Sashe 19
Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da gaske kowa ya matsu yaji labarin, na Gama aikin na dawo da yake gulma ce harda tarairayata,na zauna Hajjo tace matso kusa Dani nafi ji,shi kanshi Ice daina danna waya yayi ya zauna zaiji labari auren Mahaukaci.
Labari na fara Basu tun farkon ganina da mahaukaci, har wahalhalun Dana ci a kansa,har aure da rayuwarmu ta aure,har sanda ya Dan dawo hayyacinsa ya tafi Bayan naci duka.
Kafin na Gama na jike da Hawaye jagwab, su Cilla da Misisi har da kwalla,Hajjo kanta tayi kwalla,Nanee harda kuka wiwi,tace Dole maza su dinga Miki gizo kowa kika gani kice Danbature ne, Ice Kam yaji tausayina matuka Yana tsinewa Danbature a ransa yayi butulci.
Anty Amarya Baturiya sarakan love tace Mazaje gasu Nan everywhere ki canja shi ga masu kudi wa yake ta wani talaka me Mahaukaci.
Nanfa suka lakaba min DanBature suna na, Karimatu kuwa marar Imani cewa tayi ke Dalla makaryaciya kawai ki shirya Mana film wannan ai film ne Ina Haka zai faru.
Shuru nayi musu kawai nasan ba yarda zasuyi Dani ba,Dalilin da yasa na Basu labari ko Allah zai sa Danbature ya gane Ni ko Yan gidan su a samu a fayyace gaskiya Amma Shuru basu San ma ya taba wani Ciwon hauka ba,shi kanshi ai da zanga alamar ya gano gaskiya Amma ko Alama.
Bacin Rai yasa nace Nima yageshi zanyi a Raina kawai nayi rayuwata an daina auren ma.
Shekara tace Hajjo yaushe Daddy zai dawo next month birthday na,gwasaleta akayi tsohuwa dake 35yrs mun gaji da party sai na aurenki, Haka na kawo abinci iri iri masu arnen dadi,Yan aiki Suma Ana ta kawowa tunda suka ga kalar abincina sukace sai sunci, Nanee tace suzo su eba kafin kace me an cinye nawa ko Danbature Basu ragewa ba, nasan Kuma yunwa yake ji, Allah yasa na ebi nawa na ajiye iri iri nasan zai isheshi,masu gyara Palon sun kwashe komai sun gyara Ana ta santin girki na,Naja Cilla tace Dr who Kuna cin dadi Yar kauye da iya girki Haka Wai. Babu Wanda ya kulasu, Danbature yunwa tana ta kwakule Masa ciki ya tsaya yanga,komawa nayi na dauko Masa nawa na jera su a wani hadadden tire komai da nasa na musamman ne abin kallo na kawo na ajiye a gabansa Yana kwance sai latsa waya yake, serving dinsa nayi sai kallona sukeyi wasu suna cewa iyayi wasu na tabe Baki.
Nanee kuwa taji dadi Ashe na ajiyewa danta nasa daban, sai gadara yake zubawa da kyar ya zauna, ya cinye shi tas kuwa, 5pm aka fara watsewa daga zaman Palon na zumunci.
Yau Saturday abin ya bani mamaki Islamiyyar yaran gida na gani har maza da Mata manya da Yara,kowa ya hallara Banda DanBature, Kuma duk cikinsu ba Wanda ya Gama izu goma a schl din kawai Danna waya sukeyi da laptop basa fahimta.
Yan aiki ma ga tamu kusa da tasu.
Ni na wuce Izu arbain Karina daban ne,littafan Addini da dama na iya,na tashi Ina rero qiria ta dukkan Yan Matan da mazan hankalinsu ya dawo wajena sabo da kwarewa ta da Kuma dadin muryata, Danbature na hango zai fice na tabe Baki shi yasa Bai iya addini ba lokacin da yake Mahaukaci Ashe Bai San komai ba, da Asuba ake tashin kowa a cika masallacin gidan sallar Asuba har Mata.
Yau da Asuba Ina magagin bacci na fito.
Komai duhu Dole na gane Danbature ya fito da jallabiya harda carbi a hannunsa,a Raina nace kamar gaske ba a San ko fatiha ba, a hankali na labe kusa dashi jikin masallacin a hankali na canja murya nace ba virgin bane, juye juye ya kama yi Yana neman Ina yaji ko kunnensane, na Kara cewa ba virgin bane,ya Kara waige waige Amma ba kowa,tsaki yaja yaci gaba da Jan carbinsa kafi a tayar da sallah, nace kauyen Dingawa Gombe state kana da Aure.
Tsoro abin ya bashi ya rasa waye da sauri na bar wajen na shige masallaci ta baya.
Bayan an idar da Sallah ya Gama laziminsa ya fito na Kara labewa a kofar part dinsa sabo da karfin Hali a hankali nace ba Virgin bane...da aurenka dube dube ya fara na tsorata Naga ya wuce sama,na fice da gudu na koma part dinmu.
Sabo da mugunta yasan Ina da lecture yau Monday sai yace Nanee ki tura Wannan Yar kauyen zata gyara min Office dina,wace Kuma Yar kauye? Nanee ta tambaya,mahaukaciya Mana cewarsa,Nanee ta kalleshi kawai tace ba ruwanka da ita, 1pm na Gama girki na na shirya komai Nanee ta fito cikin kwalliya tace shirya abinci a basket driver zai kaiki office din Ice Zaki gyara Masa me aikin ya koreta Wai kafin ya samu wata.
Ba yanda na iya na sa hijab Dina Kato na dauki basket muka tafi,na kwankwasa Masa Kofa ya Dade kafin yace come in,Ina Shiga wow sanyi da kamshi ya dakeni,katon Office ne ga table dinsa da kujera tana juyashi takardu a gabansa,gefe Kuma Palo ne na Alfarma yasha kujeru babu wani dirty, Ina yini na gaisheshi hannu kawai ya daga min .
