← Book details Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 57

Sashe 36

Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi k aura ta mik e da k yar tana dafa bango saboda ciwon gwiwa da ya sakata a gaba ta shige parlor. Moddibo ya bi bayanta yana jin yarda ransa yake masa rashin da di ganin irin wahalar da take sha kafin ta mik e ya zama dole ya kaita k asar waje ta ga likita. A daf da ita ya zube bayan ya taimaka mata ta zauna a saman kujera shi kuma Ya dafa k afarta yana d an sakin ajiyar zuciya ya furta Ina kewar Didi na. Murmushi mai girma ta saki kafin ta dafa kansa ta furta Ni ma ina kewar Moddin Didi. Ya saki murmushi ka dan sai kuma ya kama hannayenta yana furta Yau duk wannan ta kau Didi, don Allah kizo ki koma sabon gidan dana gina, ko don ki taya ni kula da y an da y ar riga ta bar min Ya fa da yana kallon idonta suna sakin murmushi a tare sai kuma ya marairaice fuska yana furta Please Didi, na yarda duk bayan sati guda ki zo nan ki kwana biyu, ko a kawo ki juma a ki koma lahadi don abincin sadaka Shiru ta yi tana kallon idon Moddi da ya bayyana son a tausaya mata. Sai ta ji duk hankalinta ya tashi, ta ji tana son ta koma inuwa guda da Moddi ko don kula da tarbiyyarsa da ta yaransa ma gaba d aya. Zuciyarsa ta dinga bugu, Ya dinga jin tsoron amsar daga bakinta. Kallonsa kawai take murmushi na son sub uce mata ganin yarda ya bayyana tsoro da fargaba k arara a idonsa a hankali ta furta Na amince Moddibo ko yanzu kake so zan bika mu koma Allah ya yi maka albarka Wani irin farin ciki ya shiga ransa Ya bu de ido yana mamakin saurin amincewarta ba tare da ta sake tambayarsa wace Sana a yake yi Ya tara Uban ku di haka ba Yanzu fa Didi. Yanzu kuwa Moddi, ba dai ka saka duk abinda nake buk ata ba, amma dai ka jira ni ka dan na yiwa mak ota da abokan arziki sallama idan yaso gobe sa biyo ni su ga gida. Farin cikin da yake ciki ne yasa ya rungumeta ba tare da ya sani ba. Nata farin cikin ya ninka nasa don haka itama ta rungume shi sosai a jikinta tana jin kamar wancan Moddin d an jariri da ta haifa ta Raine shi cikin so da kulawa. Mamaki bai sake kama shi ba, sai da yaga ta shiga cikjn d akin ta fito da babban mayafinta ta rufa a kanta sai kuma ta yi hanyar waje tana furta Ka kira y an uwanka ka shaida musu yanzun nan. Hannunsa Har rawa yake Ya ciro wayar ya fara kiran wayar Fateemah. Ita Ya kamata ta fara jin wannan kyakykyawan albishir D in. Sanda ya sanar da ita a ru de ta ce Moddi bana son wasa, Didin ce ta amince ba wani ja in ja. Ya yi dariya mai sauti yana furta Ki zo Railway yanzu, don ki tabbatar. Yana zaunen bayan ya gama ha dawa Didin kayan da zata buk ata kamar su radio da sauran y an tarkacenta. Sai ga Didi ta dawo mak ota fal a bayanta tana furta Ai ina fa da musu suka biyo baya na, Har da masu kuka na dai sanar musu duk juma a zan dinga zuwa nan don haka kada ka sake ka sab a alk awari. Moddi Ya jinjina kai yana furta In sha Allah, gobe ma zan saka a zo duk a kwashe su, su je su ga gida. Hakan ya yi. Didi ta furta tana d aukar radionta y ar gado suka fita da Moddi, mak ota na bin su a baya Har da masu kuka. Sai da Didi ta shiga mota sannan suka watse suka bar wajen jikinsu a sanyaye suna jin kamar wani sashe na unguwar gaba d aya suka rasa. Ba abinda yafi zama da mak oci lafiya Haka suka isa sabon gidan Didi da hadimarta a bayan motar. Suka shiga babbar harabar gidan mai tsananin kyan tsiya. Moddi yana jiran Ya ga tashin hankali a fuskar Didi sai bai ga komai ba illa zallar farin ciki tana bin harabar gidan da kallo tana furta Ma sha Allah, Jalla abin godiya idan ba Allah ba waye zai yiwa Moddi haka? Dubi gida kamar ba na Moddi ba, Moddi da Ya sha gwagwarmayar rayuwa, idan baka manta ba fa Har nik a ka min a k ofar gida. Ya d an turo bakinsa yana shiga gidan, duk wani tsoro da taraddadi da yake zuciyarsa ya kau ganin Sam Didi bata damu ba, bai sani ba ko itama Safna ce ta rufe mata baki ruf. Part d inta ya kai ta. Babban parlorn da Ya sha duk wani kayan jin da di sai kuma k arami guda da aka yiwa adon tuntun kamar gidan sarakai. Akwai d akuna biyu a gefe da gefen na Didin Wanda Ya ce na Imaan da Amani ne tunda kin ce ba za a musu aure ba tana dariya ta furta warai kuwa, auren su ba yanzu ba sai Sun sake wayo, amma menene dalilin hakan? Su