← Book details Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 50

Sashe 35

Hadin Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fita Mum ta shigo tare da Daddy ta ruko hannunsa tana Masa wata karairayar karya,saida suka zauna zatayi serving Nasa taga ba abincin data girka bane,tsoro ya kamata ta kwala ihu tare da ja baya,tace Aljanune suka canja min abinci ba wannan na dafa ba wlh,Leka kwanon Daddy yayi yace hmm haba Maryam kawai dai kinyi girki baiyi Dadi ba Zaki ce Aljanu to wa zai canja Miki Ina kika taba Jin Haka? Kwanon ya jawo tare da cewa ko mene tunda kece kika dafa abar kaunata Dole naci, ya zuba abincin yaci abinsa Haka sabo da yunwa yake ji bazai jira ba.
Takaici ya Kama Maryam to Wai me yasa Plan dinta yanzu duk rushewa yakeyi Baya tafiya dai dai irin da?.

Part dinta ta koma tare da Kiran bokanta tana bashi labari yace na fada Miki danki Yana da aure,sannan kinyi sake Yana saduwa da Matarsa ta sunna,komai naki bazai yi dai dai ba sai kin raba aurensu.
Ki San yanda zakiyi kisa shi gaba Dole ya fada Miki Matarsa kafin mu san yanda zamu Raba su.
Kan Mum ya Gama kullewa fa ta rasa abinyi tana jira Ice ya dawo kawai ta sa Dole taji gaskiyar magana.

Washe gari da safe kasa bude idona nayi yayi yayi na ki bude idona,wayarsa na kunne Asiya ta kirashi da safe Haka ba lfy kawai yace ya daga Kiran,Hlo Nanee, labari ta bashi Aunty fa tasa an Kori yaran gida, kiyi hakuri Nanee bani da time yanzu sai na dawo Dole aiki ya min yawa,yana magana Yana kissing wuyana yanda baza a ji ba,mantawa nayi nace zanyi wanka,da sauri ya datse kiran sannan ya kalleni yace kin manta za a kamamu,au na furta tare da rufe bakina.
Kiranta yayi back suka Gama maganarsu, karshe tace naji kamar Maganar mace dazu,Da sauri yace Babu gaskiya Nanee kunnenki ne,ok sai munyi waya.
Tana kashewa ya cire layikansa Baki daya yasa sababbi a wayarsa yanda baza a sameshi ba sai idan shi ya Kira, sannan ya kaini toilet nayi wanka da Brush na fito shi Kuma tuni ya kashe wayoyinsa tare da komawa toilet wacce take wani dakin daban.
Bayan munci gayunmu na gaske da kansa yayi Mana breakfast tare da bani a Baki da kansa,ba laifi na Dan fara sakin jiki dashi.
Shi ya gyara part din Ina kallonsa ya hanani daukan ko tsinke har ya Gama ya dawo Palo inda nake, Hannuna nasa tare da sarkewa da nashi Ina Masa wani kallon so kasa hakura yayi ya Shiga kissing dina Yana shafa Albarkatun kirjina a hankali.
Zuciyata nake wa fada kan ya kamata na saki jiki da Mijina muyi rayuwa me dadi,na daina kunya da wani noke noke.

AsmaBaffa
[9/4, 10:26 PM] Sis Asma: 🏕HADIN KAI🏕

66-70

Official

By
AsmaBaffa

Ga page dinku
mutanena
Sadiya Sadiq,Fateema IG, Mummy Abbuna,Hajara,Maman Khalifa,Mmn bilkisu.

Wannan page ya min Dadi.

Ganin zai wuce gona da iri na dakatar dashi ta hanyar riko hannunsa da nawa a hankali nace uhm..uhm..pls yanlabai a taimakeni na warke,Murmushinsa me tsada ya saki tare da kallona irin na so da kauna yace Amma zuwa dare ai Zaki warke ko? Ido na zaro darefa kace? Ai sai Nan da 1wk Zan warke idan ma fa na warke da wuri kenan.
Hmm fada kawai kike yaushe zan iya jira sai kinyi 1wk Ina kallonki bazan iya ba yanda kike din Nan so sweet kwana daya ma yayi min yawa,yanzun ma Baki ji yanda nake ji ba, da Sigar Shagwaba nace Ni Dan Baturena na farko ba Haka yake ba da zalama wannan Kai ai lalata wurin zakayi da wuri.

Dariya ya Shiga yi min sosai Yana kallona yace dama Haka kike? Kara fada min naji Ina Zan lalata? A Shagwabe na Dan dakeshi a kirji da wasa Ina dariya,Ina a zaune ya kwanta a saman kujerar tare da daura kansa saman cinyata kana yace kinsan me ya bani dariya lokacin Dana tuno da Kauyenku time din bani da hankali dana Shiga cikin Matan Kai Amarya lokacin ban San me akeyi ba kawai ke nake kallo Ina tunanin ina za a kaiki,dariya nayi nace Ni Kuma lokacin Dana ajiye maka jiran tallan goro na ka bar Yara sukayi Masa kaca kaca.
Hannuna na daura saman Kirjinsa Ina Wasa da rigarsa yace aike kinfini ma Shirme time din kin San brain dina da matsala kika ajiye min goro Wai na jire Miki,hhhh muka fara dariya tare nace Wai mene Asalin zuwanka kauyenmu ne? Bazan iya tunawa ba nasan dai Ina mota tare da Driver wasu kamar Yan fashi suka taremu a Nan suka min wata Allurar tare da Sa Ni a wata motar suka tafi Dani abinda nake iya tunawa ke Nan sauran ba a hayyacina nake ba har nazo kauyenku wlh ban sani ba.

