Sashe 46
Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wulak ancinta zalla a gabanta ta tsaya tana sakin wani murmushi ta nuna kanta tana furta Na Amani Imaam Moddibo ne Safna ta k ance idonta cikin na Amani, tsanar yarinyar na sake girmama cikin zuciyatta ta dinga jin tamkar ta shak ota ta mutu, amma idanun yarinyar a yau Sun razanata Sun kuma firgita ta. A idanun Amanin ta dinga hango rashin kunya zalla da wani irin kwarjini da ba shakka idan ta cigaba da tata masifar Amanin zata iya tona mata asiri. Zata iya fallasa sirrinta ta sanar da zuri ar Lami do wacece ita? Sai kawai ta cije baki, k walla tana shirin zubo mata. Ba k wallar komai ba ce sai ta rashin sanin madafa, da rashin sanin abinda zata aikata cikin k unar zuciya ta furta Kin cuce ni Amani, kuma wallahi ba zan barki ba sai kin biya abinda kika aikata min, sai na saka ki bak i ciki fiye da Wanda kika sa min a cikin kwanakin nan zan mayar da rayuwarki miserable daga haka ta juya ta fice cikin mutuwar jiki. Imani ta dinga kallon Amani a firgice ganin wata irin da Amanin take hankalinta kwance kafin ta furta Before ta yi making life d ina miserable ni na mayar da tata, matsafaciya kawai Juyota Iman ta yi a fusace tana furta Ba zaki daina shiga sabgar matar nan ba ko? Ba zaki fita hanyarta ba ko? Sai ta cutar da rayuwarki? Amani ta dafa hannunta tana murmushi ta furta Wait and See, ba abinda zai faru sai alheri, In sha Allah sai naga bayan matar nan .na tsaneta Imani, kuma ko yanzu na San burina daf yake da cika. Daga haka ta saka kai ta fice daga d akin. Tana jin zuciyatta fresh kamar ba wata tarin matsala a tare da ita. Babban Parlorn Didin taf yake da mutane. Wa danda suka zo taya ta murna. Yau bakin Didi Sam ya k i rufuwa don a yau ne zata saka a kai ku din auren Moddi. Auren da take ji idan ya yi shi dukkan matsalolinsa da nasu za su kau. Tana kallon k aninta Kawu Jauro ta furta Duka a kai har ku din har lefen idan ta kama a basu Har sadakin bana son auren nan ya wuce sati biyu Jauro, ka gaya musu bama buk atar komai sai matar kawai. Jauro ya aga kai cike da gamsuwa. Amani kuwa gabanta ne kawai yake fa duwa haka kawai jin wai auren Dada za a je nema. A da kam ta fi kowa son Dada ya yi auren Amma yau sai taji wani abu ya dunk ule mata a k irji jin abinda Didi take cewa. Hakan yasa ta sulale daga cikin mutane ta shige d akinsu na sashen Didin tana shiga ta danno k ofa. Zuciyarta na bugawa ta lumshe ido tana jan Innalillahi a ranta don idan har ba mafarki take ba, ji take kamar kishin Dadan take, kishi mai zafin gaske mai dagargaza zuciya da saka zafi a cikin zuciyar . Ta runtse idonta tana furta Ya Allah! Me yasa ne? Ta fa da tana kwanciya saman gadon. Iman kuwa farin ciki ne ya sakata neman idanuwan Amanin don su yi farin cikin tare ko ta hanyar kallon juna ne, sai dai bata ga Amanin ba. Don haka ta mik e zuwa cikin gida don neman Amanin a daidai Sitroom da Dahda yake zama da bak i. Ta fara juyo sautin muryarsa kamar waya yake, kamar kuma magana yake da wani a kusa da shi Wannan karan fa na shirya da gaske nake zan aikata abinda kuke so, zan cika muku burinku zan kusanceta Nimfashin Iman ne ya kusa d aukewa tsabar tashin hankali bata San sanda ta yi baya ba, don idan Har zuciyarta ta fassara abin daidai Furucin Dada yana nufin zai kusanci Amani don cikar wani burinsa, Wanda ta tabbatar bakomai ba ne, sai SON DUNIYA (wannan littafin book one ne free, book 2 and 3 paid ne. A biya 500 cikin wannan asusun 2118666253 UBA. Don cigaba da jin labarin Moddin Didi, da Amanin da Dahda. Wa ke da nasara tsakanin Amani da Safna. Book 1 daf yake da k arewa.) JIKAR NASHE HADARIN GABAS NAZEEFAH SABO NASHE 08033748387. BRIGHT PENS SECOND BATCH A gigice ta ja da baya da sauri, don bata son Dahdan ya ganta. Sai dai aikin gama ya riga Ya gama, don tuni idanunsu suka ha de da juna. Ta Ware ido tana toshe bakinta da k arin ha diye kukan da yake son taho mata. Sai dai ina bata da juriyar rik e wannan kukan tuni hawayen ya kufce ya dinga zuba daga idanunta Mik ewa Dahdan ya yi don isa wajenta da son ya yi mata bayani, sai dai ko kafin ya kai k ofa ta fice da sauri, bata son ganinsa ba kuma ta son jin ko wane kalami daga bakinsa. Ta ji komai ta kuma amince Dadan matsafi ne, da gaske tsafi yake yi shi yasa duka