Sashe 6
Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau kwana nayi Ina kuka karshe dabara ta Fado min,na koma wajen Abbu Bayan na gaisheshi nace Abbu Dan Allah to Ni dai daka aura min Talle gwara ka aura min Dan Bature ko a daji zamu na kwana zan zauna,Salati Abbu ya saki kana ya fashe da kuka,Ya Salman suka afka dakin Abbu da gudu sun zata wani gagari min abune ya faru da har Abbu ya fashe da kuka Haka har tsakar gida Ana jinsa.
Musa yace Abbu lfy?, Abbu ya Kara fashewa da Kuka Yana nuna Ni da yatsa kamar yaron yaye ban San sanda na kwashe da dariya ba nace Wai Dan nace ya aura min Dan Bature Abbu Ashe Saurin kuka ne da Kai? Ya Salman ne ya Kore Ni shima Yana kunshe dariyarsa.
Gaba daya na canja halina na hakuri da kawaici tunda aka ce zan auri Talle me lemo,yau shiryawa nayi fes nayiwa Hajiyarmu sallama nayi karya nace zanje gaida dangi, harda murna tana sa min albarka, ban tsaya ko Ina ba sai rumfar Talle me lemo,ga lemo ya kasa harda kankana,Talle tunda ya ganni yake faman washe jajayan hakoransa, Ina zuwa da gadara cike da Isa nace Dattijo fere ka yankamin na dari biyar,Talle ya washe Baki yace ai Amarya kyauta za a baki, jiki na rawa yace wannan kwalliyar tawa ce? Kaina na dauke nace ta hadadden saurayina ce,Kai nifa dana maka kwalliya gwara nayiwa Mahaukacin Kare,Baki bude Talle ya kalleni kawai sannan ya yanka min lemo da yawa,nace kankanar fa ko a banza zaka aureni,Nan ma na zabi katuwa nace yanka ta,yamin yanda nake so Yana wani washe Baki na dauki ledojin nayi tafiyata.
Na Shiga gida kowa Yana sa rai zasu Sha lemo da kankana sai suka ga na wuce na dauko Sallayata katuwa Ina budawa da gadara tunda yanzu na canja halina tunda akace za ayi min auren Dole,ficewa nayi daga gidan da kayana,inda nasan zanga Dan Bature naje,Allah sarki na ganshi futu futu duk yayi dirty ya rame sabo da yunwa yau kwana hudu kenan bamu hadu ba,ji nake kamar na Shekara wani dadi nake ji Dana ganshi,tunda ya Hangoni ya mike tsaye da sauri Yana Murmushi Wanda shima na farin ciki ne, wani azabar kyau yayi ga kwarjini.
Duk da Dirty da yayi bana kyankyaminsa na Shimfida Mana Sallaya tare na zauna sannan na nuna Masa shima ya zauna tun kafin na bude ledar ya fisge ya bude,Amma bazai iya Sha da kansa ba sai dai ya dinga damalmalawa ta baci,da kaina na Shiga bashi Yana Shan kankanar, har Hannuna yake rikewa ya zuke har cizona yakeyi sabo da sauri, idan muka hada Ido Ina ta murna Ina Murmushi burina ya cika Yana cin abin da na kawo,idan muka hada Ido indai yaga Ina dariya sai shima yayi Murmushi Yana min wani kallo me zautar da hankalin duk Wanda ya kalla,ga wani kwarjini,kyau,sura da cikar zati.
Yasha fruits din da yawan gaske musamman kankanar na zuba Masa ruwa ya wanke hannunsa Amma ya kasa wanke hannayen Haka na kwara musu ruwa ya janye hannayensa da sauri ya boye abinsa,faratansa nagani Sunyi zako zako,wani yaron Almajiri dake kiwon shanu a Bayan gari na aika shago nace sauri ka siyo min Reza, Bai dauki lokaci ba ya kawo min Reza, hannu na Mika zan jawo hannunsa Amma yaki yarda sai ma bar min wajen da yayi tare da shigewa cikin Dajin abinsa.
