Sashe 48
Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wayar. Tsinkewar gabar da ta samu kanta a ciki ne yasa bata San wayar ma Upside down ta rik e ta ba. Sai da ta ji muryar Alwan yana furta Kin kasa cika mana aikinmu, ga Mijin da kike so kamar ki Mutu yau ya miki Kishiya, yau an aura auren Mijinki d wani irin waro ido ta yi tana jin wani irin zafi tun daga k asan zuciyarta Har gangar jikinta. A razane ta ce What? Alwan Ya saki murmushi yana furta Da gaske ya yi aure, mahaifiyarsa ta masa auren Sirri, idan kina son kuma ya rabu da matar sai kin aikata abinda muke so, ki saka ya kusanci yarinyar can ko ba ya so, ki yi musu vedio kice idan har bai rabu da matar ba zaki tona masa asiri zaki saki vedion kowa ya san waye shi? Murmushi ta saki wata irin nutsuwa tana shigarta. Tabbas wannan ce shawara dama ko ba a yi haka ba tayi niyyar ta saka ta tilas ya kusanci Amani don ta b ata musu rai kamar yarda suka saka tata zuciyar ciwo. Alwan ya katse wayar ya barta da tata wayar a hannu. Da k yar ta zame wayar daga kunnenta. Ta tuna a yau tana da damar da Imaam zai kusanceta sai ta saki jin da di a ranta,don a yau ne zata yi amfani da maganin mak ale mata da Malam ya bata. Ya kuma tabbatar mata in dai Imam d in ya kusanceta ba zai sake marmarin wata mace ba da sunan aure Zan yi amfani da maganin amma sai na gama da wannna matsalar. Ta furta kanta tsaye. Wanka ta shiga tana jin ba wani b acin rai tare da ita duk wani shiri ta gama shirya shi a zuciyarta. Ta gama wankan sannan ta shirya ta shiga kitchen. Favorite dishes d in Didi ta dafa a gidanta su Mama Talatu suna tayata cike da mamakin sauyawarta, ko dai bata son abinda ake ba ne a gidan. Mama Talatu ta fa da k asa k asa tana kallon Inna Laraba bayan Safnan ta shiga store da yake cikin kitchen din. Suka yi shiru ganin ta fito still fuskarta cike da walwala tana kallonsu ta umarcesu su kwashi abincin su biyota parlorn Didi da su. Haka kuwa aka yi Didi sai gani ta yi suna jera abincin a babban Dinning area d inta da Yasha adon carpet mai taushin gaske da pillows manya. Don Moddi bai saka mata Dinnig table ba ya san bata so sai ya saka mata wani table irin na k asan nan sosai Mara tsaho. Cikin mamaki Didi take bin Safna data zauna a gabanta da kallo. Murmushi Safnan ta yi sai kuma ta sunkuyar da kanta idonta yana tara k wallar da ta k iro ta k arya. Murya a k asa sosai ta shiga bawa Didin hak uri Don Allah Didi ki yafe min, In sha Allah ba zan sake aikata abinda duk na aikata a baya ba, na yi nadama kuma ina neman afuwarki data yaranki Har ma da Moddi da y ansa gaba d aya. Didi cike da mamaki take dubanta ita ba yarinya bace ta San wannan tuban na Safna bana gaskiya ba ne, da wani abu a k asan ranta ba mamaki yaudara ce ko kuma ta ji labarin auren Moddi take son ruguza shi ta hanyar makirci. Sai kawai ta saki murmushi itama in dai Makirci ne gidan ta tarar yaushe aka haifi Safnan su da aka haifa zamanin da makirai ma suka fi yawa, ba yanzu ba da mutane basu da wayon iya makircin ba ma. Hannu ta saka ta dafa kanta tana sakin murmushi ta furta Ai haka ake so Safna, tashin hankalin ai bashi da rana, Allah ya yafe mana gaba d aya. Wannan abincin dai yau ba zai ciwu ba don duk muna azimin Alhamis. Safna taji zuciyarta ta wani irin bugawa duk ku din da ta kashe cikin abincin na asirin data zuba a cikinsa Sun tashi a banza kenan? Kai ina wallahi da sake. Sai ta saki murmushi tana furta Ai ba zai yi komai ba zuwa yamma sai a yi muku warming insa ku sha ruwa da shi, amma shi Moddin ai baya azimi. Shima yau ya dauka. Didi ta furta tana k arin danne dariyar da take ranta. Ta k yale Safna a zuwan za a ci abincin da daddare. Daga wajen Didi ta nufi sashen Moddibo, zuciyarta duk ba da di wani irin zafin Moddibo take ji. Wato ita zai yaudara ai kuwa zai sha mamaki. A zaune yake laptop a gabansa. Kallo guda ya mata Ya auke kai. Ita kuwa sai da numfashinta yaso d aukewa tsabar kyau da taga Moddi ya yi cikin black shirt da farin wando. Gashin kansa ya sha gyara sosai. Ta k arasa kusa da shi tana nazartar yanayin parlorn da yake a gyare tsaf-tsaf As usual Moddi baya son k azanta ta sani don haka komai nasa yake zama very neat. So take ya kalleta sai dai tun kallo gudan da Ya mata bai sake ba