Tausayinsa da kaunar sa ta Kara Shiga ta sunkuyowa nayi da kaina zanyi kissing din lips dinsa kafin na Karasa ya turo min Dan lips dinsa jajir dashi Murmushin da ban shirya ba nayi tare da janye kaina,fuska ya Bata da Wasa,Kara mikawa nayi kamar zanyi ya Gama lumshe ido Yana jira yaji duf na janye tuni, cike da Shagwaba kamar mace yace pls...Yar dariya nayi nace to yanzu ba Wasa na Mika kafin na Kai ya sakalo wuyana da hannunsa ya rike Kam ya Shiga tsotsar lips dina.

Mun Dade a Haka kafin na kalli time 12pm nace abincin Rana ya kamata na daura Mana abinci, muna amarcin Zan Bari kiyi abinci na rigada nayi Order kullum za a kawo safe,Rana,dare sai Nan da 1wk Zaki Fara min abincinki Mai Dadi.
Fari nayi da Ido me Jan hankali,Ido ya zuba min kawai ya kasa daina kallona kusan Haka muka yini sallah ma tare mukayi abarmu gwanin shaawa,na fara sakin jiki dashi ba laifi sabo da yanda yake nuna min kauna Yana wani mugun ji dani.

Aunty Maryam gaba daya ta Hana kanta sakewa,ta dami rayuwarta da bakin cikin Rashin ganin Danta Aliyu Wanda burinta ya dawo ta sashi gaba Dole ya fada Mata wace Matarsa,yayin da ta Kara takurawa Asiya ta hanata sakewa sai faman zuga Daddy take Dan ya rabu da Asiya ko ya Kara wulakantata, Asiya Bata da aikin da ya wuce ta Shiga daki taci kuka tare da yin addua, sabo da yanzu ko Daddy ta gaisar ko kallo Bata isheshi ba,ta Gaza gane zaman wa takeyi a gidan abin da zafi ace mijinka tsakaninka dashi sai kallo,ta Dade da mantawa ita mace ce ko Namiji.
Yau ta gaji tace gwara taje ya Bata kwananta ko ya saketa.
A bedroom dinsa ta sameshi Aunty Maryam na gefensa,Karimatu tana can baya a zaune suna Hira sai nishadi sukeyi, Asiya na Shiga ya Bata fuska,Wuri ta samu ta zauna itama tare da gaida shi ko kallonta baiyi ba.
Wajenka nazo Daddyn Yara so nake ka dubi girman Allah sannan da dokokin da yasa na hakkin mace kan mijinta karfa ka manta ba Haka kawai Allah yace ayi aure ba sai da yasa dokoki,Ni ka wareni baka sauke min hakkina na tsawon shekaru ba daya ba, Ice shine ke min komai,ba Ice ke aure na ba Kaine idan har baza ka iya ba to ka sawwake min ko Kuma ka sauke min hakkina kamar yanda kakewa sauran abokan zamana, cike da ladabi ta Gama bayaninta
Budar bakin Daddy sai yace to ai da Ice din kika aura ya fiye Miki,Maganar Bata yiwa Matan Dadi ba,ba Asiya kadai ba har Karimatu da Aunty Maryam sunji rashin dacewar Maganar Daddy.
Karfa ka manta Danka ne Ice kake hada matarka ta sunna dashi cewar Karimatu uwar masifa,Dakatar da ita Daddy yayi tare da zura hannu a Aljihu ya zaro kudi dubu biyu Rak ya watsawa Asiya sannan yace gashi Nan nasan darajar kwananki Bai Kai 2k ba na siyi kwanan naki Kinga kinci riba tashi ki bace min a gani.
Asiya Bata San sanda Hawaye ya wanke Mata fuska ba ta mike ta bar Masa kudin tayi tafiyarta.

Farin ciki ya Kama Asiya,Karimatu kuwa harda munafuncin gaskiya Daddy Bai kamaceka Haka ba,a ranta Kuma tana sheka dariyar murna.
Asiya yau kuka ta shashi,Saddiqa taga tana kuka ta Shiga part dinta taji tausayinta.
Washe gari Dr who yasa Saddiqa gyaran dakinsa kasancewar yaga ta Dan goge ba irin da ba.da murna ta amshi key tace yau zaka ga gyaran da baka taba gani ba likitan yan duniya,Haka take ce Masa yanzu Dan taga Yana shaye shaye da neman Mata shike Nan tace Dr ne Amma na Yan duniya.

Bayan ta Shiga bedroom din tace yau gyara iya gyara zatayi Wanda har kyauta sai yayi Mata,sai da ta Gama da toilet neat sannan tace yau katifar har ita Zan dage kwalima zanyi Masa,ta dage katifa tana share kasan bed sai taci karo da layoyi na bokanci,ga wata Yar tukunya ta kasa daure da Jan kyalle,tarkacen iri iri,Saddiqa tace aradu Ana tsafi a gidan Nan,Nan ta rotse tukunya,sannan ta farke layoyi komai sai da tayi Masa warka warka sannan tace ance idan akayiwa tsafi fitsari Yana karyewa ta samu tarkadun laya ta hade kansu tare da tsula musu fitsari 😅 sannan ta kwashe ta zuba a toilet tayi flowshing ta share komai ta zuba a dustbin tare da goge ko Ina,har fitsarinta data tsula kadan ta gyara,Dr who yasa ayi gyara Ana Masa fitsari a dakinsa, Nan dai room ya fito fes Yana kyalli tasa turaruka ta kulle ko Ina ta fito da sharar ta Kai waje ta watsar Dan ma Kar ace itace tayi barnar kayan tsafi.
Chapter 35 · 0% Book details