← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 50

Sashe 43

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanda hakan ya jawo na karbo Allura na Masa wacce zai manta komai na baya hakan sai ya jawo Aliyu Dana ya samu tabin hankali Wanda ban San Allurar tsafin Haka take ba,tunda aka Masa nasa yarana su kaimin shi Yobe state su boye min shi sai akayi rashin saa Aliyu sun tsaya a daji kusa da Gombe zasu yo fitsari sai ya bude mota ya fita Wanda ya kusa Shekara ban San Ina yake ba,Kai Kuma ba damuwa kayi da iyalinka ba kowa abinda yaga dama yakeyi yi.

Sai yaro ya fita kasar waje Amma Babu Wanda zai sani sai dai a tambaya aji ai baya ma kasar,shi yasa nace maka Yana garinmu Paris Kai Kuma ko bincike bakayi ba,kawai ka saki iyalinka kamar shanu sabo da aikin ka ya fiye maka,Bayan Nan Boka yace Aliyu indai yayi aure to Tsafin zai karye Kuma bazan sake samun nasara a kansa ba,Haka kuma kaima ko wani abin nayi yunkurin yi maka asiri na zai tonu,katsam sai Aliyu ya min waya ya warke,na tura aka daukeshi a jirgi na yaudareshi nasa Wanda suka tafi dashi a jirgi zasu kaishi a duba lafiyarsa a London suka sake yi Masa wata kalar Allurar wacce ya manta Kuma rayuwar da yayi a baya tunda Ina zargin ko Aure yayi da gaske.

Bayan ya dawo duk ganin da kukewa Aliyu kwakwalwarsa ba dai dai take ba,baya iya tuna Abubuwa da dama sai kwana Nan,wanda duk nice sila sabo da gudun zai tona min asiri,Sai Karimatu da Hajjo Babar Daddy duk Suma nayi musu wand zasu dinga Jin tsorona sai abinda nace.

Dr who Dana shi Kuma ganin Yana neman juya min baya shima sai da nayi Masa iri iri kan Lallai sai ya Soni a matsayin uwarsa nayi Abubuwa da dama Marasa kyau,Amma yanzu Allah ya nuna min gaskiya na gane kuskurena sannan gaba daya Ina neman afwarku duk Wanda na batawa ku yafe min jahilcin rashin ilmin Addini wadatacce ne ya jawo sannan da samun Miji mara kula da rayuwar iyalinsa,Bai San munyi sallah ko ba muyi ba,Bai San ya yaransa suke rayuwa ba duk Bai damu ba Wanda ba kawai a saka mutum a schl shine tarbiya ba kadai kowa Yana bukatar kulawa da tunatarwa,kuskure ne Babba ace mutum Dan Yana da kudi zaiyi Islamiyya a gidansa baza a bar Yara suyi cudanya da mutane daban daban ba, yana jawo rashin iya muamula ta zaman rayuwa etc.

Abin farin ciki Ana farkon Sharia sai ga su Abbu,Hajiyarmu da Ya salman, tare da Musa sunzo anyi komai a gabansu.
Daddy yace tabbas da laifina Nima ta Nan Ina da laifi Kuma Zan gyara inshallah,kowa dake kotin ya Gaza magana mamakin halayen Mum ya kashe su,da Kuma Wai Nanee ce me kisa wacce kowa yake shedarta da Hali na kwarai Kai duniya,Mikewa Aliyu yayi yace Ina da magana,Hawaye mutane sukeyi kawai na tausayin Aliyu da uwarsa ta jefa Masa Ciwon hauka Ashe yasha wahala a duniya,Aliyu yace Mum Bayan na gudu daga hannun Wanda kika Sa su boyeni mota bus na hau ban San Ina zata kaini ba,ta tsaya a kusa da wani kauyen fulani Wanda shine kauyen su Fadila Naga mutane na sauka Nima na sauka na dinga garari Rana,sanyi damina har Allah yasa na Shiga garin....Nan Aliyu ya kwashe labarin rayuwarsa da yayi a garin su Fadila da aurensu,har yanda suka sake haduwa da Fadila a gidansu matsayin Yar aiki,da lokacin da aka harbeshi suka tafi turai,zuwa kwakwalwarsa ta dawo ya gane Matarsa ce,da tarewarta a gidansa da irin soyayyar da suke a junansu ya Gama sanar musu kaf kowa ka kalla hawayen tausayi yakeyi a kotu kuka wiwi Daddy yakeyi,Haka Fadila ma,Karimatu harda Shesheka,Mum ma haka Daddy yace hakika Aliyu naso ganewa lokacin da kuke jinyata sabo da idan ba kowa daga Kai sai Fadila a asibiti Ina jinku Kuna kalaman soyayya.

