Sashe 37
Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tsakaninsu kullum yana manne da jikin Fateemah da sunanta ya fara bu de baki zaka ga yana d aga hannu yana kiran T T T. Hakan har yasa kowa ya koma cewa Fateemahn T. Dijatu ma bai iya ba sai dai D D sai kawai duk sunan y an uwansa Ya koma farkon sunan sa. Kulawar Didi gaba d aya ta koma kan Moddibo wannan Ya d arsa jin haushinsa a zuciyar Dijatu idan har yaje kusa da ita sai ta yakice shi musamman ganin yarda ya tashi a sangar ce, ga rashin tsoro da taurin kai. Idan za su yi masa fa da Didi ta hana. Abu guda da yasa yake sake shiga ran y an uwansa tun bayan tasowarsa sai ya tashi da tsananin y an Uwarsa da Didi. Burinsa duk abinda ya je ya samo ya k arar da su akan y an uwansa. Idan Didi ta ga haka sai ta yi murmushi ta ce Allah yasa ka d ore Har girman ka Moddi, Allah yasa ba zaka auri matar da zata kawar da hankalinka daga wajenmu, Ubangiji yasa ka auri matar da zata taya ka so na da y an uwanka baki d aya. Tun bai San dalilin Didi na fa dar haka ba sai ya turo baki ya ce Ai Didi ba a yi macen da zata raba ni da ku ba, balle ma ni ba zan yi aure ba ina tare da ke, idan ma na yi ta ce zata raba mu wallahi sakinta zan yi, bayan ina kallon irin wahalar da muke sha tare. Didi Shafa kansa take a lokacin ta ce Allah yasa Moddi, na San Addu ar Uban Moddi ba zata tafi a banza ba Haka Ya taso namijin gaske da burinsa ya mayar da taro sisi. Burinsa ya fita ya samu ko ka dan ne ya kawowa Didi don yana jin haushin wahalar da jikinta da take wajen yin abincin siyarwa Kunu da k osai da safe. Da rana kuma shinkafa da wake. Da daddare ma ba zata huta ba zasu ora kaskon wainar filawa duk da wannan su Fatima ne suke yi a tsakargida Amma Allah ya sakawa neman su albarka duk sana ar da suka saka hannu a kai sai ka ga ta yi albarka. Shi kuwa Moddi duk ba ya son yaga suna wannan abin, burinsa ya yi ku di ya tallafi rayuwarsu don haka ya dage da Sana a da karatun boko da na addini gaba d aya. Sanda Fateemah da Dijatu suka samu Miji duka dangin Ubansu sai suka guje su suka juyawa Didi baya Wanda a bayyana take ba don komai suka aikata haka ba, sai don basa son ta jingina musu wahalar yaranta. Don k iri da muzu suka kalleta suka furta Ai sai ki aurar da y an naki, sanda Ubansu ya Mutu ba nuna mana kika yi ba zamu rik e su ba, sai yanzu da aure ya zo zaki neme mu ashe muna da rana? Didi ta ha diye wani yawu mai zafi tana tuna Uban Moddibo da dukkan alherinsa ga y an uwansa, burinsa kyautata musu koda last kobo da ya rage a aljihunsa ne idan Har zata yi magana sai ya ce Maryama kenan? Idan baka taimaki y an uwanka ba wa zaka taimaka? Sam bani da burin samun ku din da wani na waje ma ba zai ci ba, balle jini na. Didi sai ta ce Mhmhn, Malam kenan, Allah yasa bayan ba kai su rama maka abinda ka musu ba zasu rama ba, har abada kuma bana neman ramuwarsu don Allah na yi kuma gareshi nake neman sakamako. Sai ta ja bakinta ta yi shiru. Haka suka dinga fafutuka Har Allah ya fitar da su kunya don dai Fateemah Mijin marainiya ta aura take ya ce baya buk atar a kaita da komai sai zallar Fateemansa ita yake so da halayenta ba kayan d aki ba da zasu zo su Mutu ko mu da de ko mu jima. Ingancin tarbiyyyarta da nagartar halayenta ya fiye masa tilin kayan d aki. Didi taso ta turje amma sai iyayen Ahmad suka nuna dattako suka ce basa buk ata kuma har abada ba gori tsakaninsu da Fateema sun yaba da halayenta da tsatson da ta fito. Don haka duk wani shiri na Didi sai ya koma kan Dijatu aka siya mata kayan d aki da duk wani abu da zata buk ata. Haka aka yi biki aka k are cikin kwanciyar hankali. Zo kaga abin tausayi ranar rabuwar Fateemah da Kiddonta. Wunin ranar zama ya yi kamar marar lafiya, haka zai shige d aki ya saka kuka don baya son a ga kukansa Didi na hankalce da shi murmushi kawai take saki don itama ji take kamar ta fashe da kukan, tabbas ka ga auran y anka babbar ni ima ce, amma fa rabuwa da su akwai ra di mai zafin gaske. Musamman yarda ta taso da y anta kamar k awayenta, haka dai ta daure tana ji tana gani aka rabata da su zuwa gidan aure. Kiddo dai bai raka Dijatu ba, don ita murna yake da tafiyar ta Adda T kawai zan raka ya furta