← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 50

Sashe 29

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sati daya ya wuce Hajjo shuru Bata mutu ba,tace watakil Next wk ne,shima ya wuce Shuru,Hajjo tace to ko sati Uku ake nufi,shima ya wuce Shuru har taji sauki ma tana gida kayan sawarta saura kala uku Rak duk tasa an sadakar dasu,Wata daya Shuru,Hajjo tace sai wata uku ake nufi taci gaba da jiran mutuwa Bata da aiki Sai kuka da Jan carbi.
Ga zumunci ya motsa tana zuwa garin danginta yanzu,Bata gulma.

Shekara ce abokiyar munafuncinta ta shigo tare da Zama Bayan sun gaisa tace Hajjo kinji Asiya Wai zata tafi Kauyensu next wk Allah yasa ba wajen malamai zata je ba,carbin dake hannun Hajjo ta shaudawa Shekara a jikinta da karfi,Shekara ta kwalla Kara tare da ja baya,Munafuka Ni yanzu ba ruwana da duniya Ina Zama na Zaki sa na kwashi zunubi Yar kauye kawai Allah ya shiryeki.

Mamaki Shekara takeyi na canjawar Hajjo gaba daya lokaci guda,Hajjo ta karfi ta koma waazi a gidan kowa yaje gaisheta sai ya tafi da mamakin canjawar Hajjo.
Anty Maryam tunani takeyi yanda zata gano gaskiya tsakanina da Danbature ta kasa ganewa,Linda ce ta Bata Shawara cewar ta jawo Ni a jikinta sosai har na saki jiki da ita tasan gaskiyar lamarin, Bata San ta makara ba domin na Riga nasan halayenta bazan taba sakin bakina ba.
Kwana biyu tsakani Anty Maryam ta canja gabaya har Part din Asiya take zuwa nemana,tace kwana biyu bakya shugo min ki dinga zuwa muna Hira Mana,ko ta turo Yar aikinta ta kirani naje wajenta tana nemana tayi ta faman bugar cikina..

Yau ma Ina Gama aikina da yamma ta Aiko nazo wajenta Zan tayata gyara kitchen, Dana je ba wani gyara tana Murmushi tace me yasa bakya son Shigowa Fadila?Murmushi nayi kawai nace ba komai Mum,Hmm Fadila shekarar ki nawa ne? Nace 18 yanzu na kusa Shiga 19yrs, Lallai kin girma sai aure ko? Ya kamata tunda kina zuwa University ki fito da mijinki,aure shine darajar mace, Murmushi kawai nayi nace Nafi so sai na Gama Degree na sai nayi aure na,Amma Kuma naji kamar ance kina da aure Fadila cewar Mum, gabana ya Fadi Ras nace bani da aure kawai sharri yaran gidan Nan suke min,Uhm halayenki suna birgeni ko Zaki auri Dana Dr Who na hadaku aure? Baki bude nace kiyi hakuri Mum Ina da saurayi na Masa alkawari n aure schl dinmu daya dashi an kusa Kai kudin aure ma.

Farin ciki taji a ranta tace yaushe Zaki kawo min shi ya gaishe mu? Nace sai na tambayeshi sai yasa Rana da kansa,murna sosai ta kamata bani da alaka da Danta DanBature.
Muna Hira Aliyu ya shugo da sallama,muka amsa yayi mamakin ganina Ina part din Mum dinsu,kallo daya ya min ya nemi waje ya zauna kusa da Mum dinsa Yana gaida ta,sai kallona takeyi ko zata gane wata Alama da zata nuna Mata cewar muna da alaka Amma Bata ga komai ba,Muryarta naji tace Fadila kawo Masa abinci da ruwa,bana cin abinci juice kawai Zaki kawo min,ya furta Yana me hade rai.

Ina tafiya yace kin San Ni bana son abincin Yan aiki lemon ma wannan ce zata bani Mum,Bari na dauko da kaina,Mum tace me tayi maka Naga kamar baka kaunarta,Na tsaneta ne Mum ya Bata amsa kawai tare da Mikewa ya nufi kitchen, farin ciki ya Kama Mum.

Yana Shiga kitchen ban sani ba sai ji nayi ya fincikoni yana fada ki daina zuwa Nan na fada Miki me ya kawoki? Banza na Masa yace ke zanyi maganinki wlh kin rainani Naga Alama, Shuru na Masa na turo Dan bakina gaba nace to Ina ruwanka wai? Mijina ne Kai ko me? Kafa takura min,juice din ya fisge a Hannuna dai dai lokacin Mum ta shigo taga ya fisge lemo Yana hararata, wani Murmushin farin ciki tayi a fili tace mene Haka Son ? Ina ruwanka da ita.
A kitchen din ya barmu yayi gaba abinsa.

Nanee ta Fara canja min tana Jin haushina kasancewar tana ganin ko yaushe Anty Maryam tana kirana part dinta,sai ta Shiga zargin Kar a hada Baki dani a cutar da ita shike Nan ta daina sakar min fuska Abu kadan idan nayi fada da masifa,Sam ta tsaneni yanzu,Dalilin Haka yasa bana Jin dadin zaman gidan,tunani nakeyi ma yanda Zan bar aikin gaba daya na huta tunda Nasan inda Danbature na yake.
Yau Friday yau Kuma na tambayi Nanee Zan tafi gidan Attine zanyi weekend a can Bata hanani ba tace na shirya driver ya kaini,kayana na hada Sun Kai kala uku na tafi abina.

