← Book details Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 57

Sashe 18

Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

...... Hannun Muhammad Alwan ya ji a kafa darsa cikin wata irin murya mai bayyana lallashinsa ya furta Kada ka yi abinda zaka yi nadama Imaam, ko ka yarda ko baka yarda ba sai hakan ta faru gwara ma ka yarda d Girgiza kansa ya yi yana kallon cikin idon Alwan d Ba zan yarda ba, don ba abinda zai saka ni nadama na ji na tsani kaina a rayuwa kamar abinda kake son saka nin kuke son tursasa min sai na aikata shi Wannan karan Murmushi Alwan ya yi ya saki kafa dun Imaam d in yana furta As you wish ba zan hanaka yin abinda kake so ba you can do what suits you amma ka sani kana so ko baka so sai hakan ta faru gwara ma ka so d Tsaki ya zabga ya fice daga office d in da sauri. Alwan ya bi shi da kallo kafin ya zare handky d in da ke aljihunsa ya goge fuskarsa yana cigaba da mamakin taurin zuciya irin na Imaam. Ya san kuma dole abin ya faru da son sa ko ba son ransa. Ya lumshe ido kawai zuciyarsa a time d in ba abinda ba ta raya masa. Kada dai ya zama duk abinda suke so ya kasa faruwa dalilin taurin kan Imaam Har jiri ne ya dinga d ibansa kafin ya je gida tun a cikin jirgi yake jin zuciyarsa ba daidai ba. Da k yar ya isa cikin motarsa inda drivernsa yake jiransa ya yi saurin shiga cikin motar yana amsa gaisuwar Drivern. Gidan shiru alamar kowa ya kwanta don haka kansa tsaye ya nufi d akinsa. Wanka ya yi sosai kafin ya ha da coffee mai zafi ya sha burinsa ya ji ya daina jin abinda yake ji d in sai dai hakan bai samu ba. Da k yar ya samu ya runtse idonsa yana tunano mafarin ha duwarsa da Alwan da ya zama sanadiyyar shigarsa cikin wannan matsalar 10YRS BACK Wani irin zafin rana da ake ne ya saka shi parking machine d insa a gefen wani babban company. Ya zauna a saman bench yana jin kamar kansa zai tsage. Daga aiki ya taso k aramin ma aikaci ne shi a lokacin a ma aikatar aikin Jarida da take k ashin gwamnati. A lokacin ma rahoto ya je d aukowa sai ya samu kansa da matsanancin ciwo shine dalilin da yasa ya ajiye machine d in ya zauna a saman bench. Don sam ba zai iya cigaba da tuk ashi ba duk da k arin da ya yi na aikata hakan. Tsawon mintuna yana zaune idanunsa a lumshe ya dinga jin wani irin k amshin turare mai da din gaske yana ratsa k ofofin hancinsa. Da k yar ya bu de ido jin ana cewa Sannu bawan Allah.. Muryar bata masa kama da ta hausawa ba sai dai mutanen k asashen waje. Ai kuwa kamar yarda hasashensa ya ba shi wani kyakykyawan saurayi ne tsaye a kansa yana sakar masa murmushi. Sannu. Ya sake furtawa yana kallon gefe da gefen hanya. Na da de a tsaye anan baka sani ba, sai naga kamar akwai damuwa ko? Imaam ya tsuke fuskarsa don shi a rayuwarsa bai fiye son a shiga sabgarsa ba. Amma Alwan bai k yaleshi ba sai da ya zauna kusa da shi yana furta Nima aiki ya kawo ni Nigeria so kuma ban san ko ina ba ina so na maka tambaya? Allah ya sa na sani. Imaam ya furta yana kallon wani waje. Apartment nake so mai kyau na rent da zan zauna wanda ba zai ba ni damuwa ba Imaam ya yi shiru kamar ba zai amsa shi ba sai kuma ya ce Hotel ko gida? Any one. Alwan ya furta yana sakin murmushi abinda Imaam ya lura da shi Alwan ma abocin murmushi ne. Okay. Daga haka ya mik e yana d an ka de jikinsa saboda Imaam tun bai zama wani abu ba d an gayu ne na gaske. Ya hau machine d insa ya ce ya biyo shi. Alwan bai masa musu ba ya bi shi suka tafi har wani Apartment mai kyau ya ja ya tsaya yana kallonsa. Yauwa ka shiga sai ka musu bayani, ni zan wuce. Hannu Alwan ya saka ya rik e shi. Hakan da ya yi yasa Imaam ya dago ya tsareshi da ido. Alwan murmushi ya sakar masa yana d aga masa kai. Me yasa zaka tafi? Bayan ina murna na samu aboki a inda ban san kowa ba. Ka taimake min mana nima fa musulmi ne.. ko baka son lada? Ya fa da cikin gwamutstsiyar Hausarsa. Haka kawai Imaam sai ya ji ya amince da son kyautata masa Yanzu ya kake son a yi? Ni bana jin da di ne ina son na je gida. Cikin muryar tausayawa Alwan ya furta Oh Sorry, Amma pls mu yi exchanging number so that muna communicating.. Imaam bai masa musu ba ya amshi wayarsa mai d an banzan kyau ya saka masa numberrsa ya kuma yi saving da