yana ta aikin tapping computer. Sai da ta gyara muryarta wajen son k wato tunaninsa da sanyin muryarta ta da take tunanin ta siranta sannan ta furta Wajenka na zo Imaan, I need your concentration Bai kalleta ba ya furta All ears Ranta ta ji ya sosu ganin abinda yake mata, Wanda da bai isa ba, bai isa ta yi magana ya shareta ba. Amma sai ta cije ta daure b acin ranta ta furta ka yi hak uri na amsa duk laifi na ina rok on yafiyarka please! ago kansa ya yi yana kallonta sai kawai ya dan saki murmushin gefen lips ya ja bakinsa ya yi shiru. Cak ta mik e ta isa gefensa ta shiga jikinsa a hankali ta furta Da gaske nake, na yi regretting all my wrongs kuma ba zan sake ba In sha Allah cikin idanunta yake kallo yana mamakin jin kalaminta, anya kuwa ta San irin laifin da yake shirin yi mata. Sai kawai ya kama hannunta ya sumbata ba tare da ya furta komai ba ya mik e ha de da d age laptops d insa daga wajen. Ga abinci a parlorn Didi na kawo muku Azimi ya furta cikin husky voice d insa sannan ya shige d akinsa. Bakinta ta cije sai kuma ta saki murmushi Zaka dawo daidai ne Imaam, zan baka mamaki. Komawa ta yi parlorn Didi ta zauna ta sake a cikin su har tana jan Imaan a hirar don kam bata ga fuska wajen Amani ba. Imaan din ta dinga amsa mata a darare don tsoron Safnan take ji kamar yarda take tsoron ranta. Ban da Allah ya kiyaye tana dagewa da addu a da tuni ta sakata a mummunar hanya bata San me yasa a yanzu ma Safnan ta janye makaman yak inta ba. arfe shidd ta k iri ciwon cikin k arya bayan da ta tabbatar ta aikata abinda take so successfully Ba wanda ya kawo komai Didi ta ce su tafi asibiti da Imaan. Suna zuwa asibiti Doctor ya tabbatar musu sai an yi admitting Safnan. Iman taso guduwa gida Amma Safnan ta rik e hannunta tana furta Why? Idan kika tafi wa zai zauna da ni, ki bari drip din ya k are mu tafi tare. Haka Imaan ta hak ura ta zauna ba don ranta yaso ba. Suna zaune a parlorn Didin Amani ne da Didin kawai. MODDI ya shigo sai daukan ido yake fuskarsa cike da walwala ya zauna a kujerar da take gefen Didi. Yana kallon Amani da take zaune tana kallonsa cike da fa duwar gaba. Wani irin take ji a duk sanda suka kusanci juna. Didi da farin ciki ta furta Alhamdulilah Ya ka baro amaryar? Ya cire hularsa yana jingina da kujera idonsa a lumshe murmushin fuskarsa ya kasa d aukewa Ya furta Tana gaishe ki, da kowa ma. Amani taji zuciyarta kamar ta tarwatse don haka ta mik e kawai zata wuce Moddin ya ce ta juyo jin ya ambaci sunanta ledar hannunsa ya mik a mata sai kuma ya mik awa Didi tata. Daga haka ya mik e ta gefen Amanin yazo zai shige ya furta Koma ki zauna, Dodon naki ya tafi. Duka jikinta ta ji wani irin yarrr jin yanayin sound din muryarsa. Ta rik e ledar a hannunta kafin ta zauna cikin mutuwar jiki. Didi tana kallonta ta furta Alhamdulillah yau buri na ya cika Moddi Ya auri kamilar mace wallahi. Baki ganta ba. Amani ta an cije leb e kawai. Didi ta saki tsaki Wai Uban me aka miki ne yau nake ganinki sukuku, ina lura koda aka sha ruwa ba wani abin kirki kika sha ba, wuce ki je kitchen akwai fura a fridge dana dama Miki don na San ke gwanarta ce ki auko ki sha a gaba na. Amani ba don tana so ba, sai don tana son Didin ta daina mata hayaniya a kai ta samu kuma ta barta ta huta yasa ta shiga kitchen din ta auko furar ta kawowa Didin. Didi ta zuba a cup ta mik a mata tana janyo ledar da Dadan Ya bawa Amanin taga nama ne mai zafi sai Icecream a ciki da fresh milk. Ta furta To maza ki zauna ki sha komai, haba yarinya duk kin bi kin fige Dole Amani ta dinga turawa a cikinta, komai ciki take yi cikin rashin kwanciyar hankali. Didin ma ta ja nata tana ci kaza ce da yoghurt. Amani dai bata San ta kusa shanyewa fresh milk D in ba ko don da gaske tana jin yunwa ne. Ta ajiye tana kallon Didi ta mik Zan je na yi freshen up na kwanta. Didi ta fara kallonta da dishi-dishin idonta da take jin wani irin masifaffen barci ta daga mata kai. Tun kafin Amani ta kai aki Didi ta mik e ta shige nata d akin tsabar barcin da yake idonta. Amanin wanka ta yi ta kwanta rigingine tana jin yanayin da take ciki yana sake k arfi. Ta runtse idonta da k arfin gaske tana hango Dada tana kuma jin muryarsa a kunnenta kamar yarda ya saba zuwa mata a barci. Abu fa Ya fara