← Book details Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 57

Sashe 55

Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta furta cikin sigar tambaya. Matar ta sake sakin murmushi ta furta warai kuwa, na San baki Santa ba, amma nan gaba ka dan za ki Santa, ta ce tana gaisheki ki kuma kula da kanki da abinda ke cikin ki, don a yanzu bata da wani abu mafi soyuwa da ya zarce ke da an cikinki a duniyar nan Hannu Ama ta saka ta Shafa cikin, zuciyarta na wani irin wuntsilawa bata so ta gasgata abinda yake ranta, amma tabbas ko ta k i ko ta so dole ta yarda Dada ya siyar da ita, Ya kawo ta inda za a tsafaceta a tsaface d an cikinta sai ta dinga jin wani irin takaici zuciyarta ta dinga zafi. A zafafe ta kalli matar ta ce Idan burinku d an cikin, ku cire shi ku bar ni naje na yi rayuwata kamar yarda kuke so Ba hurumina bane wannan Matar ta fa da tana sakin dariya. Sai kuma ta jawo food warmers masu kyau ta shiga zuba lafiyayyen abinci a cikin plate ta tura gaban Amani. Kallon abincin ta yi kafin ta furzar da huci. Ba zan ci ba, ki d auke daga gabana. Bata bi tata ba ta fice ta bar mata d akin. Amani ta yi saurin mik ewa zuwa bakin k ofar. Sai ta tarar k ofar irin mai thumbprint ce dole ba zata iya fita ba komai zata yi. Hawaye ya zubo mata, a hankali ta zube a saman tattausan carpet din tana sakin kuka. K amshin abincin ya dinga rinjayar yunwar da take ji don haka bata San sanda ta ja plate D in ta fara ci ba. Ita kanta ta manta yaushe rabonta da abinci don haka ta zage ta ci abincin sosai. Ta kuma sha sassanyan kunun ayar da aka ajiye mata. _______ Sai da gari ya yi haske sosai sannan Iman ta farka daga sumar da ita da aka yi a d akin asibitin, aka sakata barcin dole. Su Didi da Umma T, ta fara kalla kafin ta mik e tana jin kanta na wani irin sarawa. Bu de ido ta yi ganin agogo Ya nuna har k arfe 9:00 ta fara tunanin wani irin barci suka yi, don dai bata jin duka mutanen d akin sun yi sallahr asuba, idan kuma Sun yi me yasa ita basu tashe ta ta yi ba. Saman gadon Amani ta kalla sai ta ga wayam. Tunaninta tana toilet sai dai duk zaman jiran da ta yi, ba Amani ba labarinta. Da sauri ta mik e ta isa bakin toilet d in tana zabga kiran Amanin jin shiru yasa ta tura k ofar toilet D in taga wayam. Da sauri ta dawo akin idonta Ya hasko mata takarda. Ta isa da sauri ta fara karanta takardar tana jin bugun zuciyarta na k ara gudu ganin abinda yake cikin takardar. Kada ku neme ni, ba zan dawo ba, na yi nisan da ba zaku tab a samu na ba, ba zan iya zama ba, ba zan iya cigaba da rayuwa da ku ba Ta dinga kallon rubutun tana son ta tantance na Amanin ne ko na wani daban. Idonta ya fara zubar da ruwa. Bata san sanda ta k walla ihu ba. A razane Umma T, ta farka kafin Didi ma ta farka. Suka furta Lafiya Iman? Takardar hannunta ta nuna mata tana furta Umma T, ta gudu ta tafi ta bar mu. Umma T, ta zauna turus a saman gefen gadon dafe da k irjinta da ya matsanta mata da bugu. Kira wayarta Imaan, kira mu ji idan Har wayar na yi zan saka a yi tracking d inta duk inda take. Iman ta yi saurin d aukar wayar ta fara kira sai dai me, wayar Amanin tana d akin tana ringing alamar bata tafi da ita ba. Umma T, ta runtse idonta tana jin tashin hankalinta na sake girmama, ina Amani zata tafi? Wace rayuwa zata je ta yi shine abinda ya tsaya mata a rai. Didi kuwa ba bakin magana don maganar ma ta d auke sai bin su take da ido cikin tashin hankali. Turo k ofar da aka yi ne ya saka su juyawa gaba aya. Ya shigo cikin d akin fuskarsa ba yabo ba fallasa. Sai zabga k amshi yake kasancewar garin sanyi ne, jikinsa sanye yake da riga da wandon jeans sai jibgegiyar rigar sanyi a jikinsa, hannayensa sanye cikin aljihun rigar. Umma T ta d auke kai daga kallonsa. Har cikin d akin ya shiga yana kallonsu da yanayin tambaya a idonsa sai dai ya kasa bu de baki ya yi tambayar. A zafafe Umma T ta ce Hankalinka ya kwanta ko? Ka Yi ruining rayuwar Amani, ta tafi ta shiga duniya tunda hakan ka zab ar mata. Ya waro ido yana furta What? Fateemah ta yi tsaki tana furta Ai na San ka ji sarai abinda na ce, Amani ta tafi, ba irin kunnenka da ban ja ba Moddi amma sai da ka aikata abinda ka so, yanzu me gari ya waya? Me kake so muce da mutane? Shiru ya yi yana taune lips d insa, yana