Sashe 9
Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zai sadaka da cikin gidan Amani ta ja tunga da akwatin ta ta tsaya ta daddage ta rusa ihu.. Na shiga Uku Didi na, Dada da Safna suna shirin kasheni don an ga bani da Uwa wayyo Allah na Hajja Didi da tada sallahr azahar d inta kenan ta yi saurin sallame sallahr ta fito a guje tana furta Wa nake ji haka kamar muryar magajiya Uban waye zai kashe kin? Buzuwa da Mijin Buzuwa Amani ta amsa mata da irin sunan da take kiran Moddibo da matar tasa.. Didi ta ce Jar uba, to shigo magajiya in dai ina raye ba mai tab a ki ya kwana lafiya mik o min Salula ta ki kira min Mijin Buzuwar na ji dalili JIKAR NASHE HADARIN GABAS NAZEEFAH SABO NASHE. 08033748387. Salular ta mik a mata sai kuma Hajja Didin ta wurga mata harara tana furta Duba kiga zaki ga k wallo guda shidda itace lambar Uban naki.. Amani ta kuwa duba sai ta ga an yi saving da hotunan ball guda shidda murmushi ta saki wato ta inda Hajja Didi take gane numberr yaranta kenan. Dahda shine d a na shidda a wajen Didi ya biyo bayan mata biyar cur! Ta danna numberr kafin ta saka a handsfree don ta san a haka Didin take waya. A duk sanda zata duba wayar sai Didi ta canja wani abin da yake banbanta mata yaranta. A da tambarin hula ce alamar da take gane Dada, yanzu kuma ta Mayar da shi 6Balls. Dahda da yake tsaye kan Imani da take wani irin kuka ya kai dubansa kan wayar hannunsa yana d an tsaki Ba zaki min shiru ba ne? Ta yi k asa da kanta kawai ba don ta daina kukan ba still idanunta na zubar da hawaye. Yana ganin numberr First Love kamar yarda ya yiwa Didin saving ya d an saki guntun murmushi don ya san yau kam tunda ya tab a Magajiyar Didi ba zaman lafiya. Wayar ya kara a kunnensa yana k asa da muryarsa kamar yarda ya saba Hajja Didi Tsaya Moddi ban buk aci gaisuwarka ba, Uban me Magajiya ta yi ka koreta daga gidanka? Ya d an fesar da hucin numfashi yana murza goshinsa abinda ya zame masa al ada, sannan cikin wata murya da bata fiye fita sosai ba ya furta Bata gaya miki irin rashin kirkin da take a gidan ba? ta fitini kowa ita shikkenan ba zata zauna lafiya ba? Bata gaya min ba, ba kuma na buk aci a gaya min d in ba, yo Ai yarinta ce kuma kowane yaro da irin yarinyartarsa abu guda da zan gaya maka ana iya canza mata banda d a balle kai da sukkenan k walli biyu Jalla ya baka, a haka ya kamata ka kula da su? To kazo yanzu ka d auketa Ai na sha gaya maka ba ta yarda za a yi kana raye ace y anka ba zasu zauna a gidan ka ba saboda son zuciya irin na matarka to bata isa ba gida dai gidan Ubansu ne sai dai ita Buzuwa ta fice fit daga gidan. Mintuna ashirin na baka kazo ka d au Magajiya Ka mayar da ita gida .. Zan kuma zo har gidan na ja kunnen buzuwa.. Daga haka ta zame wayar a kunnenta ba tare da ta kasheba don yana jin ta ta ce Yi shiru kin ji Magajiya yanzu zai zo ya Mayar da ke, ba a yi matar da zata hanaki zama gidan Ubanki ba.. Ni gaskiya ki daina ce min Magajiya, Ni wallahi Dahda ya cuceni da ya saka min sunanki Ai inye ni kike gayawa haka? Bayan na gama kwatar miki y ancinki yanzu.. Dahda da yake jin komai ta cikin wayar ya saki murmushi a zuciyarsa ya ce da din abin kema bata kyaleki ba. Wannan yarinyar lamarinta sai addu a sai kace Mai jinnu. Ya saka wayar a aljihunsa yana kallon Imani ya ce Sai ki rufe min baki yanzu zan je na d aukota ke kanki wahalar da ke take amma koda yaushe kin fi son ki Ganki a tare da ita. Ya saki tsaki yana furta ranar da aure zai rabaku zan ga ya zaku yi? Iman dai murmushi take sai a lokacin hankalinta ya kwanta jin zaa d auko mata Amanin. Ta bi bayan Dahdan da kallo da ya fice cikin shigar black Jallabiya da ta masa kyau sam ba zaka ce Dahdan ya diresu ba wani irin murjajjen jiki ne da Shi mai kyan gaske da kullum baya tsufa ko don abin ya ha du da arziki ana kuma cin mai kyau Ta shige kitchen don k arasa abinda take ranta ta furta Saura Inna Talatu In sha Allah itama sai ta dawo a yau. Ta kori Inna Talatu ma ta ce a yau ta bar mata gidanta. Didi ta ware ido tana furta Ita buzuwar? Eeh to lallai lamarin nata azimin ne, ban san sanda da na haifi Moddibo nace mata na bar mata shi ba? Irin