abubuwan suke faruwa. Ashe hauka take da take d orawa Mommy Alhajin komai. Dahdan ne mai laifi shi ya yi silar afkawar Amani cikin wannan halin. Ta mayar da k ofar ta rufe Har da murza key sannan ta jingina da k ofar wani irin kuka da bata tab a irinsa ba a rayuwarta ta shiga yi. Da dukkan k arfinta take buga k ofar da kanta tana furzar da wani irin huci mai zafi. Daga k asan ranta take jin wani irin zafi zuciyarta kuwa kamar ana tafasa ta da ruwan zafi. Gangar jikinta idan banda tsiyayar da gumi ba abinda take yi. Duk da tarin sanyin A.cn da yake d akin jin ta take kamar tana cikin Oven, tsabar zafin da take ji na tashin hankalin da take ciki. Ta zube a gado idanunta akan hoton mahaifiyarsu, kallon hoton ta yi kafin ta fisgo shi da k arfinta ta shiga magana da shi kamar wacce take cikin hoton tana jinta. Me yasa? Me yasa Mahmeey kika Mutu kika bar mu? Me yasa baki tafi da mu ba, kika barmu a wannan duniyar mai cike da maciya Amana da burin duniya? Mun fuskanci k alubale da dama kafin mu tashi mu kai yanzu, sai gashi a yanzu muna fuskantar k alubalen da yafi Wanda muke ciki, mahaifinmu Mahmeey, Dahdah yana shirin kusantar Amani y ar cikinsa don Son Duniya Sai ta sak fashewa da kuka da k arfin gaske, ta rungume hoton y ar riga a jikinta. Ta da de zube a wajen cikin fitar hayyaci kamar wacce ta zare, burinta mutuwa a loakcin burinta ha duwa da mahmeey a can inda ba zata sake ganin Dahda ba, ba zata sake ha duwa da duk wani k alubale mai shirin tarwatsa mata zuciya ba. Tana so ta Mutu sosai kamar yarda Amani take burin mutuwar itama. Bugun k ofar da ake yi ne yasa ta dawo cikin hayyacinta, sai kuma tabi k ofar da kallo tana tunanin waye sai ta ji muryar Amani tana kiran sunanta. A kasalance ta mik e ta bu de mata k ofar. Idanu suka zubawa juna gaba d ayansu kowa yana jin wani irin ciwo a ransa, ganin halin da d an uwansa yake ciki. Iman ta finciko Amanin ta mayar da k ofar ta rufe ta rungume ta da k arfin gaske, a tare suka saki kuka sautin bugun zuciyarsu yana k aruwa. Jikin Amanin zafi zau da alama mugun zazzab i ne ya kamata. Iman ta ja hannunta zuwa bakin gadon ta zaunar da ita kafin ta mik e cikin First aid box da yake gefen gadonsu ta bu de ta Ciro pain reliever ta d auko table water ta dawo inda Amanin take. A baki ta zuba mata maganin Amanin tana b ata fuska ta sha maganin. Kafin ta zube a saman gado. Iman D in ma kwanciya ta yi daf da ita tana sakin ajiyar zuciya ta furta Matsalar mu daga yau In sha Allah ta kau Ama. Amanin ta ago tana kallonta da neman k arin bayani. Iman ta d aga mata kai Dole zamu bar gidan nan a daren yau Amanin ta zaro ido kafin ta lumshe su sai kuma ta ciji leb enta bata ce komai ba. Zamu wuce wajen dangin Mahmeey, Har sai komai ya lafa, ina tsoron afkuwar wani abu da naji shi da kunne na yau, da wani ne ya gaya min ba zan tab a yarda ba Amanin bata bu de idonta ba. Zuciyarta ce kawai take bugawa da wata irin k aunar Dahda mai zafin gaske tana kallo Iman ta shiga ha da musu abinda zasu buk ata. Har ta gama bata ce komai ba, tana jin abinda Iman in ta yanke shine mai kyau Dahda kuwa tun bayan fitar Imani sai kawai ya lumshe ido Ya jingina da kujera yana jin kansa yana matsa da wani irin ciwo. A hankali yake taune lips d insa. Daidai lokacin Amanin ta shigo kamar an jehota a firgice duk ta yi wani irin. Kallonta yake da mamakin yanayin da take kamar wata Mara lafiya. Zama ta yi a gefen kujerar da yake kawai sai ta samu kanta da saka kuka. Bai ce mata komai ba har ta gama kukan da ya tabbatar shine zai saka ta samu sauk in ra din da take ji a zuciyarta. Ta ago a fisge ta sauke ganinta a kansa kafin ta furta Dahdah da gaske kai ka haife ni? Shiru ya yi bai amsa mata ba, sai dai bai janye idonsa daga kanta ba, ya furta Kina tantama ne? Ta cije leb enta da k arfin gaske kafin a fusace ta ce Ina tantama, idan Uban da ya kawo y arsa duniya zai aikata abinda ka aikata, idan kuwa kai ka haife ni ka cuce ni ka cuci kanka Dahda, ka gaya min me yasa ka aikata min haka, kuma waye Uba na don ban yarda Kai ne ka haife ni ba Bai mata magana ba, Ya cigaba da kallonta yana fusgar leb ensa kafin ya mik e tsaye. Wata drawer taga Ya bu de ya zaro wani enveloped. Ya cilla mata a hankali ya furta Your answer Ya koma ya zauna yana furta Komai kika