← Book details Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 57

Sashe 27

Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zuciyarta na tuno mata da hanya mai sauk i ta ruguzuwar rayuwar Amani, dole ta mik e tsaye ta cikawa Alwan burinta ko itama nata burin zai cika, ta San duniya da mutanen cikinta zasu tsani Amani idan suka ji ta nemi mahaifinta da kanta. Wajen Bokan Neja da zata je Ya zama dole ta bijiro masa da zancen ko da taimakon da zai yi mata. Zata sakawa a sawa Amanin son mahaifinta kamar ta Mutu da tsananin sha awarsa Har shi Moddin daga haka burin ta zai cika. Zata yi amfani da wannna damar wajen mallakar Moddi ita ka dai, don da zarar ya bijiro da maganar aure zata sanar da shi zata nunawa duniya vedionsu tsirara da y arsa suna fasik anci. Shikkenan ta jefi tsuntsu biyu da dutse guda. Ta b atawa Amani rayuwa ta yarda ko Mijin aure bata ji zata samu .. ta tuno yarda suka yi da Muhammad Alwan a daren da ta je gidansa bayan samun numberrsa a wajen Moddi Sai da wayar ta yi ringing sosai Ya d aga. Nan ta sanar masa Matar Moddibo ce, Yallab ai naji wata magana kuma, ai rayuwa ba zata yiwu ba wannna harkar ba, ina a dai sake wata. Alwan ya saki murmushi yana furta Dole haka ne zai faru. And ina son ganinki ma personally ki gaya min when zamu ha Wata irin dariya ta saki ranta fes ta furta Yaushe kake so? Yau da daddare Ya furta a hankali zan turo Miki address na gida na. Farin cikin da zuciyar Safna take ciki ya kasa b uya. Ba ruwanta wallahi ko me yace ta yi yi zata yi in dai zai mayar da ita Hamshak iyar mai ku di. Ko ta baya zai biya buk atarsa da ita zata amince, ba ance yanzu duk da haka ake ku din ba. Da daddare wani irin shiri tayi na musamman, ta saka shegun kayan barcinta kafin ta bulbula sihirtaccen turare a jikinta. Maganin barci ta bawa Moddibo ta fice ba tare da ya sani ba. Tana shiga gidan ta San ta shiga inda ake kira Aljannar duniya. Burinta da son duniya ta ji Sun k aru. Zama ta yi a parlor na musamman da Alwan yasa aka kaita. Tana zama sai ga shi ya fito. Waya a kunnensa yana magana k asa k asa. Tana ganinsa ta saki murmushi kafin ta cire Hijab D in ta yar. Alwan runtse idonsa Ya yi kafin ya furta Subhanallah Ya juya da sauri yana furta Rufe jikinki Madam, ba na kira ki don haka ba ne. Jikinta a sanyaye ta rufe jikinta hankalinta Ya yi mugun tashi. Ya zauna fuskarsa a d aure yana kallonta Zubewa ta yi a gabansa zata fara bashi hak uri ya d aga mata hannu. Ya isa, ba zan gayawa Mijin ki ba, but da shara din nima zaki min abinda nake so, idan yaso daga baya if ina buk atarki zan gayyaceki yanzu dai ba don haka na kira ba. Idan kin k i amjncewa kuma ina da CCTV cameras har a parlorn nan zan nunawa mijinki abinda kika aikata. Da sauri ta ce Ka gaya min ko menene zan maka. Alwan ya saki murmushi yana gyara zama ya furta Na San Mijinki ya gaya miki yarda muka yi da shi yau. Ta d aga kai. Na San zai Miki wahala Amma ki yi hak uri for sometimes ne, ina son ki taya ni wani aiki idan har abinda muke so Ya samu ina tabbatar miki Mijinki zai yi wani irin masifaffen arziki da duk Nigeria ma sai an San da shi, ba mamaki ma Ya fi ni. Da sauri Safna ta ce gaya min koma menene wallahi zan saka shi, ko baya so ko wajen boka zan kai shi. Alwan ya jima yana kallonta kafin ya furta Za ki iya saka shi ya kusanci y arsa ta cikinsa Amani? Zuciyarta sai da ta buga, amma da ta tuna maganar ku di sai kawai ta d aga kai Zan iya koma Uwarsa ne ba y arsa ba, akwai hanyoyi da dama da zan bi sai hakan ta faru. Alwan ya mik e yana zagayeta kafin ya dure mata akwatin ku di a gabanta ta Ware ido tana kallon ku din. Ta ce Na menene? Naki ne, akwai ni ki su uku idan komai ya tafi successfully. Zan far bijiro masa da buk atar hakan ke kuma ki cigaba da taya ni yak i. Allah yasa ya amince. Ta wani zabura tana furta Dole ne ma zai amince ko baya so wallahi Ya bu de idonsa a hankali bayan ya gama dawowa daga tunanin mafarin arzikinsa da ya yi. Idanunsa sun ka da sun yi jawur. Ya kai dubansa kan agogo jin wani nocking mai k arfi da ake masa. 4:00 na dare gabansa ya wani irin fa duwa haka kawai ya mik e jikinsa a sanyaye ya na furta waye? Muryarta can k asa da k yar take fita ta furta Nice Dahda Sake ji ya yi gabansa na tsananta bugu ya saka hannu ya bu de k ofar ya kai idonsa kanta. A firgice take