Gida na tafi Ina sauri sabo da na Dade.
Ina sauri sabo da gaskiya na Dade,ina komawa gida Hajiyarmu tasa Salman da Musa suka zaneni Nasha kuka Amma kamar me kunnen Kashi washe gari ma saida na saci jiki naje wajen Dan Bature.
Ranar Kuma Abbu yace ya haramta min fita ko kofar gida,Amma kwana uku na karya dokar sabo da yanda tunanin Dan Bature ya addabeni bani da sukuni Sam tunanina tausayinsa nake ji kawai.
Abbu tunda ya samu labarin yau na karya dokar na fita ya samu Yara majiya karfi mahaukatan fulanin daji suka kamo Dan Bature har kofar gidanmu na fito Ina kuka Ina bada hakuri me ya Muku Dan Allah kuyi hakuri karku taba lafiyarsa,Abbu indai zuwa wajensa ne wlh na hakura bazan sake ba Dan Allah karku yi Masa komai zaku dauki zunubi,a gabana Abbu yasa kartan Nan suka fara jibgar Dan Bature da makami,suka Masa jina jina sannan suka jashi can gefen titi suka yasar dashi Ina ta uban kuka na fito da gudu zan bishi Abbu yasa Musa suka rikeni suka maidani gida,yau nayi kukan da ban taba yi ba a duniya duk me Imani sai ya tausayawa bawan Allah Nan.
Abbu yasa na daina fita ta Dole Haka Dan Bature ya karaci jinyarsa ya warke duk ya Kara lalacewa ya rame,ga dirty Yana cikinsa farcen Nan zako zako Suma ta Kara taruwa.
Yau ya rage saura kwana daya a daura min Aure da Talle,kasa jure bacin Raina nayi na saci jiki na tafi Office din Yan Hisba dake kauyen na Kai Karar Abbu za ayi min auren Dole.
Nan danan Yan Hisba suka min Nasiha sannan suka je har wajen Abbu suka kwatar min yanci na,suka yiwa Abbu nasiha sosai,Abbu yace naji na hakura Amma bazan daga ranar daurin aure ba ta kawo min Wanda take so yau.
Ba tare da tunanin komai ba nace na Amince, da yamma na fito neman Dan Bature can kusa da wata bola na hangoshi Yana kwance a tsakiyar Rana,sai karkarwar sanyi yake yi da Alama zazzabi ne ya kamashi,tausayinsa ya kamani jikinsa duk raunikan da Su Ya Musa suka dake shi.
Chemist naje na taho da me chemist din ya ganshi ya bani Magunguna yace a bashi,nace nawa? Me Chemist yace kyauta na bashi idan Bai warke ba ki dawo a canja wasu.
Da kyar a cokali na jika maganin ya narke Ishu me chemist ya tallafa min na bashi maganin da kyar ya Sha.
Haka Ishu ya Kira min wasu maza suka dauki Dan Bature aka kaishi inuwa Nan bacci ya kwashe shi,a wajen na yini Nima sai da yaci baccinsa ya koshi sannan ya farka da sauki Don maganin yayi Masa aiki,Abinci na naje gida na dakko taliya da miyar kifi na siyo ruwa na zauna na bashi da kaina Yara an taru Ana ta kallonmu, saida na tabbatar ya koshi sannan na sake bashi maganinsa lokacin Ishu me chemist yazo duba shi, na mike zan tafi gida naji ya rike min hannu, juyowa nayi Ina kallonsa nace me zanyi maka? Ina Masa Maganar kurame, Hawaye ne Naga ya zubo Masa sharrr....Ishu yace subhanallah wannan wlh duk yanda akayi haukar tasa me Tsafta ce,ba shahararriya bace Amma Mahaukaci shahararre ba Haka yake ba Sam, Allah Baki ladanki Fadila tabbas kina kokari Kuma sai Allah ya Baki Lada.