danna waya sai kuma kamar Wanda aka ce tashi, ya tashi da sauri ya nufi waje wayar a kunnensa Fateemah ta bi shi da kallo idanunta har yaji suke saboda hawayen da Moddibo yake saka ta. Didi ma binsa ta yi da kallon don ita yanzu ko magana bata iya yi ciwon hawan jini ya saka muryarta ta karye Iman kuwa haushin Dada kamar ya kasheta abinda ta lura da shi kamar bai damu ba, kamar ba abinda ya dame shi da tafiyar Amanin, tunda burinsa ya cika.. Yana fita ya shiga motarsa, tsabar turirin da zuciyarsa take masa ne yasa ya kasa driving d in ya zubawa wayarsa ido. Still numberr Alwan ta k i shiga. Taune lips d insa kawai yake yana Jin kamar ya rufe ido ya gan shi a Abuja. Kamar wasa a karo na barkatai wayar ta shiga sai dai instead of Alwan d in ya yi picking sai bai yi ba, ya turo masa text message Ka daina kira na, don ba zan amsa ba, ka gama mana aikin mu bamu da wani sauran business da kai yarinya kuma tana hannun mu. Moddibo ya waro ido yana sake kallon message din mai hakan yake nufi? Alwan ya yaudare shi kenan? Har Abuja ya je Amma an sanar masa Alwan baya nan. Bai dawo daga wancan firgicin ba wani message din ya shigo masa Amani bata Nigeria Imam, kada ka yi wahalar nemanta zamu dawo da ita da zarar mun samu abinda muke so, Nima kuma ba zaka sake samu na ba da k arfi Moddi ya ce t Alwan, Don t ba haka muka yi da kai ba ya fa da a zafafe kamar Alwan din yana gabansa. Ya tura masa message amma bai tafi ba, da alama da gaske Alwan ya daina aiki da layin. Me kenan ya aikata me ya shiga Kansa da ya aikata komai ba shaidu? Me zai ce da Didi wani bayani zai yi musu? Dole ne ya yi shiru kawai da bakinsa ya dinga cijen leb ensa yana Jin kwanyar Kansa kamar ta tarwatse ba kowa ya jawo masa wannan matsalar ba sai Safna ta ina zai fara? Kiran numberr Alwan yake amma still wayar bata shiga. Ya kifa kansa kawai a saman sitiyarin motar yana sakin huci a hankali. A haka ne yake pretending kamar bakomai, kamar ba ya Jin komai a zuciyarsa Amma shi ya San abinda yake zuciyar tasa kamar an tsikare shi, ya sake fincikar motar da mugun speed. Allah ne ya kiyaye, Allah ne kuma ya kai shi gida lafiya ko motar bai rufe ba ya fito ya nufi cikin gidan . A bedroom dinta ya dinga jiyo hirarsu da dariyarsu basu San da zuwansa ba shi yasa suka cigaba da hirar cikin daga murya. Boss lady ta ce Kice dai gida ya zama naki, kai Safna kin iya tsiya, ya aka yi wai aikin ya ci har haka? Ba za ki gane ba Na ima, bafa k aramar tsanar yarinyar nan na yi ba, duk wani aiki da na yi a kanta baya tafiya min successfully. Ba k aramin asarar ku di take saka ni ba, yarinya sai ka ce aljanna. Alwan shine tsani na na cikar buri na, da abinda ya bani na yi amfani, na saka mata a furar da na san tana sha duk dare, na san Didi bata Shan sugar don haka mazubin da ake zuba mata daban ne, a cikin na Didin na saka maganin barci, shi kuma Imaam a kettle din shayinsa da yake sha duk dare kamar ibada anan na zuba maganin da na karb o wajen bokan, Wanda ya tabbatar min in dai suka sha a tare sai sun kusanci juna, koda ba a cikin hayyacinsu ba ne, na kirkirarwa kaina ciwon k arya don kawai na cika buri na sai gashi komai successfully, ai ina ta jira ki dawo daga South Africa ki sha labari. Zancen da nake miki suna can har tsohuwar zube a asibiti sakamakon bayyanuwar ciki a jikin yarinyar, cikin da na tabbatar koda tsiya koda tsiya tsiya sai na zubar da shi Da sauri Dada ya ja baya, yana k arin controlling zuciyarsa Ashe Safna ce da wannan mugun aikin, yaransa suke zargin shi ya saka musu magani suka kusanci juna. Ya dinga jin jiri a Kansa fisgar leb ensa kawai yake, yana k arin danne b acin ransa, bai kamata ya nunawa Safna ya ji komai ba, zai yi maganinta a lokacin da bata tsammani ba, shi yanzu burinsa ganin inda Amani take. Don haka ya shige part insa hankalinsa a tashe, duk wani layin Alwan da na Boss insa ba Wanda bai kira ba sun k i shiga A karo na biyu ta sake Jin motsi a bakin k ofar d akin da sauri ta gyara zamanta don wannan karan kam ta shirya fita daga gidan koda hakan yana nufin sai ta sumar da mai kawo mata abincin ne. A lissafin ta kwananta biyu a gidan ko wanka bata yi ba, ba kuma ta damu ta yi ba duk da nacin matar da take kula da ita. Ta
Chapter 55 · 0% Book details