hankalinta a tashe ta furta Dada na shiga uku HADARIN GABAS PAGE 15. NAZEEFAH SABO NASHE 08033748387. BRIGHT PENS... 2nd batch Zazzafar tafiya mai abin ban mamaki, tawayen jerin marubuta hu u a sabuwar tafiyar ta second batch. *HADARIN GABAS* Nazeefah Sabo Nashe ARFE A WUTA* Ayushercool *ZAYTOON* Zee kumurya *MUTALLAB* Nimcyluv Sarauta. (Book one is free Book 2 and 3 paid. 500 Mutane Na Musamman cikin aji na Musamman 1k 2118665253 UBA Kallonta yake kawai shima cikin tashin hankalin yana jin duk wata jijiya ta jikinsa tana mik ewa. Da k yar ya d aga tattausan lips d insa ya furta Me ya faru? Imaan sai da ta ja ajiyar numfashi sannan ta ce Amani ce bata da lafiya, she is unconscious Tun kafin ta k arasa ya janyeta gefe da sauri cikin matuk ar tashin hankali ya nufi hanyar da zata sada shi da d akinsu. Tsoro yake ji sosai baya son wani abu da bai shirya masa ba ya samu Ama d A durk ushe take a bakin gadon hannunta rik e da k asan cikinta tana mirgina kanta cikin wani hali. Zufa ko ta ina sai zuba take a jikinta kamar ba A.c a d akin. Dahda ya k arasa cikin sanyin jiki kusa da ita yana furta me ya faru? Jin muryarsa ya sata sake runtse idonta musamman da ya kusanceta ya durk ushe a gabanta. Idonsa ya kai kan hannayenta da ya dafe cikin da su. Ya saki ajiyar zuciya yana kallon Imani ya furta Period cramps ne ko? Imani jijjiga kai ta yi tana furta Wallahi Dahda ba shi ba ne, ina zaton dai ko Aljannu ne suke son tab a ta saboda duk dare sai ta yi wani irin mafarki mai nuni da ta na having se Imaan! Amani ta fa da tana d ago kanta cikin wata irin kakkarwa ta fara girgiza mata kai. Bana so kada ki ce komai Dahda da ya shiga shock duk da Imaan bata k arasa abinda ta fa da d in ba ya san ragowar zancenta Ya rik e kansa a hankali cikin wani irin matsanancin tashin hankali. Daidai lokacin ciwon ya sake turnuk e Amani ba abinda take so irin tabbatuwar abinda yake cikin mafarkinta ta gan shi a zahiri.. tana son ta ji d umin Dahdah yana kusantar ta yana mata duk wani hot romance da take gani a mafarkin ta Dahda ya dinga kallonta yana observing yanayin da take ciki. Tsoro ne ya kama shi har ya dinga jin zuciyarsa na wani irin abu. A hankali ya kalli Imaan Ki matse mata lemon tsami a kitchen, ki kawo mata da ruwan tea Imaan ta mik e da sauri ta fice don yanayin Amanin itama yana bata tsoro. Bayan fitar Imaan Dada ya Janyeta daga jikinsa a hankali sai kuma ya ce.. Amani ya kike ji? Ya furta idanunsa a kanta. Cije leb enta ta yi tana bu de idonta a kansa sai kuma ta runtse take fuskar Dahdan ta zame mata irin waccen fuskar da take gani a cikin barci mai nuna mata tsananin k auna. Da ciwon ya sake murd deta bata san sanda ta shige jikin Dahdan ba ta kai masa wata irin runguma Dahda runtse idonsa kawai ya yi yana jin wata irin kakkarwa da Amanin ta saki a jikinsa kafin ta sauke ajiyar zuciya ta lumshe idonta. Sai sannan ta samu sassauncin abinda take ji. Rungumar da ta yi masa da k amshin turarensa da ta ji su suka saka ta releasing abinda ke jikinta. Dahda ya dinga kallonta k irjinsa na bugu. Ya mik e yana kallon Imaan da ta shigo da cups a hannunta Ki bata ta sha, ta kwanta ta yi barci kuma idan zaku kwanta you make sure kun kunna karatun Alk ani ku dinga kuma rufe jikinku, ji fa irin rigar da take jikinta ba dole koma mutanen b oyen bane su samu mafaka. Imaan ta d aga kai tana sake kallon y ar ficilar rigar da take jikin Amanin da ta bayyana duk wata sura mai nuna cikar d iya mace. Ta gyara mata gashinta sannan ta tasheta zaune. Dahdan yana tsaye yana kallonta abin duniya duk ya dameshi so yake ya yi nazari ya gano bakin zaren don an zo gab ar da ya kamata ya binciki al amarin mai kama da Almara. Amani kasa ha da ido da shi ta yi ga kunyar rigar da take jikinta wacce da ita da babu duk d aya. Imaan ta sha yi mata fa dan kwana haka amma bata ji. Dahda ya juya yana fita daga d akin da saurinsa. Tunda ya shiga d akin bai zauna ba, zagaye kawai yake zuciyarsa cike da tunani Dole akwai ayar tambaya me yasa al amarin yake faruwa haka? Bai bar tunanin ba sai da ya ji kansa yana neman tsawa sannan ya zauna rik e da kan nasa yana danna numberr Muhammad Alwan don kamar shi ya kamata ya tambaya. Me yasa abubuwan suke tafiya a haka kamar wani sihiri? Duk da san dalili. Ya ja fasali a hankali ganin Alwan
Chapter 27 · 0% Book details