← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 50

Sashe 49

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallamarsa naji tarbar Dana Saba Masa banyi ba yau yasan Akan me nake fushi,kusa Dani ya zaune tare da ajiye ledojin shopping a gaba na,yace ga dinkunanki na karbo Miki,sannan ga wasu kayan Nan,dama fa dinkunan biki ne Kuma kace bazan je ba me zanyi dasu,Ni nace karki je? Kullum Zan kaiki da safe da yamma na dakko ki,rau rau nayi kamar zanyi kuka nace yanzu kamar Attine bazan kwana ba? Sannan Safarau ko yaushe tana hanyar zuwa wajena tare mukayi shirye shiryen bikin Amma ace bazan je na kwana ba.
Mene ne abin kwana pls tunda Zan kaiki me yasa bakya Jin magana ne,da yaron ciki Zan Bari ki tafi unguwar kwana kullum da zazzabi kike kwana fa in kin tafi gidan su wa zai kula dake?
Indai wannan ne Zan kula da kaina ga Attine ma,Kai ya girgiza yace to a dawo lfy ya mike tare da haurawa sama.

Ni dai ko a jikina shiri na fara yi kawai Yana kallona ransa a matukar bace yaje yaci abincinsa na Gama shiri na tsaf na fito nace na shirya,jikina sanyi yayi ganin yanda yake fushi Kar na tafi ba a son ransa ba Allah yasa wani abun ya sameni.
Bedroom na koma na ajiye kayan Dana shirya na dawo Inda yake a Palo na zauna gefensa da sanyayyar muryarta nace na fasa zuwa Allah
ya kaimu ranar Event din sai ka kaini kamar yanda ka tsara.
Tausayina yaji sosai yayi wani Murmushi lafiyayye yace ko kefa Allah ya Miki albarka Ameen nace na kwanta a jikinsa.

Kamar yanda yace Haka ya kaini Dinner abin mamaki Ashe Saad Shi zai auri Safarau,a Company nasu take aiki shine Manager kuma,Lokacin yaso Ni a ransa Amma Allah ya taimakeshi ya Kai zuciyarsa nesa tunda suka hadu da Safarau Kyakyawa itama kusan Muna yanayi da ita ya kamu da sonta gashi yanzu,Munsha shagalin biki lfy mun Gama lfy.

Bayan wata biyu Tunda Saddiqa ta koma dakin mijinta tana zaune lfy tana kula da mijinta suna soyewa yayin da Alamin Wanda ya taba kidnapping dina suke soyayya da Meena kanwar Ice.
Saura kwana biyu bikin Ya Salman,Musa da Mahmood Dan Kawu Salisu.
Wannan karon Bai hanani zuwa ba cikina Yana wata biyar ya fara Fitowa ma Amma Haka naje Gombe a jirgi,shi da Daddy Kuma zasu zo daurin aure,Mum ma zata zo bikin da Meena,Saddiqa da wasu kannensu Sunyi min Kara sunzo, anyi biki lfy an Gama lfy,dama su Abbu sun koma sabon gidansu a birnin Gombe,sannan har kauyenmu naje ganin dangi.
Sai da aka Gama komai Dani sannan na dawo gida,lokacin Kuma tuni su Mum sun Gama Idda.

Nanee saurayinta na farko da suka Sha soyayya tun saurayi da budurwa yanzu shima Hamshakin me kudi ne yarans hudu kacal sabo da baya Haihuwa sosai a Nan birnin Adanawa, Matarsa kwana Nan ta rasu Yana Jin labarin Nanee aurenta ya mutu dama tsohuwar soyayyar tana Nan yazo,itama dake tun farko shine farkon soyayayyarta akansa tasan so,Allah yayi Bata aureshi ba yanzu kuwa Yana zuwa ta Amince ai kuwa ranar wata jumaa aka daura musu aure ta tare,yaranta dake Lagos labari kawai suka ji Sunyi bakin ciki tare da kishin Daddy,sanda Labarin ya iske Danbature shima baiji Dadi ba yaso Bata yi gaggawa ba Daddy ya dawo maybe ya maidasu dakinsu,Koda ya buga Mata waya sai hakuri ta basu kawai.
Bayin Allah Kar kuyi zaton Dan Mace ta Tara Yara gidan miji baza su iya rabuwa da Mijin ba,sannan komai tsufanki matukar kika fito daga gidan miji to da yawa tsofaffin samarinki sai sun dawo,wani dama Allah ya rubuta sai kin aureshi Amma sai kinyi Aure kin fito sannan shi ya aureki kaddara kenan Allah yasa mu Dace.

