Sashe 24
Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kika yi da shi tsabar Mallaka amma yanzu ma ki sha kuruminki za mu yi masa aikin da ba zai gaya musu komai ba daga cigaban da ya sameshi gudun kada su hana ruwa gudu Ta saki ajiyar zuciya ta fara kallon Malam tana godiya. Ya ha da mata duk abinda ya dace saura kuma ya ce ta dawo kashegari. Yanzu Malam idan na aikata haka d in, ba zai min maganar abinda ya faru da safe ba? Ko zancen ba zai d aga ba, ki je kuma zaki bani labari. Bata ji ko d ar a ranta ba don ta yarda da Aikin Malamin. Ta zura takalminta jikinta na rawa ta fice direct gida ta koma hankalinta kwance ta fara aiwatar da surkullenta da k ulle k ullenta Tana yi tana sakin murmushi a ranta tana k addara cin zalin yaran da bata son ganinsu ko ka dan yanzu ta fara Har k ofar gidan Hajjan ya je da motar, sai dai yana fitowa ya samu k aton kwa do a k ofar gidan. Rik e kansa ya yi kawai don bai ji da din rashin ganin Hajjan ba. Don haka ya sake komawa motar ya nufi gidansa duk da yaso zuwa gidan Fateema sai ya ji zuciyarsa ta kasa aminta gida kawai yake so ya je ya nunawa Safna. Gidan fes ta saka su Mama Talatu sun share sai k amshin turaren wuta yake. Ita Kuma ta fece wanka da wani Ubansu Riga da wando ta yi kyau sosai don kam k irjinta a cike yake sosai har yana rinjayarta daga k asa ne dai bata da shape ko ka dan. Jikinta gaba d aya ta balbaleshi da turarukan sihirin Malam. Ta d au Layar ta saka a k asan harshenta idonta akwai sihirtaccen kwalli. Tunda ya yi sallama ya ji kansa ya sara da k arfin gaske. Matsalar Moddibo kenan rashin addu a ya kama kan yana zama a saman kujera kafin ya yi aune Safna ta shiga jikinsa ta yi amfani da wannan damar wajen ribartasa ya kusanceta a take a wajen cikin fitar hayyaci saboda turarenn da yake jikinta ya sabbaba masa son kusantarta a k asanta kuwa dama ta shafa rubutun da Malam ya bata. Tuni Moddi ya manta da duk abinda ya faru. So da k aunar Safna sai sake ruruwa suke a ransa. Ya kama hannunta yana janta waje. Zo mu je kiga kyautar da aka ba ni? Cikin farin ciki ta dinga zagaye motar tana jifansa da wani kalar murmushi ta furta Alwan d in ne ya baka? Ya aga mata kai yana murmushi. Cikin son sanin ko aikinta ya kama shi ta furta To kada na ji kada na gani bana son ka gayawa kowa cigaban da zai sameka Imaam Ya d aga mata kai, fuskarsa na bayyana da gaske ya bi umarninta. Ta d an saki murmushi tana lakace masa hanci ta furta duniya sabuwa! Daga ranar an d au tsawon sati biyu Alwan bai neme shi ba. Bai kawo komai a ransa ba don shi sam bai saka son duniya a gabansa kamar yarda Safna ta saka ba. Itace dai shiga d ari fita d ari idan zai yi, she will keep asking Alwan D in Ya kira ka? Idan ya girgiza mata kai. Sai ta yi kamar zata yi kuka ta furta Kai kuma ba sai ka nemeshi ba, ni wallahi Ban tab a ganin Wanda arziki ke bi ba sai kai, ko da yake ba abin mamaki ba ne dama kun yi gadon talauci duk Wanda Ya Saba da arziki ai ba zai guje shi ba Ranar da ta fara fa da masa haka zuba mata ido ya yi ransa a b ace yana fitar da hucin numfashi Amma kuma ya kasa d aukan mataki. A kashegari kamar wasa sai ga kiran Muhammad Alwan nan wajen sha biyun dare Da wani irin sauri Safna ta finciki wayar ta saka ta a handsfree tana masa nuni da Ya amsa murya a hankali suka gaisa da Muhammad Alwan d in. Sai daga can Alwan D in Ya ce Friend, sai ka ji ni shiru kuma? Amma baka nemeni ba, haka ake abota? Da sauri Safna ta ce Eeeh wallahi, yana ta son kiranka to ba ya so ya damekane kana aiki, amma kana ransa wallahi ta furta tana hararar Imaam da ya yi shiru kawai ya kasa furta komai. Alwan daga can ya d an yi murmushi kawai kafin ya furta Haba Aboki, ai an zama d aya you can call me at what ever time you want yanzu forget wannan, abinda yasa na kiraka I want to meet with you at Abuja that s why na maka booking flight na 7:30 am zaka same ni gobe a can. Moddi ya d an waro ido. Safna ta zabga masa harara tana furta Zai zo In sha Allah, ba abinda zai hana shi zuwa. Mun gode k warai. Muhammad Alwan Ya yi cutting kiran, yana mamakin hali irin na matar abokinsa da alama ko wata matsala ce ta taso nan gaba, ba zasu yi wahalar siye