Tunda naje gidan Attine na Samu nutsuwa ban boyewa Attine komai ba na Bata labarin komai har zuwa kauyenmu da Danbature,ta Taya Ni murnar ganin Mijina,sannan tace kawai na bar aiki a can na dawo mu zauna tare,sabo da idan naci gaba da Zama a gidan tofa za a samu matsala Nan gaba.nima na yarda da shawarar Attine.
Attine da kanta ta shirya taje ta sanarwa Asiya cewar aure za ayi mini a kauyenmu Dan Haka na bar aiki gaba daya,Asiya dama haushina takeji yanzu sabo da Anty Maryam Bata ji wata damuwa ba sai ma murna da tayi,Sha Tara ta arziki ta hada min ta shirya kayana kaf a mota,tace Driver ya Kai Attine da kayana gida.
Duk abinda ya faru karaf a kunnen Danbature,har Wai yaji za ayi min Aure a kauye,to a kauyen Shi Kuma aurensa dake kaina fa ina Zan kaishi, Driver na tafiya tare da Attine Dan Bature ya fito a hargitse da sauri ya fada motarsa yabi bayansu Yana ganin Ina Attine zata je.
Haka suka dinga tafiya har suka je kofar gidan Attine ba tare da sun San Danbature na binsu a baya ba.
Nesa yayi parking da motarsa ya gani na sanda na fito daga gidan Attine na taimaka Mata muka kwashi kayana muna shigarwa ciki har muka Gama Driver ya tafi abinsa.

Shi kuwa Yana mota Bai tafi ba har na sake Fitowa zanje siyo danyen kifi,Yana kallona na wuce ta kusa da motar Sa Amma ban ganshi ba sam, Mahaukacin Horn ya Danna min saida na toshe kunnena,murfin motar ya balle ya fito sanye da farar jallabiya fitted yayi kyau matuka,mamaki ya kamani ya akayi yasan inda nake,kallonsa nayi shima ya kalleni kawai yaja tsaki ya koma motarsa ya finciketa a tamanin ya bar layin.
Baki Nima na tabe nayi tafiyata abina.
Ta bayana naji Karar motarsa ya shararota kamar zai takeni na matsa gefe,glass ya sauke yace ke Kinga na juyo na kalleshi yace na daina kulaki ya finciki motarsa ya Kara gaba.
Dariya ya bani sosai nayi na gaji sannan na tafi inda zanje.
Na siyo kifi na juyo kenan na sake ganin motarsa yayi slow saitina yace idan kika Kuma Fitowa ban yafe Miki ba indai ba da Izini na ba, Duk inda Zaki as from today sai kin nemeni a waya idan na yarda,wlh ko kofar gida kika fita ba Izinina ban yafe Miki ba.
Baki bude nake kallon ikon Allah,Number dinsa ya jefo min a farar takarda yayi tafiyarsa a fusace kamar zai cire titin layin.

AsmaBaffa
[9/4, 10:26 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕

51-55

Official

By
AsmaBaffa

Bayan na koma gida na bawa Attine labari,tace Oh Anya Fadila danginsa zasu yarda ya zauna dake? Abinda nake so dake ki rage ja Masa aji ki dinga Dan saurararsa ta Haka Zaki Kara Shiga ransa ya fada sosai sannan ku daidaita, hmm Attine mazan Nan musamman irin su Danbature sai da Jan aji Kinga yanda ya wulakantani a farko? kiyi dai a hankali a ilmince ba kawai ai ta Jan aji Ana wulakanta mutum wannan ba na masu ilmi bane,kiyi ajin na wise people ba Shirme ba.
Inshallah na Bata amsa muna kitchen muna shirya abincinmu.

Washe gari da misalin 5pm lokacin Attine Bata Nan taje business dinta sai dare take dawowa,banyi girki da wuri ba sai 4pm na Gama,na Kara gyara gidan tare da wanka nayi sallah,ba wata kwalliya nayi ba powder kawai na shafa da Maroon Jan Baki Na shirya cikin Riga da skert na atamfa nayi kyau dinkin kamar a jikina aka dinka,rigar me tattara da dogon hannu Wanda ake cewa kaci uwaka.

Nasha kyau Ina zaune na ebo abinci da littafi a Hannuna Ina karatun schl jibi zanyi test, knocking naji tunani na Attine ce Ina budewa numfashi na ya dauke na wucin gadi ganin Danbature yaci wanka kamar zai je fadar shugaban kasa,Kofar na tare sannan na Bata fuska nace me ya kawoka gidanmu Malam? Bai ko ce kala ba ya tureni ciki ya shigo abinsa kamar gidansu,Palon ya zauna ya harde kafafu sannan ya kalleni yaci gaba da latsa wayarsa, bance Masa komai ba Nima naci gaba da cin abincina Ina Shan Lemon Dana hada, sai da na gama na mike na kawo Masa Lemo da ruwa,kafin na ajiye yace kwashe abinki ban so sai da kika Gama koshi Zaki kawo min, Baki na tabe na kwashe na maida kitchen na dawo na zauna kasa tare da canja channel daga BBC zuwa Bollywood, ba tare da ya kalleni ba yace ki maida Min BBC News nake ji, ikon Allah na furta a fili nace Wai gidanku ne Nan da zaka zo ka Dame ni.
Chapter 29 · 0% Book details