Karimatu kuwa babanta ya matsa Mata yace da sauran kuruciyarta ta fito da miji cikin zawarawanta ta aura a hakika ita Daddy tafi so ta koma gidansa Amma Shuru Bai ko nuna alamat zai iya maidasu ba,Dole ta yanke Shawara cikin Zawarawanta ta fitar da wani Me kudi Dan majalisar tarayya yayi sai uku ya rike mukamai da dama sannan yanzu ma shine Akan mulki a Maiduguri,Aiko ta aureshi bashi da wata matsala Kuma Yana da Matarsa daya da yaransa 7.
Sai labari muka Kara ji Karimatu ma ta tare a gidan mijinta Daddy Yana can Bai sani ba,ko a waya ba Wanda ya sanar Masa.

Mum kuwa so take ta koma wajen iyayenta can Paris Amma Ice yace wlh baza ta koma yanzu ba,Mum ta Gama Zama cikakkiyar salihar mace Sannan ta koma Islamiyyar Matan aure tana zuwa sosai Bata da aiki sai karatun ilmin islama, muna zaune lfy abinmu Ras,yayin da cikina ke Kara girma.

Cikina ya cika wata takwas Daddy ya dawo Nigeria yayi kiba kuruciyarsa ta kara Fitowa,har gidanmu sai ganinsa mukayi katsam lokacin Mum tana Islamiyya dagani sai Ice,Daddy dawowa ba sanarwa sannu da zuwa muka karramashi na cika Masa gabansa da kayan ci da Sha,bayan mun gaisa mun nutsu,Daddy yace Aliyu ya kamata na dawo da matayena nasan yanzu sun koyi darasi,ba Wai bana sonsu bane abinda sukayi yasa na musu Haka sabo da Nan gaba su kiyaye ya kake gani Kai? Aliyu yaji ba Dadi sun Riga Sunyi aure,Daddy yace musamman Asiya tayi hakuri Dani ya Dace ace ita na fara maidowa dakinta taci moriyata kafin sauran,Mum kuwa Ina sonta fiye da kowa,tsakani da Allah bazan iya hada sonta da kowa ba Allah ne ya jarabceni da hakan,nayi mamaki Kuma da ba ita ce tayi yunkurin kashe ni ba sai Asiya Ido da Ido abin ya girgizani.

Daddy sai dai hakuri Amma Nanee tayi aure ta auri tsohon saurayinta,Haka Karimatu ma tayi aure tuni,wani Dukul Daddy yaji kishi sosai yaji da takaici,da yasan Haka zata faru bazai sake su ba,Yana son matansa Kuma shima ai Yana da laifi,kamar ya kurma ihu Haka yaji musamman ma Nanee,da kyar ya daure yace Mum dinka fa? Danbature yace batayi aure ba Amma taso ta koma Paris tayi aurenta itama Ni na hanata,su Nanee kuwa Daddy kasan da nasan zasu yi aure wlh bazan Bari ba to ban sani ba Kuma Haka Allah ya tsara.
Daddy yaji Dadi Jin Mum batayi aure ba sabo da yafi sonta da kowa Amma da tayi aure da Bai san ya zai yi da rayuwarsa ba.

Daddy ya mike yayi Mana sallama zai tafi kawai sai ga Mum ta dawo daga Islamiyya sanye da hijab dinta,Ita kanta Tana kaunar mijinta,har kasa ta duka tare da gaidashi ya amsa da Faraa Yana mata kallon so ya fita abinsa. Ice yabi bayansa suna magana sannan ya tafi.