Daddy yace Alhmdllh Ni duk na yafewa kowa Ina Rokon kuma ku yafe min Baki daya,sannan Dan Allah a yafi kowa Haka akayi ta yafewa juna,daga karshe Daddy yace da me shariya tunda ya koma Dan kallo yace a kashe Kara ya yafe Yana son matansa Haka,Alkali yace Dole sai ya yanke hukunci sabo da ya zamo darasi ga mutane gaba.

Kotu tayi Shuru Ana sauraro Alkali yace Asiya me yunkurin kisa kin dauki doka a hannu Allah yasa Bai mutu ba kotu ta yanke Miki Hukuncin daurin Shekara biyar a gidan yari ko tarar milliyan biyar,sannan Zaki biya Daddy duk kudin da aka kashe Masa a asibiti,Nanee kuka wiwi takeyi tana Nadama.
Mum daurin wata biyar a gidan kaso ko Kuma tarar milliyan daya sabo da itace silar komai zakiyi wata guda a gidan kaso Babu Tara,sai Karimatu kotu ta wanketa fes Babu sa hannunta.
Hukuncin yayiwa mutane Dadi sabo da Nanee baza tayi zaman prison ba za a biya Tara,Mum kuma tunda itace tayi asiri har Daddy da Nanee suka samu sabani hakan ta faru,Nan take Aliyu ya biya komai Dana Mum Dana Nanee aka tafi da Mum gidan kaso zatayi wata dayanta su Kuma suka tafi gida Baki daya sabo da alkali ya sallami Kara yace sauran abinda ya shafi Family dinsu ne suje suyi a gida.

Mum sai kuka da Nadama akeyi duk da Aliyu ya biya wuri mai kyau na masu kudi za a ajiyeta ba wurin wahala ba
A Babban Palo aka hallara har su Abbu,Hajjo ma taji sauki a gabanta akayi komai,Daddy ya karbi su Abbu hannu biyu aka zauna cike da farin ciki,Tunanin su Karimatu ruwa Tasha sai muka ji Daddy yace Asiya da Karimatu ku tashi ku bar min gida Baki daya sai na nemeku,ba musu kowaccensu ta mike ta Hado kayanta ta tafi jaharsu ba Wanda yace kala sabo da sun cancan ci hakan.

Daddy ya fara Magana da cewa mutane yanzu sun lalace da bin malamai Wanda yawancinsu ba malaman Allah bane bokaye ne, wasu ma sun San bokaye ne suke zuwa Ana shirka,Babu abinda Kuma wani ya Isa ya maka Wanda Allah Bai ma ba cewar Abbu,yanzu abinda ya addabi alumma kenan,kowa Malam Ana jefe jefen juna,Wanda wlh duk abinda ya samu wani ya aikata marar kyau duk ya rataya a wuyana Wanda yayi Masa sihirin Allah yasa mu Dace Cewar Abbu.

Aliyu Allah make albarka kasha wahala Kuma ka cancanci yabo yanda duk da Haka kake yiwa Mum biyayya,Fadila ban San irin godiyar da Zan Miki ba Ke da iyayenki Allah ya albarkaci aurenku,Allah ya muku albarka Baki daya cewar Daddy,yaci gaba da saura Wanda suke gidan Nan Mum tasa na koresu ko wacce kuyi Mata waya su dawo muci gaba da Zama tare,sannan ku hadu ku bani hadin Kai mu taru mu gyara gidan a canja tsarin rayuwa ba irin ta baya ba.

