← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 50

Sashe 3

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gashinsa yawansa ya baci gashi me santsi ga wani sajensa Wanda ya taru da Dan yawa sai bakin Nan Pink abin shaaawa.mutane suna ta kallonsa shi kuma Yana jikin bishiya a zaune ya turo lips dinsa gaba kamar wani shagwababbe,a gabansa na tsaya,Ina ta kallonsa Ina washe Baki,ganin kallon Bai isheni ba a gabansa na tsuguna tare da Kara tura Masa fuskata saitin tasa,kamar zan Shiga cikin fuskarsa.

Abin mamaki ko kallona baiyi ba kamar Bai San da mutum ba,rigarsa na Dan ja ai kuwa ya kalleni kadan ya Kara turo Dan lips dinsa ya tsuke shi tare da make kafadar Shagwaba,a fili nace ah..ah...tofa sai na tintsire da dariya mutanen ma dake kallo suka fara dariya kamar mahaukata,wani yaro cikin Yan kallo yace Fadila Dan tabo Mana gashinsa muji,a hankali na Kai hannu zan taba gashin a tsorace,ai ko ya make min hannu ba tare da ya kalleni ba,ban hakura ba na Kara Kai hannu ya bige Hannuna ya mike tsaye a fusace idonsa har ya canja kala daga fari zuwa red,Alawata na Ciro a Jakar da nake Tara kudin tallana na Mika Masa ita,kallo na yayi kadan kamar bazai karba ba sai ko ya karba,abin da ya bamu mamaki ba tare da ya bare ledar ba ya cinye har ledar a Nan muka ce yana da tabin kai,mutane kuwa Kara yanyame wajen suke an samu a tsakiya.

Kallon mutanen yayi sai ya fara toshe hanci Yana ja da baya,sai ya fara buya a bayana, idan na matsa sai ya matsa ya boye a bayana Yana leken mutane ta bayana,tsoro ya shigeni na fito daga mutanen nayi hanyar gida a guje, Abin mamaki Mutumin ya biyo Ni Amma cikin takunsa na Isa da gadara.

Gudun na daina na tsaya kawai sai ya biyoni mutane na binmu Yana buya a bayana,ban Shiga gida ba kawai na dauki hanyar wani shago cikin kudin tallan na siya Masa pure water Yana tsaye kusa Dani kamshin sa ya cika ko Ina,na Mika Masa ruwan ya karba kawai sai ya jefar a kasa da yatsa ya nuna min ruwan jarka da ake siyarwa,Baki na hangame nace Kai almubazzari Dan asarar kudi sai na roba ko Ni ban Sha ba sai kai,to wlh baka Isa ba, kudin Hannunna ya nuna da yatsansa sannan ya nuna min ruwan roba,a Shagwabe nace Kai baka San Ba kudina bane! Na Hajiyarmu ne dukana zatayi daga wannan Ni dai bazan siya ma ba,Dole na mika kudi aka bani na roba na bashi,sai na ga ya kasa budewa Yana ta gwagwagwa,na karba Ina masifa Kato da Kai Amma baka iya abin duniya ba ungo na sa Masa bakin robar ai kuwa ya shanye ruwan tas,Allah sarki kishi yake ji, biscuits ya nuna min Nan na gane yunwa yake ji na siya Masa biyu, Dana bude na bashi Bai iya ci da kansa ba Haka na bashi da kaina ya cinye, nace to ka tafi yawonka Ni gida zanje duk ka cinye min kudi na Ina ta masifa Amma yayi mursisi ko a jikinsa, Dana tafi Nan ma Bina yayi a Haka har kofar gidanmu,nace ka biyo Ni su Salman zasu koreka ne yaro ba ruwana Ni.