Mum ya samu Ya sanar Mata za a sake daura aurenta da Daddy,Murna kamar tayi me sai Godiya take ga Allah,sabo da Murna kasa daurewa tayi ta sanarwa iyayenta a waya Nima da nake surukarta sai da ta fada min Ni kaina Dana ji labarin naji Dadi matuka.

Jumaa na zagayowa Bayan an idar da sallah aka maida Auren Mum da Daddy.duk yaran Daddy ma sunji Dadi,lokacin da labari ya samu Nanee da Karimatu Basu ji komai ba sabo da mazajen da suka aura Sunyi Dace suna Jin Dadi a wajensu sai dai sun so a hannun Daddy suke don yafi mazajen nasu komai,Amma kaddara Haka take Allah ya tsara akwai wanda zasu sake aura.
Daddy gidan sai da ya canja komai ya dawo sabo da ba Lallai ma ka gane gidan bane yasha gyara ko Ina.
Mum Tasha kyau anyi gyaran jiki etc sannan Da kansa Daddy ya dauki Abarsa,Hajjo tayi farin ciki danta Bai Zama gwauro ba.ana ta murna da Jin Dadi Mum ta koma ta rungumi yaran gaba daya da yaran Yan uwa take rike su sosai take basu tarbiya komai na gidan ya canja rayuwa suke me Dadi,tarbiya da ilmi.

Cikina ya cika wata Tara cif cif yayi girma,bana komai na aiki sai girki shima girkin idan Danbature Yana Nan shi yake Mana da kansa,Addua muke Allah ya sauke Ni lfy,Mum da kanta tazo ta daukeni na koma gida wajenta da Zama tana kula Dani Kuma abin farin ciki Danbature Bai Hana ba shi kanshi Yana son na zauna inda za a kular Masa Dani sai dai kullum ya tare a gidan.
Saddiqa ta samu ciki,Haka sauran da aka musu aure tare suna da ciki,Safarau ma Haka,muna ziyartar juna Ana mutunci,Ya Salman tunda sukayi kudi suna yawan zuwa wajena,Haka kishiyar Hajiyarmu Anty Amarya ta gyara halayenta har a waya take kirana mu gaisa,tace sai na haihu zata zo,su Abbu sun waye sun gyara halayensu yayin da Karimatu da Nanee suke zaune lfy gidan Mazajensu.

Yau Saturday cikin ikon Allah na tashi da Nakuda akwa kwashe Ni sai Hospital na Dr who, Danbature sai share kwalla yakeyi na tausayina ya rasa inda zai sa kansa, cikin hukuncin Allah ban Dade ba Allah ya saukeni lfy na haifi Dana Kyakyawa Namiji katon gaske,Murna wajen Yan uwa da abokan arziki ba a magana,da yamma lis aka sallamemu Muka tafi gida jaririn Yana Hannun Ice yaki Bari ma a dauke shi kana karba zaice kawoshi to ya huta yasha wahalar hanya zuwa duniya tafiya ce me Nisa.

Kafin kace me gida ya cika Ana ta sintiri,washe gari kamar bani na haihu ba naci wanka da kwalliya muna zuba kamshi, Danbature Yana kwance kusa Dani Yana ta bacci,Mum dake Baturiya ce Bata ce ya fita ba ko ajikinsu Haka ake ta zuwa Ana fita sai in baza ka iya ba ka fasa shigowa,nayi nayi dashi y aki yarda.

Suna saura kwana biyu dangina Yan Gombe maza da Mata sunzo har Anty Amarya,baza ayi wani bikin suna ba,ranar suna yaro aka sa Masa Fadeel an kashe kudi Sa Kato da raguna biyu aka yanka, Ice Bayan suna da kwana uku Baki duk sun tafi ya nemi Mum da ta barni na koma tace sai nayi 40days naje Gombe na gaida dangi Zan koma,har yayi fushinsa ya gaji ya hakura.

Bikin Meena da Alamin Yana karatowa, Ni Kam Ina ta gyara jikina har nayi arbain naje Gombe nayi 3days na dawo na zaga dangin miji dake Lagos,da Safarau sai Attine sannan na koma dakin Mijina muka Shiga Holewa da soyewa ba Kama kafar yaro.
Anyi bikin Meena lfy an kare.
Chapter 49 · 0% Book details