Imaaam Moddibo.. Alwan ya kalli sunan yana furta Nice . Ni kuma sunana Muhammad Alwan. From Turkey hope na samu d an uwa. aga kai Imaam ya yi daga nan ya masa sallama ya burga machine d insa ya wuce. Koda ya koma gida bai wani kira Alwan ba ya ma manta da shi. Y an biyunsa Iman da Amani ya yiwa wasa ya shige d aki.Safana ta bi bayansa ganin kamar baya jin da di. Bai b oye mata ha duwarsu da Alwan ba ya gaya mata komai. Murmushi ta saki tana furta Allah yasa ha duwar ta zama alheri Da sassafe ya dinga jin wayarsa tana ringing. Yana dubawa yaga Muhammad Alwan ne sai da ya mik e ya zauna sosai sannan ya saka wayar a kunnensa Morning Alwan ya furta cikin nutsuwa So ka tafi ka bar amanarka da Musulunci ya baka, baka sake kirana ka ji ya nake ba na kira kuma baka d aga ba. Imaam ya d an saki ajiyar zuciya ya furta Am sorry.. No problem yanzu ina so kazo ka raka ni inda za ni pls! Kallon agogo Imaam ya yi ya furta Ina zuwa aiki yanzu please ka zo idan akwai yiwuwar ka samu wani aikin da yafi naka sai kaga ka dace muna da companies a Nigeria and menene qualification naka? Ko da yake sai kazo dai.. Ya fa da yana kashe wayar. Safna da ta ji komai kasancewar wayar a handsfree take ta mik e da sauri tana furta Alhamdulilah Moddibo ka maza ka shirya ka je ba mamaki wahalarmu ce tazo k arshe, dama aikin gwamnati bakomai a cikinsa sai wahala.. an kallonta kawai Moddibo ya yi ya tab e baki ya shige toilet ba wai don yana ji zai amince ya karb i tayin da Muhammad Alwan ya masa ba. Wanka ya yi ya shirya cikin k ananan kayan da ya saba sakawa ya fito fes da shi sai zabga k amshi yake. Safna ta dinga kallonsa tana jin alfaharin kasancewarsa Mijinta. D an rungumo shi ta yi tana shafa masa wani turare da ba na komai bane sai na mallaka a kullum idan zai fita sai ta shafa masa sam baya kawo komai a ransa don ta iya salo da kissa iri iri. A parlorn su madaidaici ya zauna. Daidai lokacin da Iman da Amani suka shigo jikinsu a d arare yaran suna kallon Dahdansu da yake shan tea da k wai. Yawu suke ha diyewa don dai su ba shi aka basu ba. Kunu ne da k uli-k uli kullum Mommyn take sakawa a basu kuma ta garga di masu aikin da kada su kuskura su fa da k arshe ma ta saka duk aka musu dabaibayi sai abinda tace suke aikatawa. Don haka ba zasu tab a bu de bak i su fa da ba sai idan ta so. Idon Amani ya kawo ruwa tana kallon Dahda ta nuna k wan hannunsa. Da mamaki yake kallonta cikin tausayin yaran da kullum a fuskarsu zaka san su marayu ne ba su da walwala sam sai dai idan Hajja tazo gidan ta kwana biyu. Ya ja hannunta ta matsa kusa da shi ya furta Zaki ci ne? Ta d aga kai. Shiru ya yi kafin ya d ago yana kallon Safna ya furta Yaran nan basu karya ba ne? Ta ware ido tana furta In ji Uban wa? Ke dube ni nan baku karya ba? Ido Dahda ya zuba mata ya ce In ji Ubana Ya gutsiro k wan ya mik a musu duka dankali da k wan da suke cikin plate d in. Da wani irin sauri suka dinga ci har bai san sanda wata k walla ta fara zubo masa ba.. Daga ganin yarda suke ci ya tabbata yunwa suke ji. Sai da suka ci sosai sannan ya ha da musu tea mai kauri suka sha. Ya d ago yana kallon Safna As from today da yara na zan dinga cin abinci Safna ta ha diye wani mugun yawu tana furta Haba dai kawai kuma sai mu zauna da su cin abinci su hanamu sakewa Ya watsa mata wani kallo da ya sakata yin shiru bata shirya ba. Goge musu baki ya yi sannan ya bu de lunchbox d insu abinda bai tab a yi ba. Waro ido ya yi yana furta What? Me Ye wannan? da d umamen tuwo za su makarantar? Da sauri Safna ta waro ido kamar gaske hankalinta a tashe ta ce what a nonsense, wannan ai ba laifina ba ne laifin su Talatu ne bari a kira su a ji dalili Har ta je bakin k ofa ya jata baya da k arfin gaske ya wancakalar da ita saman kujera, idanunsa sun fito sosai ya furta Wallahi na samu laifinkine sai kin ga abinda zan miki. Don su nake nema na don haka dole a dinga ciyar da su da cima mai kyau ya fita tsakargida yana k wala kiran Mama Talatu da Inna Laraba. Da sauri suka fito daga d akinsu da yake gefen tsakargidan. Yanayin da suka gan shi a lokacin ya basu tsoro suka furta Baban yara lafiya? Lunch box d in ya cilla musu Meye wannan? waye ya ce a
Chapter 18 · 0% Book details