ka rabu da su kenan? Saboda matarka? Ya girgiza kai. A can ma akwai d akunansu, ranar da ba kya nan sai su je can su kwana. Ta jinjina kai tana furta Allah ya kyauta, su basu dawo ba ne? Ya d aga mata kai Ke na fara kawowa sai gobe su kuma sai na kawo su, Uwa ce gaba da kowa ai. Farin ciki Ya tsarga a zuciyar Didi, ta dinga jin dama su dawwama haka Moddinta Ya dawo kamar wancan Moddin mai so da k aunar ta. A zuciyar ta tace In sha Allah, Allah zai kawo wacce zata dawo min da Moddi na. Ta gyara zamanta tana sake nazarin gidan kyau kam iya kyau gidan ya yi ba makusa. A hankali ta mik e ta murd akin da aka ce na su Amani ne. Idanunta suka sauka akan hotunan y ar riga. Ta dinga bin su da kallo d aya bayan d aya idanunta na son zubar da ruwa. Hoto guda ta d auka a hannunta ta k ura masa ido ba zata manta ranar da aka d auke shi ba, hoton ya tuna mata da lokutan baya da yarda komai ya canja a yanzu don haka kawai ta zauna a gefen gado idonta a lumshe yana zubar da hawaye tana tuno Uban Moddi da y ar riga. Tarihin rayuwarsu ta baya ya dinga dawo mata daki daki a kwanyarta Shekaru arba in da suka wuce baya Jikar Nashe HADARIN GABAS NAZEEFAH SABO NASHE 08033748387. Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/Kztc35CmtLK45zM8fQmmSY (Book 1 ne free Book 2 and 3 paid ne. Contact this number for subscribing . 08033748387.) BRIGHT PENS SECOND BATCH Abubuwa da dama sun Faru a rayuwarsu, wasu tana Jin da din tuna su yayinda wasu take Jin bak in ciki da k una a cikin zuciyarta idan ta tuna su. Da gaske duniya juyi-juyi ce yau fari gobe tsumma musamman ga y an uwa irinmu talaka. Rayuwa ta yiwa iyalen Uban Moddibo zafi a wancan k arnin kafin komai yazo Ya zama sai labari Yaransu Shidda rigis mata, kafin samuwar Moddibo duk da suna son haihuwar namiji sai dai hakan bai yi tasirin rusa soyayyar da suke yiwa yaransu mata ba. A basu da shi din suka d auki d awainiyar karatunsu tun daga primary har zuwa secondary. Malam Lami do Uban Moddibo Sam kasancewarsa mutumin da, da yazo daga Rugar fulani bai saka zuciyarsa ta jahilce shi wajen bawa yaransa ilimi daidai gwargwado ba na addini da na boko. Dijatu ce babba sai Fateemah, Sa adatu, Maryam, Kareemah da Jameela. Kafin su samu cikin Moddibo a lokacin Dijatu da Fateemah sun zama matasan y an mata masu kyau don duk yaran Didi sai Allah ya taimaketa ya bata su kyawawan gaske. Sai dai bayan Haihuwar Moddibo da ya yi Kama kwabo da kwabo da Fateemah sai aka ga Ashe ba wani kyau suke da shi ba, kyau kam mai suna kyau sai Moddin Didi. Samuwar cikinsa Malam Lami do Ya kwanta jinyar da ko tafiya baya iya yi, a haka Didi ta dinga jinyarsa tana kuma kula da laulayin cikin da yazo mata da masifaffen laulayin da bata tab a ciki irinsa ba. A Daren da ta haifi Moddibo wani irin zallar farin ciki ta dinga gani a fuskar Lami do Wanda bai tab a yi ba a duk sauran haihuwarta. Yasa a ka d ora masa shi a saman cinyarsa yana binsa da kallo murmushi d auke a fuskarsa Ya furta Allah ya raya min Kai rayuwa mai albarka, Ubangiji yasa ka zama sanyin idaniya a wajen mahaifiyarka da y an uwanka, ni dai kam na San bana raye zaka tashi, da na nuna maka kulawa da gata sosai Amma a hakan ma Alhamdulillah na San zaka Maye gurbina wajen kula da k annenka da mahaifiyarka, ina fata ubangiji ya baka managarciyar mace da zaka yi alfahari da aurenta . Bayan gama masa addu a ya sunkuya ka dan ya masa hu duba da Muhammad Moddibo. A ranar Sunan Muhammad Moddibo a ranar Malam Lami do Ya bar duniya. Tashin hankalin zuriyarsa kam ba a magana musamman Didi. Sun yi kukan rashinsa kamar ba gobe don duk da bai kasance mutum mai wadata ba Amma yana daga cikin maza masu kula da ci da Shan iyali da suttura daidai gwargwado. Sanda ya Mutu bai bar musu komai ba sai gidan da suke ciki. Tashin hankalin da Didi take ciki ya ninka na yaranta ba don komai ba sai don tana tunanin ta inda zata fara. Duk da tana y ar sana arta ta siye da siyarwa sai dai sana'ar ba inda zata Kai ta don sana ar ma bata farata ba sai bayan da Uban Moddi Ya kwanta ciwon ajali. Wannan tashin hankali da take ciki sai ya shafi har kula da Moddibo dole kulawarsa ta koma wajen Fateemah ita ke masa komai idan har yaje wajen Didi to kuwa shayar da shi zata yi. Hakan ya sanya wata irin shak uwa a
Chapter 36 · 0% Book details