Komawa nayi na zauna kusa dashi na Shiga lallashinsa cikin sanyin muryata nace kayi hakuri anjima zan dawo kaga Abbu na zai dukeni, ya sunanka? Kallona yayi baice komai ba,nace ur name pls, kansa ya dafe ya Lula tunani da sauri ya zabura ya tuna kenan yace Aliyu Hydar,Murmushi na saki nace nice name, na Dade ina lallabashi sannan na mike na tafi ba tare da ya rikeni ba sai Murmushi da yayi min kadan.
Misalin Karfe 10 na dare Hadari ne ya Hado sosai,ba abinda ya dameni irin tunanin Dan Bature gashi bashi da lfy idan ruwa ya zaneshi shike nan Kuma.
Zumbur na mike na lallaba ba tare da kowa ya sani ba na bude gidanmu na fita da gudu naje inda na Saba ganinsa, hannunsa na jawo da sauri muka tafi gidanmu dashi,ina ta jansa,tsorona idan na barshi a zaure za a ganshi ayi Masa wani abun kawai na kaishi dakina na nuna Masa bed dina nace kwanta yaki kwanciya,nayi nayi Amma yaki kwanciya sai ya koma kasan ledar dakina ya kwanta,Bargo na lulluba Masa ya cire tare da jefarwa Yana Bata fuska.
Kofar na kulle Masa sannan na koma dakin Hajiyarmu nace Tsoron tsawa da walkiya nakeyi yau a Nan zan kwana,Hajiyarmu tace Kya karaci gulmarki gulmawuya.
da Sassafe na farka kafin nayi sallah na budewa Dan Bature kofa Wanda dama ya gaji da Zama a dakin Ina budewa ya fice daga gidanmu da sauri,Abbu Yana kofar gida lokacin sai ganin Dan Bature yayi ya fito daga gidansa.
Abbu yace Kai Kai.....Amma ko kallonsa baiyi ba yayi gaba abinsa, da sauri Abbu ya dawo gida kafin nayi magana ya rufeni da duka tako ina,.
Yau zan daura Miki aure Dan ubanki tunda Baki da mutunci Haka ya fice a fusace ya sanarwa Talle da danginsa,nan danan aka taru a kofar gidanmu,gashi yace idan na bar gari Bai yafe ba bare na gudu.
Office din Yan Hisba na koma Ina kuka nace Abbu baiji nasiharku ba,Haka muka taho da Yan Hisba filin daurin aure an cika makil.
Dan Hisba ya fara waazi da Nasiha,Abbu yace nace yanzu ta kawo Wanda take so idan Bata kawo ba to wlh na daura da Talle,Talle ya washe Baki yace Bata da wani sai Ni a daura kawai, Ina Hawaye nace Ni Dan Bature nake so.
Abbu yace to kunji Mahaukaci take so,Dan Hisba yace a kawo Mana shi muji idan yasan sunansa sai a daura dashi tunda tace ita so take ta taimaka Masa ta ceto shi daga halin da yake ciki,,Nan mutane suka tafi neman Dan Bature suka ganshi a zaune kamar me hankali, mutanen kauyen har Yan hisban ba wani ilmin addini garesu ba, sukayi juyin duniya ya tashi bare ya bisu sai da nazo wajen da kaina sannan ya bini,nace ka fada min sunanka Dan Allah kayi magana sunanka za a daura Mana aure yanda zan kula dakai daga halin da kake ciki,wannan itace damar da zan iya yi maka komai,zan aureka ba Wai Dan Ina sonka ba,don kawai na taimaka maka,ka duba irin wahalar Dana ke Sha a kanka.
Sai da na Dade ina Masa maganganu nayi Masa Zancen kurame ya fada min sunansa,da kyar kamar me koyon magana yace Aliyu Hydar.