← Book details Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 57

Sashe 23

Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BRIGHT PENS... 2nd batch Zazzafar tafiya mai abin ban mamaki, tawayen jerin marubuta hu u a sabuwar tafiyar ta second batch. *HADARIN GABAS* Nazeefah Sabo Nashe ARFE A WUTA* Ayushercool *ZAYTOON* Zee kumurya *MUTALLAB* Nimcyluv Sarauta. Yawaitar kiran da Muhammad Alwan Yake masa ne, ya saka shi bai k arasa gidan Hajja ba sai kawai ya tafi direct wajen Muhd d in, bayan ya yi waya office ya bada uzirin gaibu. Don bai ji a ransa zai iya barin aikin sa ba. Madadin ya fito Muhd d in cewa ya yi ya shiga d aki ya same shi. Bai masa musu ba ya shiga in da ya ce masa. Tsaf d akin sai zabga azababben k amshi yake. Muhd ya nuna masa wajen zama Please sit mana Imaam, me yasa kake yin kamar bak Murmushi Imam ya saki karo na farko tun bayan ha duwarsu ya zauna a kujerar. Alwan ya cigaba da shiryawa cikin ha daddiyar suit d insa ya yi combing kansa mai kama da gashin larabawa. Sai da ya gama ya kalli Juice d in da ya ajiye masa da snacks ya mayar da kallonsa kan Imaam d in da alamar tambaya ya furta Me yasa baka ci komai ba? Ko baka yarda da ni ba ne? Girgiza kai Imaam ya yi kafin ya tsiyayi lemon mai sanyin gaske ya kai bakinsa. Idanunsa akan Alwan da yake sakin murmushi. Nagode da ka sha, da baka sha ba akwai matsala Ya furta yana saka glass d insa da ya kasance bak i wuluk. Matsala kuma? Alwan ba wani damuwa a fuskarsa ya d aga kai yana furta Babba ma kuwa ya d an ja fasali sai kuma Ya furta Ka san mu larabawa bama son mu yiwa mutum kyauta ya k i amsa, sai mu ji ba da di a zuciyarmu. Ya sake fa da yana d an sakin murmushi. dafa shi ya yi ya furta Rashin shan da zaka yi zai saka na ji a zuciyata baka amince da ni ba. Sai sannan Imam ya saki ajiyar zuciya, amma sai ya samu kansa da jin wani irin nauyi a kansa take ya d an lumshe ido yana sakin ajiyar zuciya bai kawo komai a ransa ba sai tunanin ko don yana cikin b acin ran Safna ne. Ka tashi mu je. Ya furta yana dafa kafa darsa Imaam ya mik e a hankali ya bi bayansa. Motarsa ya ce su shiga ya ajiye machine d in nasa. Hakan kuwa aka yi. Direct cikin abinda bai fi mintuna ba Imaam ya gan su a cikin Government House. Da mamaki yake kallon Alwan d in. D aga masa kai kawai ya yi ya furta Mu je, zan ga Governor na kai masa sak Jikin Imaam a sanyaye ya fito ya bi bayansa yana mamakin wai yau shine zai ga Governor lallai ha duwarsa da Alwan alheri ne. A babban parlorn gwamnati aka saukesu inda gwamna yake gaisawa da manyan bak insa. Mamaki bai gama cika zuciyar Imaam ba, sai da Gwamna ya shigo madadin yaga Alwan ya mik e ya kai gaisuwa sai yaga ma Gwamnan ne yake daraja Alwan d in. Barka da sauka Doctor Alwan Murmushi Alwan ya sakar masa yana firta Nice to meet you excellency Gwamna ya d aga kai yana sake sakin murmushi sai kuma ya kai dubansa kan Imaam yana masa kallon rashin sani ko kafin ya yi magana Alwan ya yi gyaran murya ya furta A best friend of mine Gwamna ya saki murmushi yana mik awa Imaam hannu. Imaam ya d an ji wani banbarakwai sai kuma ya dake ya mik a masa nasa hannun shima. Zai Mik e ya fita ganin kamar tattaunawar tasu ta sirri ce Alwan ya saka baki ya kira shi. Just sit, ba sai ka fita ba. Ya koma ya zauna. Yana kallon wani kallo da Gwamna ya masa sai kuma ya d auke kai ya cigaba da kallon Alwan da yake mik o masa papers. Zaka yi signing anan kamar yarda na fa da maka, mun kuma amince da buk atarka ta ka sanya hannun jari a companyn da zamu bu de anan, mun yarda zamu bu de babban companyn don cigaban arewa Murmushi da ya bayyana tsananin murnarsa gwamna ya saki yana furta Alhamdulillah Nagode sosai ka mik a min godiyata wajen Boss murmushi Alwan ya saki yana furta No problem Excellency.. ya mik e yana mik a masa hannu suka gaisa da tafawa sannan ya fice a hanzarce bayan ya kalli Imaam da duk yabi ya zama kamr wani gunki a wajen. Murmushi ya saki ka dan. Ya dafa shi yana furta Shall we? Imaam ya d Aga kai ya mik e shima ya bi bayansa da d an hanzari. A mota kasa shiru Imaam ya yi sai da ya kalli Alwan ya furta Dama ka tab a zuwa Nigeria? Murmushi kawai Alwan ya sakar masa kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya saki ajiyar zuciya ya furta Rabin rayuwa