka Shiga,wata dattijuwa tsohuwa ce fara yakunanniya Tasha Lace me tsada da Alama itace Babar me gidan,Nanee ta zube a kasa tare da sallama Nima nayi yanda tayi, Nanee sabo da biyayya kanta kasa ta gaisheta Nima Haka Amma da kyar ta amsa sau daya, tace Asiya uwar kinibibi komai ki nuna kinfi kowa ladabi Wai ke kissa ko to baza ki taba birgeni ba.

Mamaki ya kamani tace wannan Kuma kodaddiyar daga Ina?nasan danginku babu farere kyawawa haka,Asiya Bata damu ba tace Yar aiki nace me min girki tare da Ice, Baki Hajjo ta tabe tace Dalla gafara can wai me yiwa Ice girki Ice din danki ne? in ba shishigi ba,Kinga je ku karata can dallah ku barmin part dina ban son ganinku.

Ji nayi na tsani Hajjo tsohuwa haka muka tafi jiki ba kwari Asiya tana share hawaye, nace kiyi hakuri Nanee komai me wucewa ne nawa take duniyar,dadi taji a ranta tace na gode Fadila kina da hankali.
Part din gaba muka je Wanda ka rantse gidan wani sarki ne Nanee tace Nan part din mijinmu ne Bai cika Zama a kasar ba Amma Ni baya bani kwana na yanzu Fadila,na yarda dake shi yasa na iya fada Miki ban San me nayi Masa ba yace bazai iya kwanciya ko daki daya Dani ba,yayi niyyar sakina Ice shine Wanda ya Hana hakan,Kinga Dole naso Dana Ice, tace Ina cikin wulakanta a gidan Nan,kiyi hakuri Nanee inshallah komai zai wuce mu dage da Addua tace na gode yanzu naji labari Mijin namu ya dawo shekaran jiya muje na gabatar dake.

Mun Shiga cikin part din Palo Palo kafin mu Isa inda yake,kishingide na hango farin Dattijo me Kamala da haiba,Wata dattijuwa Baturiya wato Amarya Maryam Maman su Ice tana gefensa tana bashi abinci Yana ci,itace take ciyar da shi kunya ta kamani Amma Naga su ba ruwansu, ganin Asiya sai ya hade Rai kadan yace lfy ya akayi? Muka zube a kasa tare da gaisheshi da sakin fuska ya amsa Mana,tace me min girkice Ni da Ice sunanta Fadila na kawo ta gaisheka, kallona yayi kadan yace na gode Allah ya taimaka kuje kawai, Amarya Maryam ta hade Rai ta zuba min tsaki tana min mugun kallo da hausarta wacce Bata iya sosai ba tace Ana kwace min yaro na kamar uban wanine ya aifa Mani shi, wlh Ana ta kashe min yaro sai nayi daure ku gaba daya.

Mu dai Shuru mukayi dariya hausar Tata ta bani kawai muka wuce,sai part din Karimatu uwar gida Nan fa muka Sha matsiyacin kallo ita da yaranta ko kallo bamu ishesu ba muka tafi, part din Amarya tana wajen mijinta sai kawayenta da Yan uwanta muka gaisa sama sama suna dauke Kai muka fito sai part din yaran dangin Me gidan Nan fa Naja wacce ake kira da Cilla tace hmm Yar aiki da kwalliya ayiriri , sadiya misisi tace Ni Misisi Naga ta kaina Wai Nanee daga kauye take Haka? Ahayye dukkan Yan Matan suka saki shewa, Shehu Niga yace gaskiya Naga budurwa in da kasan kuluwa tsohuwar budurwata ta kauye, Nanee tace zaku ci ubanku wlh wannan tafi uwar kuluwa ma,Kuma Kar naji wlh kun sa Mata Sunan banza nasan halinku Yan iskan kauye da ance anyi sabon bako yanzu zaku kalleshi ku sa masa Sunan banza.
Dariya sukayi gaba daya.

Bayan mun fito Nanee tace yaran Nan Yan iska ne in kika zauna dasu cikinki zaiyi ciwo ranar Friday gaba daya Family suke Zama ayi Hira aci a Sha zamuje dake kici dariyar su Cilla, ko Ice da baya dariya watarana Dole suke bashi dariya.

Murmushi nayi nace wato su suke sawa mutum Sunan banza? Nanee tace duk sune suka radawa kowa suna har Dr Who.zai wahala kema Basu Sa Miki ba.
Murmushi nayi kawai Haka muka Gama zagawa gulmata ko Ina ya dauka a gidan,breakfast din Dana shirya Naga an cinye komai,nace Nanee waye ya cinye? Tace Ice ne kin San na ebi nawa na bar Masa nasa,nace to Ni me zanci banci komai ba,Wannan kinfi kowa Shirme kiyi girki da kanki ki kasa ci,Kitchen na koma na hada cornflakes da Madara Nasha abina a kitchen din masu wanke wanke da shara goge goge suka fara aikinsu.

Dakina na koma Nasha bacci na har 12:40pm Nanee ta turo me aiki ta tasoni na daura girkin Rana Ice ya fara Kiran waya,a firgice na mike Ina magagin bacci kaina na daurawa wani Dan gyale kawai nayi waje Ina tafiya Ido a rufe ji kake Kum munyi karo da wani,kamshi ya cika min hanci ban bude idona ba na kauce Zan sake hanya naji yace what...Fadila kece a gidanmu Oh My God,Muryar Dr who naji na bude Ido na kalleshi tar na saki Murmushi gani nayi kamarsu daya da Dan Bature na bangale Dan bakina na saki Ido Ina kallonsa nace Nanee yanzu nakewa aikin abinci na dawo Nan,oh dazu kece me kamshin girkin da muke ji? Munci abincin nida Ice wlh bamu taba cin girki me dadin naki ba bakiji yanda Ice ya dinga Santi ba.

Murmushi nayi Nanee tace ya kika tsaya kin sanshi? Kai na daga Mata tayi Murmushi sabo da kowa yasan idan Dr who yayi iskanci da mace to ita ta amince bayawa mutum Dole, yace Nanee ta window din gidan Ijeoma ta sanni wannan ta gari ce karki ji komai,dariya Nanee tayi tace see u na sani Malam, kan uba wani azababben kamshi muka ji na fitar hankali wajen dadin Shaka,ban San sanda na lumshe ido ba, wani ne kamar aljani sabo da haduwa sai da na kusa sumewa sabo da Jarabar haduwarsa, can Naga Yana sakkowa daga sama yasha kyau cikin wata shadda me tsananin kyau dinkin da kadan ya wuce gwiwa,wandon pencil na shaddar kun san dai maza yanzu Suma fitted ake damesu, hannun links ya Hadu ya Hadu,sumarsa me yawa baka me santsi tana sheki yaci uwar wani askin Wanda ya take na Dr who haduwa.
Tafiya yake cikin wata Izza takama da gadara fuska ba Rahma,waya yake dannawa wata iri Ni ban taba sani da irinta a duniya ba, komai Fari har takalmi, Dr who naji yace Aljani na Nanee kaga Ice sabo da sanyin zuciya wannan uban kyau Ina zaka je Haka kamar yau za daura ma aure? Kansa Yana kasa Yana latsa waya na kafeshi da Ido,dariya Nanee tayi tace Dana kenan tamkar da dubu ga kyau ga iya wanka,gadanga kusan yaki,kainuwa dashen Allah duk Wanda yace bashi ba,Dr who Yana dariya ya Karasa min nace mishi shima ba shi ba Nanee.
Chapter 16 · 0% Book details