kansa tsaye yana kallon Dijatun. Ta kuwa zabga masa harara har da rank washi ta furta Sai me idan baka raka ni ba? Kuma koda wasa kada naga k afarka a gidana ka zo kwa dayin kaza. Ya janye jikinsa kafin ya furta Ke ma ki samu kazar tukun, wannan k ulumin ne zai siya Miki kaza? Ta bi shi da duka sai dai kafin ta cim masa ya fece da gudu, kamar lokutan baya da suka Saba. K wafa Dijatu ta yi kafin ta sake rushewa da kuka tana furta Ai Didi tana Jin abinda ya ce mata Amma ta k i yi masa magana saboda ita ba a sonta shine d an so Haka rayuwa ta cigaba da gangara musu, da da di ba da di suna cikin godiyar Ubangiji don shi ke bayarwa ya kuma hana a sanda ya so ya kuma ga dama. Moddibo na girma kyansa da wani irin kwarjini yana sake bayyana tattare da shi. Shekara 19 idan ka gan shi sai ka zata wani babban saurayi ne, saboda son gayu da Allah ya bashi. Bai k i ba ko last kobo ne a jikinsa ya saka ya siyi riga da turare duk don ya je makaranta ya yi burga ya shiga cikin gayu kuma yafi kowa. Sau tari idan ka ganshi zata zaka yi wani shegen d an mai ku din ne, duk da bai d au girman Kai ya dorawa Kansa ba Amma yanayin suturunsa da fatar jikinsa da ta bayyana tsananin Hutu duk da naturally haka take, wannan zai saka ka yi zaton Uban Moddibo attajiri ne, haka Didi take furtawa a duk sanda taso ta tsokane shi. Murmushi yake saki ya ce Didi ki yi shiru fa, nan gaba baki san me Moddi zai zama ba, idan bai zama D an Attajiri ba zai iya zama attajirin da kansa Didi ta kan ce Allah ya bada masu albarka, amma a rage dogon buri, rayuwar ma nawa take gaba d ayanta Moddi? Duk arzikin da zaka yi wani ya yi fiye da shi tun kan a san asalinka, don haka ka yi fatan masu albarka kuma na Halak. Idan kuwa Dijatu na kusa harara take zuba masa ta ce Da charging wayar za ka yi arziki? Ko da siyar da raken? Idan Moddi ya juyo da birkitattun idanunsa Didi ce kawai take rusunar da su ta hana ya Kai mata duka, sai ko idan Fateemah tana nan. Sanda Moddi ya shiga Jami a yana shekaru Ashirin cif, a sannan za su ce k addararsa ta fara daga ranar da suka ha du da Safna daga ranar basu sake gane kan Moddi ba, har bayan auren da aka masa da y ar riga da mutuwarta Didi ta saki ajiyar zuciya Jin hannuwan Moddibo a kafa darta ta d ago tana kallon idanunsa da yake binta da natkakken kallo, mai nuni da yana son sanin menene a ranta me take tunani? Duk da bai furta ba, hakanan ta sanar masa murmushi tana Shafa gefen fuskarsa ta furta Ina tunanin Moddi ne, ina tuna Uban Moddi da duk wata rayuwar mu ta baya mai cike da k alubale, ina tuna wancan Moddin masoyin Didinsa, wancan Moddin Wanda ya zama majinginar y an uwansa, ba wannan ba da gaba d aya ka canja a idanunka nake hango rashin gaskiya Moddi, tun bayan ha duwar ka da Safna ban sake farin ciki ba Moddi, na yarda ha duwarka da Safna shine silar rugujewar farin cikin zuri ar Lami do Uban Moddibo Moddibo ya runtse idonsa yana Jin wani irin zafi a zuciyarsa, haka nan idanunsa wani irin ra di suke, da alama so yake kawai ya zubar da hawaye. Hannu ya cusa aljihu yana cizon gefen leb ensa, shi da kansa ya San Safna itace silar rushewar farin cikin ahalin Lami do. Zufa ce kawai take zubo masa ya runtse ido yana tuna ranar da k addara ta caku de zuciyarsa da ta Safna wace guda, daga ranar ya canja daga Moddibonsa ya koma wani mutum daban Da sauri ya dinga shiri saboda murna da zakwa din shigar sa Jami a. Jami ar da da yasan Safna zata zamo k addararsa a ciki da koda wasa bai je ta ba. Wanka ya fesa sosai ya kuma k ure Adaka cikin wani rantsatstsen jeans black da Jar shirt da ta yiwa fatar jikinsa masifar kyau. Ya kawo P.Cap black ya saka a kwantacciyar sumar sa ta asalin fulani. Sannan ya saka Black shade a idonsa. Idan ka gan shi wallahi ba zaka zata haihuwar Nigeria ba ne cikin garin Kano a unguwar Yola, saboda tsananin kyan da ya yi. Kamar yarda ya Saba a duk sanda zai fita daga gida sai ya isa wajen Didi ya zube a gabanta ita kuma sai ta sunkuya saman Kansa ta karanto masa addu oin tsari. Wannan karan saboda azarb i yana shiga Jameelah ta ce masa Didi tana wanka. Ba zai iya jira ba don haka ya ce idan ta fito ki ce mata na wuce saboda abokaina suna jira na. Jameela