wannan iko haka da k afafa sai kace ita ta min wahalar Moddibon? To Bari yazo na ji ko shine ya sahhale mata ta dinga ikon da ta ga dama a gidan. Talatu kam ko bayan raina ba zata bar gidan Moddibo ba, matar da tun daga k uruciyarta take wahala da ni sai kawai don Moddibo ya yi arziki ya auro Hurul aini sai ta koreta bari yazo na ji dalili? Amani ta saki murmushi don ta sake kunna Didi ta furta Didi wai wacece Uwargida ne da Mamanmu da Buzuwa? Didi ta saki tsaki don ko zancen bata so ta furta Allah dai ya gafartawa Uwarku mace ta gari salihar baiwa. Ita mai sunanta Ai kwafinta ce kwabo da kwabo Ke kuwa ba wanda kika gado sai Dijatu itace na sha wahala da ita tana yarinya kai Allah dai ya yafewa Dijatu amma ta yi abin da tayi lokacin yarinta shi yasa nake cewa Moddi ya k yaleki kema zaki daina duk da har yanzu idan Dijatu ta tubure sai kowa ya ji a jikinsa Sallamar Dahda ce ta katse musu hirar. Didi ta amsa a k asan mak oshi Amani kuwa ido ta zuba masa tana hango yarda ya gimtse fuskarsa kamar bai tab a dariya ba. Tashi Magajiya ki samo masa bulala don a fuskarsa na hango so yake da ni da ke ya rufe mu da duka, idan banda haka meye na shigowa fuskarsa a turb une kamar dai an sanar da shi na mutu Moddi d an murmushi ya yi ya zauna a gefenta yana kama hannayenta ya furta Allah ya rufa min asiri ba dake nake ha da rai ba, ni ba zan dakeki ba amma idan aka cigaba da tafiya a haka Magajiayr taki tana daf da fara dukan mu ni da matata Didi ta ware ido tana furta Allahumma ajirni! Mugun fatan da kake mata kenan, to ba zan ga wannan ba, d a dai kiwonsa Allah yake bawa Bawa, idan ka k i kula da shi Allah kai zai kama, kuma gida ba zata bar shi ba tunda gidan Ubanta ne ba na Uban buzuwa ba, don haka ka d auketa ku tafi a yi ta mata addu a kurwar Yayarka Dijatu ne a tare da ita Moddi ya wara ido jin abinda ta ce ya furta Wallahi Didi ki bar maganar nan anan Kada Adda Dija ta ji ki Ba zan bari ba Dijan Uwata ce? Ai ba k arya na fa da ba, ba ta inda ta baro kaf halayenta, sawunka a likkafa ka d auketa ka bar min gida idan ta gagareka ka kaiwa Dija ita nima ba zan iya ciwon kai ba.. Amani ta zuba mata ido tana turo baki ta furta Ni nake saki ciwon kai kenan? Kuma wallahi sai na gayawa Umma Dee abinda kika ce mata. Didi ta sake ha de fuska duk da a ranta ta ji d an fargabar a gayawa Dijatun abinda ta ce sai dai bata nuna ba, ta furta Ki gaya mata d in tsoronta nake? Uwata ce Ko Ubana ko kuma ita d in ta maye gurbin Uban Moddibo ne? Shi dai Dahda a k asan ransa yake murumushi a bayyane kuwa harara ya zubawa Amanin yana cije leb ensa. Amanin ta d an turo baki tana kallon Didi ta furta Allah ya kai mu asabar zaki amsa da bakin ki (Asabar itace ranar da duk ahalin Didin suke bayyana a gidanta da yaransu da jikokinsu. Sak Jikin Didin ta yi kafin ta furta Magajiya fitina dai barci take Allah kuma ya tsinewa mai tayar da ita auke kai tana furta Oho ashe ba kya son na gaya mata sai a bayan idonta ki yi ta zaginta Kina ce mata mai bak in hali amma a gaban idonta ba abinda kike iya yi sai abinda ta zartar kamar dai Umma Dee d in Uwarki ce? Dahda ya waro ido kafin ya furta Amani zagin Didin zaki yi? Ah to yau Kai ka fara jin ta zageni, ai ba sabon abu bane wajen Magajiya kai kanka Ubanta ma idan ba ka nan ce maka take Mallakak Wata irin sufa Amani ta yi ta dira a gabanta tana toshe mata baki Allah ki ka gaya masa sai na fa dawa Umma Dee maganar rannan da kika gaya min Tsaf Dada ta shanye zancen. Dada dai lumshe idonsa ya yi kafin ya e yana wurga mata harara don yana da wajen zuwa da yamma ba zai iya da Didi da Magajiyatta ba To Didi bari mu wuce.. Allah ya yi maka albarka, Yauwa Moddi ya maganar mu ta kwanaki ne? Baka samu matar auren ba ne har yanzu? Ko sai na tara maka y an uwanka, wace irin masifa ce ta sameka ace kana zaune da mace ba haihuwa ta hanaka aure balle ka samu magaji, ka san dai y a mata ba naka bane gidan wasu zasu ko? Moddi ya koma ya zauna ya rik e kansa kafin ya d ago yana kallon Didi ya furta please Didi ki bar maganar nan, kin san dai sau uku ina neman aure bai yiwu ba to ba mamaki k addara ta ce a haka? Ba wata k addararka