← Book details Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 57

Sashe 25

Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

furta Ba zan iya abinda suke so ba Zaka iya Imaam, ka yi koma me suke so? Yanzu fa ba abinda baa yi saboda ku di, ana ya Kai Kai, mutum yana kwanciyar da y ar cikinsa, da Uwar data haifeshi ma saboda ku di, ana luwa di da ma digo saboda ku di, ana bada Uwa ko y a Yaya ko k anwa, K ani ko wa? Duk saboda ku di, don haka ka yi ko me suke so Moddi Saboda ku bana son musu ta fa da tana zame kanta a duk sunayen da ta ambata, bata k i ya yi komai ba in dai zai samar musu da ku di, bata damu ta ji shara din da suka bashi ba. Imaam Ya saki ajiyar zuciya, sai ya ji ya samu k warin gwiwar bayar da mahaifarta tunda ita ta jawowa kanta ta ce ya yi komai saboda ku di. A zuciyarsa Ya dinga jin baya so, amma harshensa ya kasa amince masa ya furta baya so d in. Ya kalli Alwan da Ya shigo d akin idanunsa a kansa shima ya ce Yaya Aboki? Ka yarda ko a a? Abu guda dana sani baka isa ka San sirrinmu sannan ka bijire mana ba JIKAR NASHE. HADARIN GABAS Page NAZEEFAH SABO NASHE 08033748387. (Book 1 free. Book 2&3 paid ne) Ku saka ku dinku anan account d in don samun Shiga paid group. 500 (0000612945 TITAN TRUST BANK) mutanena Na Musamman cikin Gida Na Musamman 1k Dai Kacal as Usual. Jikar NASHE LOVES YOU ALL.) BRIGHT PENS... 2nd batch Zazzafar tafiya mai abin ban mamaki, tawayen jerin marubuta hu u a sabuwar tafiyar ta second batch. *HADARIN GABAS* Nazeefah Sabo Nashe ARFE A WUTA* Ayushercool *ZAYTOON* Zee kumurya *MUTALLAB* Nimcyluv Sarauta. Na amince Shine abinda ya ce yana jin kansa yana wani irin sarawa. Alwan ya d ago yana murmushi kafin ya zare glass d in fuskarsa ya furta Ka kyautawa kan ka, wannan ya zama sirri a tsakanin mu, Zan baka maganin da zaka mata amfani da shi a lemo komai zai tafi yarda muke fata successfully. Sannan Daga haka zaka samu duk abinda kake buk ata zamu ajiye ka a companyn da zaka dinga samun ku di ba k akkautawa kafin wata buk atar ta bijiro Congratulations Mr. Imaam Moddibo and welcome to the Family sakin ajiyar zuciya ya yi yana furzar da huci ka dan gani yake kamar ya yi gaggawar amincewa da buk atar da suka zo maka da shi. Idanunsa a lumshe Alwan ya mik a masa ruwa mai sanyi. D an bu de lumsassun idanun nasa ya yi yana kallon Alwan d in da yake kallonsa fuskarsa cike da murmushi ya d aga masa kai Bai yi musu ba ya karb a ya saka a bakinsa ya shanye tas. Sai ya ji kamar an tafi da tsoron da yake zuciyarsa wata nutsuwa ta shige shi. Alwan ya mik a masa wani dogon file me d auke da takardu a ciki Ka yi signing. Ka kuma cike form d in company. Hannunsa har rawa yake ya aikata abinda aka ce masa. A ranar Alwan ya kai shi masauki sannan ya saka aka kawo masa abinci mai rai da motsi bai bar hotel din ba sai da Imaam ya ji alert d in 50million a account d insa. Yana ware ido yake kallonsa da neman k arin bayani. Na siyan kayan sawa, waya da duk abinda kake buk ata. Ai kana da y a ko? aga kai kawai Imam ya yi don ba shi da karsashin amsawa. To ka musu hidima ka ajiye musu duk abin buk ata zamu yi wata tafiya da kai zamu yi 2weeks don zan nuna maka yanayin business d in da zaka dinga mana. Zan sake jaddada maka bama son surutu, ka gane ko? Imaam ya d aga kansa yana kallon Alwan din ya fice da sauri saboda kiran wayarsa da ake ta yi. Sai sannan Imaam ya saki ajiyar zuciya yana rik e kansa da ya ji yana sara masa ka dan. A ransa yake jinjina girman wautar sa na amsar tayin kasuwancin da bai san menene ba? Ga bayar da mahaifar matarsa da ya yi. Anya bai yi kuskure ba duk da wata zuciyar na tunasar da shi Ku di Imam! Ku di zaka yi yaranka zasu huta Hajja su Huta da Yayyenka matarka Kuma ai ita ta janyo koma me ya faru wayarsa da take k ara ce ta dawo da shi cikin hankalinsa idanu ya kai kan wayar ganin numberr wife sai da ya ji gabansa ya fa di da ya tuna abinda ya aikata mata.. bari dai ya gaya mata idan ta yarda shikkenan idan kuma bata yarda ba kawai sai ya hak Yana saka wayar a kunnensa ta furta Hope dai kun gama kuma ka amince da dukkan shara dansu? Shiru ya yi yana jan ajiyar numfashi Moddi baka ji na ne? Ya furzar da iska ya furta Ina jin ki.. sun zo min da abinda