matar can ba. Ya saki murmushi kawai. Yana gyara zamansa idonsa akan Boss d insa data zuba masa ido. Hannunta d auke da wani glass cup mai shegen kyau tana kurb ar ruwan tattaccen inib . Kayan jikinta masu masifar kyau. Ita kanta dattijuwar mai kyau ce jikinta duk ta sha adon gold wuya da hannu Har da sark ar k afa. Kanta ba d ankwali hakan ya bawa gashinta irin na larabawa damar zuba Har gadon bayanta. Muryarta very low kamar wacce bata son yin magana ta furta. Aikinka yana kyau Bro ya amince zai zo goben? Alwan ya d aga kai yana furta Sure zai zo Hala. Kuma aikin ba zai mana wahala ba, don wannan matar tasa masoyiyar ku di ce. Matar da Ya kira da Hala ta d an saki murmushi tana lumshe idonta ta sake kai cup D in bakinta, ta yi sipping kamar bata so sai kuma ta furta Make sure ka yi yarda na ce, bana son kuskure you know a komai nawa bana son shirme, ku di ba matsalata ba ce ka jik a su da Naira matuk ar zan samu cikar burina Alwan Ya jinjina kai. Yana furta Ba wani kuskure fa In sha Allah Hala. Good for you. Ta furta tana mik ewa cike da tafiyar rangaji ta shige d aki. Alwan Ya bi bayanta kafin ya mik e shima Ya fice tabbas gaba da gabanta ji yarda yake Boss a waje, amma anan Macece take da mulkin take kuma bashi umarni yarda take so. Ya saki murmushi kawai ya fita don cigaba da shirin tarar Moddi da zai zo a goben. Asubar fari Safna ta tashe shi, da mamaki ya dinga kallonta don baya tunanin ta yi barcin arziki. Matar da da sai ya yi da gske take tashi ta yi sallah k arfe bakwai amma yau itace ta tashi da wuri haka. Ya zuba mata ido da sauri ta ja hannunsa tana furta Ka tashi mana Imaam, ka wani zuba min ido sai lokaci ya k ure? Kai komai sai ka saka shiririta. Ta zabga tsaki tana shigewa Toilet tana jansa kamar wani yaro. A toilet da k yar yake wankan haka kawai sai ya dinga jin gaba d aya ba ya jin da din zuciyarsa ga wani irin fa duwar gaba da bai San ko ta Mecece ba. Haka dai ya yi wankan ya fito. Kafin nan har Safna ta fito masa da kaya sabuwar shaddarsa ta Sallah, abinda da bata tab a yi ba. A hanzarce ta saka shi Ya shirya ranar har cikin bedroom ta kawo masa breakfast. Ya dan kurb i ka dan ya ajiye yana yamutsa fuska ya ce Safna, bafa son tafiyar nan nake ba, gaskiya a hak ura kawai Ai kuwa tafiya kamar ka je ka gama Ta fa da idonta a cikin nasa tana danne Layar bakinta. Ba shiri ya zura hularsa kamar Wanda ake kunnnawa da remote Har ya kai k ofa ya jiyo yana kallonta Ya ce Su Ama fa? Wa zai kai su School yau? A zafafe Safna ta ce Kutma Sai kuma ta shanye zagin ta furta Zan kai su Malam, don Allah ka fita ka tafi kada jirgin Ya cika. Murmushi kawai ya yi yana furta Ta Yaya jirgi zai cika bayan kowa da wajen zamansa, ga ma Boarding pass an turo min. Hannunsa ta fincika suka fita waje. Sai da ta kai shi har Airport sannan ta juyo da motar bata wani koma gida ba ta isa wajen Malaminta ta sanar da shi. A d inke bakin Moddi duk abinda suka ce suna buk ata ya amsa kawai. Malamin kuwa ya d auko allon k arfensa ya shiga rubutu yana k onawa da wuta mai zafi. Ya d ago yana kallonta yana murmushi ya ce An gama! Itama murmushin ta saki ta fice daga wajen zuciyarta fes tana ji a ranta kamar Moddi ya yi arziki ya gama. Babban Hotel aka masa masauki. Ya dinga bin ko ina da kallo a zuciyarsa yana furta arziki yana wajen masu shi. Tabbas su Alwan suna da arziki fiye da tunaninsa.Sai da suka ci abinci sannan Alwan ya ce Ka san me yasa na kiraka? Imaam ya girgiza kai. Alwan ya saki murmushi yana furta Kafin mu yarda da kai sai ka amince zaka shigo cikinmu akan shara din duk abinda muka saka ka za ka yi shi? Imam ya d an bu de ido yana so ya ce Kamar me? sai dai bakinsa ya k i bashi ha din kai kawai sai ya samu kansa da furucin Na amince. Good For you. alwan ya fa da yana murmushi Abu na farko da zamu buk ata daga wajenka shine mahaifar matarka, Ma ana ba zaku haihu da matarka ba. Imaam ya dago yana kallonsa Ya ji kansa ya wani sar masa, amma sam ya kasa masa musu Alwan yana murmushi ya ce Ka kirata ku yi shawara Ya fice ya bar masa wajen. Da sauri Imaam Ya kira Safna. Tana d agawa ta ce Yaya? Imaam Allah yasa dai baka musu taurin kai ba? Ya saki huci ka dan ya