AsmaBaffa
[9/4, 10:25 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕

2

Official

By

AsmaBaffa

Bai ce kala ba Haka muka je har kofar gidanmu babu kowa duk suna Masallaci sallar Magrib, Haka na shige gidanmu bayan na dauki kudina Dana kashewa Dan Bature na biya Hajiyarmu da kudina da nake Tarawa,muna zaune a tsakar gida Ana cin abincin da dare kawai sai ga Dan Bature ba ko sallama ya shigo kamar gidansu,Anty da yaranta tare da Hajiyarmu tuni suka fada daki da gudu tunaninsu Bature ne Dan wani fari ne tas ga uban kyau kamar shi yayi kansa,harsu Salman sunji tsoronsa kasa motsi sukayi,Abbu dake gefe saman carpet jikin dakinsa shine yayi ta maza ya daka Masa tsawa Kai lfy gidan ubanwa zaka je Haka? Shuru Babu amsa sai ma toshe kunnansa da Bature yayi sannan ya hade Rai tare da turo lips irin an takura Masa baya son hayaniya, dube dube ya fara can ya Hangoni saman katuwar Shimfidar tabarma Ina cin tuwo,a hankali cikin takunsa na birgewa ga uwar gadara gefena ya zauna kusa Dani a saman tabarmar,Su Anty da yaran gida sai lekenmu sukeyi,mamaki ya kamasu ganin banji tsoro ba,Baki Bude Abbu yake kallon mu, Su Salman ma Haka,Kwanan tuwona na tura Masa gabansa,ya zubawa kwanon Ido tunawa nayi baya iya cin Abu da kansa,Hannu nasa na yanke tuwon sannan na Kai Bakinsa ai kuwa ya bude bakin na saka Masa ya fara taunawa kamar baya so da gani Bai Saba ci ba kawai Dan Yana Jin yunwa ne yake karba Yana ci.

Muryar Abbu ce ta bamu tsoro yanda ya daka Mana tsawa,Iskancin naki ya Kai Haka dama? Shi yasa nake murna da Allah Bai bani Yara Mata ba sai maza ke kadai mace Amma sai jawo min magana kikeyi to Zaki ci ubanki aure zan Miki na Dole Kuma wlh kika sake da mahaukacin Nan zan hada ki.
Kayi Hakuri Abbu taimako fa nakeyi wlh yunwa yake ji,Dan Allah ku daina ce Masa Mahaukaci duk Wanda ka ciyar Allah zai baka Lada ko dabba ce,Jar uba lallai zan karyaki a gidan Nan Fadila cewar Abbu, Hajiyarmu ce ta fito daga daki a tsorace ta kalli Dan Bature tace Kai tashi ka fitar Mana a gida,kallonta yayi sai ya koma ta bayana ya buya Yana leko da kansa ta kafadata, yau nake ganin Dan iska wannan ko a fili tantiri ne sai shegen Jan kunne,ga uwar Suma kamar dakin bukkar fulani.

Salman ne yazo ya fara kokarin Jan Bature zai kaishi waje Amma ya kasa Kuma yaki fita sai ma like min da yake faman yi a bayana, rada Salman yayi min a kunne cewar tashi ku tafi waje ki jashi ki San yanda zakiyi ku rabu mu rufe gidanmu kafin ran Abbu ya baci wlh duka Zaki ci kin sani ko ya Miki auren Dole kuma Kinga mu baza muji dadi ba.

Mikewa nayi na dauki wani kwanon na zubo Masa tuwo da Miya na rufe da murfi,Hajiyarmu tace a kwano na me kyau Zaki zubawa Mahaukaci abinci?ubanki ne ya siya min,to kudina nasa na siya Dan gwal ne da sai a kwano me kyau zaici?, Mayar ki zubo Masa a wannan tsohuwar langar wacce ta kwankwatse idan ta Bace ma taje,amma kwano na me kyau sabo a bawa Mahaukaci abinci a ciki ai kinyi karya Yar Nan,Anty ta leko tace Wai ita iyayi ga Yar me kudi komai nata sai anyi karya Yar karya kawai shine harda daukan sabuwar silver.