Yana Shan tea Yana ta rubuce rubucensa na wuce na zauna a palon,inda aka tanadi kujeru lafiyayyu Yan gaske,kallon Office nayi tsab ya gaji da haduwa, wani maaikacin ne ya kwankwasa Izini ya bashi ya shugo wani saurayi matashi Kyakyawa shima Dan gayu, tafawa sukayi yace Kai Dan iska ka share mutane bikina fa saura 3wks Zan barka a gwauro, Aliyu ya kalleshi cikin nutsuwarsa da Izza Bai ce komai ba yaci gaba da aikinsa, ban son rashin mutunci zanzo har Office naka kana min kallon da ka Saba, kayi wani Shuru dama ka Saba yi Mana haka,Me kake so nace maka Allah ya kaimu musha biki Omar.
Wata hirar suka sake,Ni kuwa Ina gefe Dadi nakeji gani kusa da Danbature shi yasa nayi zamana Ina satar kallonsa,zuciyata tana sanyi Ina Jin dadi.
Mikewa nayi nace na tafi sum sum Zan fita yace hey.. come back stupid girl,wa zaiyi serving na ko Nanee Bata fada Miki yanda nake ba, Omar abokinsa yace wanna me kyau Haka kanwarka ce,badan an Sa min Rana ba ai wlh canjawa zanyi na aureta, karaf nace malam Ina da aure,ke Dalla shut up wani kina da aure mahaukaciya Hospital Zan kaiki sai anyi Miki gwajin kwakwalwa cewar Masifaffe Dan Bature.
Omar yace to fa Kai matar wani kake wa tsawa? Na tabe Baki nace Kai ai shinefa...cike da balai yace shinefa ubanki wlh Zaki jawo na Miki mugun duka, kallon Omar yayi a hasale yace Malam tashi ka tafi gidanku zanzo da yamma,au korata kayi? Ae Jeka.
Yana fita manager dinsa ya shugo suna ta aikinsu,Yana fita Secretary itama tazo,Bayan ta fita wani yazo da kudade a shirye cikin kwali, ka rantse macaroni ne, waya ya daga ya Kira Daddy suka Gama maganganunsu a waya na wajen business, wani ya Kira a waya yace ya Kai kudin bank.
Mikewa yayi Yana mikar gajiya ya bude wani Room Wanda hadadden bedroom ne ciki toilet ya Shiga yayi Alwala ya fito a bedroom din yayi sallah,Ni kuwa yau bana sallah period nakeyi,na matsu ya barni na tafi sabo da rushing yake min Kar na baci Allah ma yasa na taho da pad a hand bag Dina.
Fitowa yayi Yana Izza tsakiyar Centre carpet ya zauna yana latsa waya yace serve me,ban San me yake so ba na bude nace wanne ya nuna abinda yake so na zuba Masa komai a plate biyu sai juice Amma kadan Yana da Saurin cin abinci Amma baya ci da yawa,a Raina nace oh halayensa ne Zama a kasa tun Yana Mahaukaci ma.
Ya fara ci a ransa Yana Jin dadin girki kamar me Amma baya ko nunawa ma, Bayan ya Gama ya Kira maaikatansa masu aiki karkashinsa suka dauka abincin suka tafi ci sabo da tunda na fara girki suke maitar abincin sabo da dadin girki na.
A kasan carpet ya kwanta Bayan ya Dan jira abincin ya tsirga Masa,idonsa ya lumshe yace jeki fara aikinki ko ina ya Zama neat, ta bedroom na fara da toilet suna sheki da kamshi na fito nayi Wurin Table nasa da komai har na karaso inda yake kwance Yana bacci,tuna baya nayi baya so yana bacci a tasheshi a Raina nace wancan daban Danbature wannan daban Aliyu Ice,
Tashinsa nayi nace zanyi shara ka koma bedroom, ya mike kuwa ya koma bedroom ya kwanta yaci gaba da baccinsa har na Gama ko Ina Yana kyalli da kamshi,na zauna ina jiransa.
Ya Dade sai 4pm ya tashi yayi Alwala da sallah sannan ya fito, ganina a zaune yasha mamaki,Ni kuwa searching girki nakeyi Ina koya a YouTube yace ke Wai bakya sallah ne? Ae kawai nace yace kanki tashi ki barmin Office.
Har na bude kofa yace ke dawo na dawo na tsaya gabansa Ni haushinsa nake ji yaki so na ya mantani, yace bani Detail na Mijin da kika aura Mahaukaci ya gudu ya barki Naga kin haukace kema so Zan taimaka nasa a bincikoshi duk inda yake a fadin duniya.
Dariya ya bani ga mutum Amma yace ba shi bane,a Nemo shi mu gani,a fili nace Sunansa Aliyu Hydar Sulaiman da Haka aka daura Mana aure,yasan sunana Fadila,sannan kirarsa da komai irinku daya, kauyen da kika zauna dashi?, Nan ma na sanar Masa,Ina Agogon nasa da Zobe da kika ce nasa ne kina dashi? Nace ae jiya naje gidan Attine nace ta bani na karbo gasu a jakata,Ina murna ai yanzu Danbature zai ganeni nice Matarsa,na kwaso jikina na rawa na Mika Masa su,Abin mamaki juyasu ya Shiga yi ya Kare musu kallo sai ya tabe Baki yace wannan ai trash ne kina wani kalli agogo tsoho dashi haka Danma na diamond ne ga wannan kazamin zobe, sa min su a Leda Kar na dauki cuta, Jin abinda yace ya tabbatar Bai gane komai ba.