Zama akayi Yan aiki na kawo lafiyayyun abinci munsa Daddy a tsakiya Ana ci Ana Hira,Abbu yace ke Fadila muje muga gidanki mu tafi kauyenmu,Abbu yace Haba Haba dai sai sai jibi zaku koma naji Dadi da Daddy ya hanasu tafiya yace gobe sai ku shirya a kaiku gidan na Aliyu har mu gaba daya zamuje muga gidan, Daddy da Abbu tare da Hajjo Nasiha suka dinga zubawa.
Murna Aliyu yake kamar me Nima Haka,Ido muka hada ya min inkiya Wai na taso mu tafi gidanmu na make kafada nace a Nan Zan kwana wajen Su Abbu.
Fuska ya Bata yace Daddy kaga Fadila Wai baza tazo mu tafi ba wajen Abbunta zata zauna.
Da can da ba mu sani ba wa kake kaiwa Kara? Ka bar yarinya tayi Hira da danginta dama a asibiti fa Ina jinka irin fitsarar da kakeyi Ina kwance Rai a hannun Allah,kunya ce ta rufe mu,na mike sum sum nayi waje, Ice ya biyo bayana da sauri gaba daya Yan gidan suka Fara dariya.
Ta baya naji anyi sama Dani nasan DanBature ne...

AsmaBaffa
[9/4, 10:26 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕

91-95

Official

By
AsmaBaffa

AsmaBaffa fans wannan page naku ne.

Tunda na kwanta bacci ya kwashe ni ban farka ba sai da Magrib na tashi na duba ko Ina Danbaturena da gaske Bai dawo ba tun ina sa Rai har na Gama dafa lafiyayyen abinci tare da fesa wanka naci kwalliyata ta Amma har 9pm banji alamarsa ba,Shawara na yanke na nemeshi a waya,Nan take na Danna Masa Kira,kashewa yayi tare da kirana back,ya na ganka Shuru ne? Zance muka tafi ai na fada Miki gata ma ki gaisa da sabuwar Amaryata me zuwa Nan gaba,sabo da nasan Wasa yake nace Bata mu gaisa,abin mamaki sai ko naji Muryar mace me sanyi tace Aunty Ina yini ya gida ya aiki,kishi yasa na dauke wuta duf na kasa magana karshe ma na kashe wayata Baki daya.

Ba afi 20mnt tsakani ba ya dawo gidan dauke da Ledoji sai da ya siyo Mana kayan ciye ciye,ban nuna naji haushi ba na danne zuciyata yanda na Saba tarbarsa Haka nayi yayi mamaki shima tunda ya sanni da kishin masifa, ya dai ganni Ina Abu kamar Banda jini a jikina,bance Masa komai ba sabo da abinda nake ji a Raina nasan Ina magana kuka zanyi kawai karma ya rainani yasa nayi shuru kawai.
Wanka yayi tare da Shirin bacci sannan na kawo Masa abinci yaci ya koshi Ni Kuma Ina Shan Ice cream dina da sauran kayan ciye ciyensa daya kawo min,Zaki Bai dameshi ba.

Bayan mun Gama Nima Shirin bacci nayi shima ya sake yin brush muka kwanta nayi tunanin zai nemeni sai naji Shuru har bacci ya fara kwasa ta Yana danne danne a laptop dinsa,light ya kashe tare da kwanciya ya rungumeni a jikinsa yayi missing dina da yawa Nima Haka ji kawai nayi Yana shafa min jiki na,yace I'm sorry ba wajen wata naje ba kanwar Ayman ce, farkaw nayi Nima naji want farin ciki, jikina ya karbi sakonsa dama kadan nake jira ban san sanda muka Shiga farantawa juna Rai ba sai da muka kusa cinye daren kaf muna aikin samun jindadinmu,Ni kaina Ina mamakin kaina da nake iya zagewa na nuna Masa kauna ba wani matsala.
Chapter 43 · 0% Book details