Bance komai ba na canja kwanon lokacin Bature ya biyo Ni har kitchen Yana buya,Hajiyarmu ta rike haba tana Salati tace wannan yaron mashahurin Dan iska ne,Dan ubanki wlh ki kiyayeshi,Anty ta karbe da Allah ya kiyaye Kar ya dirka Miki ciki kafin ta rufe Baki Abbu yace da kuwa na kasheta da Hannuna.

Bance musu komai ba nayi hanyar waje ai kuwa da sauri ya biyo Ni mun wuce Abbu kenan ya Sa Muficin da yake fifita dashi ya kwalawa Bature a kafafu Amma kamar dutse ya daka,Abbu ya sake rade Masa kafafu sosai da zafin gaske,Bai ko kalli Abbu ba yabi bayana muka bar gidan.

Can nesa da gidanmu saman wani dakali na zauna shima ya zauna a gefena,tuwon naci gaba da bashi ya ci da yawa kuwa nasan Yana bukatar ruwa haka na tafi shago Yana Bina a baya kamar jela na siyo pure water biyu na bashi daya da kaina wannan time din Bai nuna ruwan roba ba.

Saman dakali muka zauna na dinga Masa magana Amma Bai ce kala ba,nace Dan Allah ya sunanka? Yayi Shuru ba magana,ko Kai kurma ne? Nan ma Shuru, maganata naci gaba da fada Dan Allah ka daina zuwa gidanmu wajena Abbu na zai Duke Ni,Amma ban San Ina zaka kwana ba,ga hadari a gari tabbas ruwa zai zaneka wayyo ya zanyi na taimake ka ni. Haka dai na karaci surutuna na mike zan tafi gida ganin dare yayi da yawa,na gargadeshi Kar ya biyo Ni.

Nayi Nisa da tafiya kawai na hango shi Yana Bina a baya Nan na kwashe da gudu na fada gidanmu sannan na kulle kofar har Hawaye nayi na tausayin bawan Allah yau nasan idan anyi ruwa ba shakka zai zaneshi.

Shi kuwa Yana karatowa yaji gidan Gam a kulle sai ya zauna a bakin kofar gidan namu ya fara gyangyadi bacci ya kwasheshi.
Misalin Sha biyun dare na kasa bacci tunanin Dan Bature nakeyi gashi tuni an fara ruwa nasan ruwa Yana dukansa yanzu hawayen tausayi ya zubo min,a hankali na tashi na fito a dakina na lallaba naje na bude kofar gidanmu a hankali, Aiko na ganshi a zaune Ana tsinka ruwan sama kamar da bakin kwarya shi kuma Yana zaune ya dunkule waje daya ruwa na labtarsa Yana ta karkarwa.

Salman ne ya fito yaji kamar an bude gida tunaninsa barayi ne sai ya ganni Ina leke,yace Sister lfy?, Nace leko ka gani,ya leka yaga Bature shi kanshi ba karamin tausayinsa yaji ba,yace taimaka Masa ya kwana ko a zaure ne Amma Da Asuba ki zo ki fitar dashi kafin Abbu ya tarfa ki.

Dadi naji sosai shi Kuma Salman ya juya ya koma dakinsu,Da gudu na fito na Karasa inda Bature yake na Dan bugi bayansa da Hannuna ga ruwa ya Kara tsugewa, da sauri ya juyo ai kuwa ya ganni ba shiri ya mike tsaye duk da duhu Amma ya gane nice,karo na farko da naga Dan Murmushinsa kadan,ban jira ba kawai na figi hannunsa me Masifar laushi muka Shiga gidanmu, Salman ne ya kawo min wani kayansa Shadda Riga da wando Tasha guga yace gashi ki bashi ya canja Kar sanyi ya Masa Illa,sannan ya dakko min wani bargo guda biyu,ungo ki Masa Shimfidar da daya ki lulluba Masa,na fara Masa Godiya Ina murna yace ke dai kiyi sauri karfa a Kama mu ya juya dakinsu.
Chapter 3 · 0% Book details