Sashe 38
Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta bi shi da kallo kafin ta furta Addu ar fa? Yau ka yafe? Sai ga Didi ta fito da d an hanzari tana furta Tsaya Moddi, bana son fitar ka gida ba addu a, duk saurin da kake ka dinga tsayawa ina maka addu a saboda ido da bakin al umma, don na lura Kai Sam addini da addu a basu wani zauna a ranka ba, kullum kuma fa dan hakan nake maka. Ya dan turo baki yana furta To ki yi sauri Didi, bana son na ja layi da yawa. Ta fa da yana mik a mata kansa bayan ya rusuna ka dan. Addu ar ta masa sai kuma ta tofa tana furta Allah ya tsare sharrin mutum da Aljannu Allah ya kareka. Ya amsa da Ameen yana ficewa daga gida. Mamaki yake me yasa har yanzu Didi take mayar da shi yaro. Ya saki murmushi shi ka dai bayan ya d ane bayan machine D in abokinsa da ya fara tsokanarsa an Autan Didi, wallahi ka ji da dinka, ka samu Uwa mai kula da dukkan lamarinka, inama duka iyaye haka suke? Murmushi kawai ya saki shi Kansa yana alfahari da Uwa kamar Didi. Makarantar ta B.U.K dank am take da y an mata da samari, kasancewar a ranar duk aka fara registration. Shigowar sa filin wajen ba wacce bata kalle shi ba a jikinsa ya dinga Jin hakan. Tsaki ya d an ja yana kallon abokinsa ya furta I hate kallo wallahi, su kuma matan yanzu basu da kunyar hakan. Salihi ya ce Aa fa wallahi kada ka zargesu kana da duk abinda suke so ne yaro, ai dole su kalleka Ma sha Allah. de ransa ya yi sosai kamar bai tab a dariya ba, yana Jin yarda y an matan wajen suke furta Subhanallah, Allah ya yi halitta bala P.CAP d insa ya ja ya rufe fuskarsa yana kallon Salihu ya furta idan an zo Kai na please ka kira ni, ina k asan bishiyar can. Kafin Salihi ya amsa masa har ya wuce cikin wata kalar tafiyar sassarfa da ta sake jan hankalin y an matan wajen. Suka bi shi da kallo. Ya zauna a saman wata kujera yana jan tsaki duk sai ya ji ransa ya b aci Sam baya son mata marasa aji. Idonsa a rufe cikin P.Cap ya dinga Jin ana buga table D in gabansa ga wani masifaffen k amshi da baibaye wajen. Cikin kunnuwansa ya dinga Jin sound D in yarda take taunar chewingum da wani irin masifa ya cire P.Cap D in daga fuskarsa idonsa ya fa da cikin nata data kafe shi da mayataccen kallo tana cizar leb enta Jikar Nashe HADARIN GABAS NAZEEFAH SABO NASHE 08033748387. BRIGHT PENS SECOND BATCH Takaici bak in ciki, da b acin rai ne suka dabaibaye zuciyarsa, a lokacin da ya kalli Safna, Ya dinga Jin wata irin tsanarta a ransa kamar ya saka hannu Ya bugeta. Wani irin rashin aji ne haka? Shi fa yana son Mace Ma aji wacce idan ka kalleta ma zata zuba maka harara ba irin wannan da take gabansa ba. Shi yasa ko aure zai yi zai sha wuya wajen neman matar aure don sai ya tantance sosai kada ya auro B ARAGURBI. Ya sake gintse fuskarsa Har girarsa tana alamar tattarewa gefe guda yana fin cikar leb ensa al amari ne da yake nuna kaiwa k ololuwa wajen b acin ransa. Madadin fushi daga Safna dariya ta saki ka dan irin dariyar shahararrun y an bariki ta kuma ja ta tsaya hannayenta a k irji ta furta Dole ka yi, kai da kanka ka San ka ha du, nice to meet you sunana Safna addu a ta guda Allah yasa department D in mu d aya. Idan kai da baka wajen ka yi magana to Moddi ma ya yi magana, shiru ya yi bai amsa mata ba ya sake mayar da P.Cap d insa kawai zuciyarsa na gaya masa ya tashi ya falla mata mari. Sai dai kawai ya share yana k ananan tsaki ya furta Bar nan wajen. Safna ta ware ido tana kallonsa ta ce In ji ina? Ai ni nan naga wajen zama A zafafe ya mik e Har yana y ar da P.Cap d insa ya saka hannu don d auka hannunsu ya sauka tare da na Safna ya bi hannun da kallo da ya sha zak ala zak alan farce kamar ba y ar musulmai. Caraf ta rik e P.Cap d in Har da manna ta a k irjinta tana furta Alhamdulillah na yi babban kamu wannan hular tafi min samun 100k yau Moddi cikin b acin rai ya d aga mata hannu sai dai ya rasa mai zai ce mata kawai sai ya danne lips d insa da harshen sa ya furta Fuck you kansa tsaye yana kallon cikin k wayar idonta. Safna ta yi murmushi ta ce Thank you. A hassala ya bar wajen yana jin idan ta sake biyo shi wannan karan sai ya mareta sai Allah yasa bata bi shi ba ta wuce