nake tunanin ba mai yiwuwa ba ne Ba wani abu da ba mai yiwuwa bane Moddi a duniyar nan Moddi ka amince da komai suka ce maka. Duk duniyar haka ta riki de ta koma yanzu kowa ka gan shi ka k yaleshi kawai da guntun kashinsa a gindinsa don haka in dai ni zan baka shawara kawai ka aikata abinda suke so yanzu ake yankan kai ma don a samu ku Imam ya d an waro ido Yankan kai fa? Eeh yankan kai kai in gaya maka mai k at mutum yana sadaukar da Uwarsa ko y arsa ko y aruwa don ya yi ku ta cire mata don koda wasa ba zata so Moddi ya bada ita a yi tsafi don ya samu ku di ba, amma bata k i ya bada Hajja ko Y ansa ko Yayyensa ba. Moddi ya ji wani abu ya daki k irjinsa ya ce Haba dai? Allah ya kiyaye. Ameen, ai ina gaya maka ne ka amince da duk me za su ce maka, har luwa di ake da mutum don ya samu ku Wannan karan sai da Moddi y runtse idonsa ya ji gabansa yana wani irin bugawa. Ajiyar zuciya ya yi ya furta Shikkenan, bari na kwanta. Ya latse wayar yana sakin murmushi sai ya ji zuciyarsa ta daina nauyin da take masa ya ji ya amince da sallama mahaifarta tunda ita ta jawowa kanta. Wato tana tunanin ya bada uwarsa da y ansa amma bata tunanin ya bada ko farcenta? Ya tab e bakinsa kawai yana kurb ar lemonsa mai sanyin gaske Wannan shine mafarin samuwar arzikinsa don daga lokacin da suka yi tafiya ya je yaga yanayin business d in, shikkenan Alwan ya sakar masa jan ragamar companynsa na turkey da yake Abuja. Bai fiye zuwa Kano ba. Ya kuma kasa sanarwa da Didi sana ar da yake ya dai ce mata companynsu sun koma Abuja an kuma yi masa k arfin girma. Fatan alheri ta masa tana furta Ka dai kula Moddi, ka saka Allah a gabanka ka kuma kula da amanar da Allah ya baka ta yaranka bana jin da din yanayin yarda yarannan suke rayuwa a gidanka.. aga kai shi kansa sau tari baya son irin rayuwar da suke sai dai ba yarda zai yi ne, idan ya yi nufin tsawatarwa sai Safna ta janye hankalinsa. Sau tari Didin na zuwa ta kwana musu biyu don ita da kanta ta ce su dawo hannunta Umma Dee ce ta hana tana furta idan suka dawo Didi Ai makirar matarsa sai ta yi murna ta ci galaba akan mu, gidan Ubansu ne dole su zauna wallahi. Hakan ne yake togace Didi daga janye yaran zuwa gidanta. Don kam bata ja da duk abinda Dijatu ta ce. Ranar da ya gama gininsa da yake ciki a yanxu, kasa gayawa Didin ya yi sai Gidan Umma Tee ya ya sanar mata ga shi a lokacin ma Safna ta riga ta matsa masa sun tare cikin murna da zakwa di tana ji dai da fankamar mijinta ya zama mai ku di. Umma Tee kallonsa ta dinga yi tana mamakin abinda ya ce mata. Ka gama gida Moddi? Har kun tare a ciki ba tare da Hajja ta je ta gani ta saka albarka ba? A hankali ya sunyar da kansa yana jin kansa da jikinsa sun masa wani irin nauyi tabbas ya san bai kyauta ba, amma baya sanin rashin kyautatawar tasa sai ya aikata abin rashin kyautatawar sannan yake dawowa cikin hankalinsa. Abin ne yazo bagatatan ki rufa min asiri don Allah kawai ki je ki gaya mata Tsam ta yi da ranta tana nazarin idanunsa Wai Anya kuwa Kido baa canjawa Didi kai ba? Ta fa da wata k walla na shirin zubo mata. Idanunta sun ka da sun yi jawur. Shima sai ya samu kansa da zubar k wallar Ni kai na Tee ban san me ya same ni ba? Wasu irin abubuwa nake aikatawa da ban san ya aka yi tunani na yake gocewa ba sai na aikata na ji ina da na sani Hawayen ta share ta ce Shikkenan akwai Allah, yanzu ka tashi mu je gidan Didin ka gaya mata da kanka ka kuma bara hak urin rashin sanar da ita da baka yi da wuri ba. Zaka iya cewa gudun kada ta maka fa da ne. Ya d aga kai yana amincewa da shawarar da ta ba shi. Suka tafi gidan Didin. Tun a mota ita kanta Fateeman ta dinga mamakin zundumemiyar Motar Moddin mai kyan gaske. Kiddo sun k ara maka matsayi a wajen aikin ne? Ta furta don ta kasa shiru. D an murmushi ya yi yana d aga kai ya furta Eeh, sun k ara min mantawa na yi ban sanar da ku ba Ta saki ajiyar zuciya kawai tana furta Anya Kido kana dagewa da Azkar kuwa? Ya d an saci kallonta a idanunsa ta ga rashin gaskiya don ya kasa kallonta sai d an cije leb en da ya zame masa jiki yake yi. A kula dai da addini da Azkar ba don komai ba sai don duniyar yanzu gaba d ayanta abar tsoro ce. Ya d aga kai kawai daidai lokacin suka zo gidan
Chapter 25 · 0% Book details