ta na yi ne a Nigeria Abuja, shi yasa zaka ji na iya Hausa sosai, amma all my family suna Turkey, ni na zauna anan ne saboda issue na business Imaam ya girgiza kai. Ka san Turkish companies da suke cikin k asar nan? Imaam ya yi saurin d aga kai Shi kuwa ya san Turkish group of companies duk wanda yake K asar nan Ai ba zai ce bai san wa dannan companies d in da k asar nan take alfahari da su ba. Kamfaninnika ne da suke sarrafa kayan masarufi iri iri na abubuwan amfani da furniture s masu kyau da tsadar gaske, a kwanan nan suke shirin bu de companyn ha da motoci. Na familyn mu ne Ya ji muryar Alwan a sama Ni nake monitoring na Nigeria. Da sauri Imaam ya juya yana kallonsa idan kuwa har ta tabbata da gaske ne tabbas Alwan ba shi da girman kai kuma ya tsinci dami a kala. Kana son ka yi business da mu? Imaam ya d aga kai da sauri don ba zai bar kansa ya k ulle ba. Murmushi Alwan ya saki a zuciyarsa ya furta Nice, hakan ya yi a fili kuwa cewa ya yi Akwai shara idan ka amince sai nace maka ka godewa Allah ka kusa shiga sahun billionaires na Arewa Imaam ya ha diye yawu yana d aga kai Sharad in me? Sai da Alwan ya juyo kamar ba driving yake ba sai kuma ya juya yana cigaba da tuk in ya furta I will tell you, but not now. A wurin siyar da motoci ya yi parking yana kallon Imaam ya furta Mu je ka min rakiya, Allah yasa ka iya mota ka ja min ita. Imaam ya d aga kai yana furta Na iya.. ya jijjiga kai yana murmushi suka isa wajen wata Honda accord mai masifar kyau bak a wuluk. Ya yi ciniki ya biya ku din ya mik awa Imaam key d in. Imaam yana kallonsa ya furta na menene? Na taimako na da ka yi, kuma kada ka ce min ba zaka amsa ba ka san hukuncin hakan islamically.. Imaam ya saki ajiyar zuciya ya kuma kasa yi masa musu yana kallo ya fita ya bar shi a wajen yana furta Zan kiraka anjima zan je Abuja but zan dawo morning. Ya lakace hancin Imaam ya fita daga wajen yana murmushi ko bakomai burinsa ya cika. Imaam kasa motsa wa ya yi daga wajen ya dinga kallon Motar da aka ce tasa ce ya lumshe ido yana mamakin Alwan da dukkan alherensa daga ha duwa jiya kawai? Ko da yake a arziki irin na danginsu ya san wannan bakomai ba ne. Don haka sai ya ji ya samu nutsuwar zuciya ya shiga motar cikin matuk ar farin ciki ya ja zuwa gidan Hajja don ita ya kamata ya fara sanarwa Safna kuwa tun bayan fitar ta gida hankalinta tashe bata tsaya ko ina ba sai a gaban Malaminta. Yanayinta da ya gani ya tabbatar masa ba lafiya ba. Ya san Safna ba tun yau ba ta amince da cewa shi ke samar Mata da duk wani farin ciki. Sun gaisa hankalinta a tashe ta sanar da shi dalilin zuwanta. Idanu ya zuba mata bayan duk ya gama jin abinda ta ce ya furta Akwai matsala Safna, dole ki tashi tsaye akan Mijinki don idan baki wasa ba kina ji kina gani zai fi k arfinki Tashin hankali ya bayyana k arara akan fuskarta idan da abinda ta tsana a sanar mata da Imaam zai rabu da ita. Ta yarda da aikin Malamin nan tun farkon ha duwarsu da Imaam shi ya mallake mata zuciyarsa da tunaninsa. Akwai alheri ma da yake matso shi nan kusa, sai dai idan ba ki yi da gaske ba zai ture Alherin akan wani dalili Ta waro ido Malam hakane wallahi, don jiya ya ha du da wani mutum mai ku di sai dai da dukkan alamu baya son tarayyarsu da mutumin Malam ina son ka kulle bakinsa ya zama duk abinda mutumin ya umarceshi kawai ya aikata ba musu, ni in dai Imaam zai yi ku di kawai koma ta wani hali ne ya yi, ko na huta da gorin dangina na auri wanda ba shi da ku Malam ya saki murmushi An gama Safna, arziki kam Mijinki zai yi shi, amma a k arshe fa naga wani duhu In dai a k arshe ne Malam duk daga baya ne, kawai a min aikin da zai yi abinda suke so ko baya so. Sannan ka rufe min bakinsa tsaf kada ya dinga gayawa kowa sirrinsa sai ni ka dai don kada ya je ya gayawa Hajja ta hana shi ta cucemu. Ta fa da ba tare da ta bari bokan ya gaya mata duhun me ya gani ba.Malam ya jijjiga kai ya cigaba da dube duben k asarsa ya d ago yana kallonta ya furta Zaki iya birne bunsuru da rai? Ba abinda ba zan iya ba Malam kai kanka shaida ne don na yi wanda ya fi wannan in dai akan Moddibo ne Tabbas kin yi Safna ni kaina ina jinjinawa jarumtarki da rashin tsoro, don ma dai mijin naki tsohuwar sa a tsaye take a kansa da wallahi sai yarda
Chapter 23 · 0% Book details