da hular a hannunta, tana shinshina turarensa da k amshin sa ya mak ale a jikin ta. Hararar k asan ido ya bita da ita kafin ya tauna lips d insa a hankali yana furta Rubbish. Daga ranar Ya zama na duk inda Safna ta San zasu ha du sai ta bi shi. Ya yi mata jan idon amma sam bata ji. Gashi ajinsu d aya don department d insu guda. Tun kowa bai sani ba har jama a da dama suka targa da yawan nacin da take masa, shi kuma baya gajiya wajen yarfa ta a gaban kowa. Mata da yawa bayan ita Sun kawo masa tayin abota ko soyayya, sai dai kallo guda yake musu su bawa wandonsu iska. Don a idonsa suke hango wani kwarjini da alamun rashin wasa a tattare da shi. Kullum girarsa a tsare idan ka gan shi yana hira to cikin y an uwansa maza ne, wannan kuwa zaka tarar da shi yana faffa dan murmushi. Bai san abubuwan da suka faru, sai dai lokaci guda ya samu kansa dumu dumu cikin wata irin zazzafiyar k aunar Safna, da ko a mafarki bai tab a zaton zai riski kansa a haka ba. Sha awarta mai zafi ta kama shi ya dinga yin wasu irin mafarkai a kanta abin kamar sammu ko sihiri. Tun yana daurewa yana sharewa Har dai da kansa ya kai kanta wajenta wata ranar Laraba da ba zai tab a mantawa da ita ba. Address D in gidansu ya nema. A shekaru irin nasa Ashirin sai ya dinga ji kamar ya yi k anta da zuwa wajen budurwa Amma abinda yake ji a ransa ya hana shi togace kansa daga zuwa wajen Safna. Wanka ya tsala sosai ya shirya sosai cikin shigar da yake tafiyar da Imanin mata. Jikinsa ya d au k amshin masifaffen turarensa na MIYAKI Wanda a lokacin sai ka kai ka kawo kake fesa shi. Ya fita tsakargidan sai da ya ji gidan shiru sannan ya tuna basa nan sun tafi biki k auyen su Didin, sai ya ji missing Didi da addu ointa. Ya d an Shafa kansa kawai yana sakin murmushi da tana nan da ta tuni ta tofe shi da addu a. Fita ya yi daga gidan bayan ya ja k yauren gidan ya datse da mukulli, bai damu da ya yi addu ar ba ya nufi bakin titi direct don samun abin hawa. Inda za shi ya sanar da mai abin hawa unguwar Lamid o crescent. Tabbas Ya san unguwar masu ku di ce don haka yake ganin kamar ya yi tsalle Ya kai kansa inda Allah bai kai shi ba. Babban gida mai girman gaske nan Mutumin da Ya tambaya ya nuna masa. Nan shine gidan Aliyu Mak arfi d an samari wani ka zo nema a gidan? Kallo guda ya yiwa gidan ya ji kamar Ya koma sai dai so da k aunar Safna tasa ya kasa barinsa komawa. So yake ya bata surprise tunda har yanzu ya san tana son sa ba abinda zai faru In sha Allah. D an d aga kai ya yi yana amsawa Dattijon mutumin. Sai mutumin ya yi murmushi Ya dafa kafa darsa yana furta Ka kula, ka yi takatsantsan don jama ar gidan basu da mutunci , basu San mutuncin d an Adam ba, gani suke tunda suna da ku di za su taka Uban kowa bakomai ba ne a wajensu. Moddi ya d aga kai yana yiwa mutumin godiya sannan ya k arasa bakin gate D in. Suka gaisa da mai gadin da yake masa wani gani gani sannan ya gaya masa Safna yake son gani Mai gadin Ya bi shi da wani kallo kafin ya furta Dama kai ne bak on da Safna ta ce min ko mu da de ko mu jima zaka zo, idan kazo kuma na barka ka shiga. Na zata zan ga wani gwaska sai na ganka a kan sawayenka Moddi ya cije bakinsa yana tattare girarsa waje guda, sai mai gadin ya shiga taitayinsa ganin Alamun Moddi bai zo da wasa ba ya ce Bari na kira maka ita, shiga da ciki Moddi ya girgiza kai yana mik ewa ya ce Batta kawai. Da sauri Maigadin Ya ce Afuwa d an samari, Ban fa da fa don wani abu ba. Abin ne Ya bani mamaki ganin irin manyan mutanen da suke zuwa wajenta su fita a mota yau kuma sai na ga kai dai matashi ne da baka zarce shekaru ashirin ba, kuma da alama baka da Ba ni da ku Moddi ya fa da yana zuba birkitattun idanunsa kan na Mai gadin yana jin wani zallar b acin rai. Me yasa jama ar yanzu Sun fi girmama ku di ne fiye da mutunci? Da sauri Maigadin Ya girgiza kai yana furta Afuwa ban san da Soja nake tare ba ya furta yana k arin zubewa a gabansa. Moddi ya saka hannu Ya d aga shi yana sakin murmushin da bai shirya ba ya ce Baba wa ya ce maka ni Soja ne? Mai gadi Ya girgiza kai yana furta Ai ba sai an gaya min ba, kwarjinin idanunka ya isa ya tabbatar da haka, ka godewa Allah