Sashe 7
Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bata nan kike kiranta da sunan Magajiya da bata so ko? Kin san dai rigimarta ba ruwana idan ta tashi. Inna da yunwa fa na tashi baku gama naku abincin ba ne? ta furta tana murza cikinta da yake mata k ugi. Inna na murmushi ta ce Mun gama Fulani, yana can kitchen d in baya kuma mutuminki yau aka yi kunun gya da da alala da mai da yaji. imani ta saki murmushin jin da di don da gaske tana son abincin gargajiya fiye da jagwalgwalon abincin k asashen k etare da muka ara Muka yafa, banbancinsu da Amani da abincin ma sam Bai dameta ba ta fi ganewa kayan k walama da black tea da suke rayuwarta don haka da abinci da babu duk d aya suke a wajenta shi yasa take nan kamar a hureta ta fa di ita kuwa Imani dumur mur take. Bari na kawo miki, sai ki fi jin da din yin naki aikin da k arfin jiki. Inna Talatu ta fa da tana ajiye dusterr da ke hannunta ta bi ta k ofar baya da ke kitchen d in ta fice. Kafin ta dawo Imani har ta fito da frozen fish ta saka a bowl ta zuba masa ruwa kafin ta janyo plantain da dankali ta fara feresu. Ta yi saurin d aura black tea da ya ji kayan shayi masu mugun k amshi. Inna Talatu ta shigo tana mik a mata abincin Ci ki k oshi y ar gidan Inna, ki bar alank osa ana can ana fama da bargo. iman dai ta yi murmushi ta fara cin abincin don sau tari bata fiye magana ba. Haka ta dinga aikin cikin karkasashi tana yi suna hira da Innan da take nata aikin na goge goge a gefe. Har suka gama Amani bata tashi ba, duk da addu ar da Imani take na kada Allah yasa Mommy ta fito Amani bata fito ba addu arta bata amsu ba. Don suna wanke kwanuka a sink d in dadda dan turarenta ya dinga kusanto su a Kitchen d in wanda shine alama na cewa ta fito kafin Inna talatun ta yi saurin matsawa daga bakin sink d in don ta san sarai Mommyn ta hanata tab a komai a kitchen d in dokar Dada ce Mommyn ta shigo idaninta akan Hannun Innan da take rawar jikin ajiye bowl d in hannunta. Rawar da hannunta ya fara ganin idanun Mommyn a kanta ne yasa bowl d in sub ucewa ya fa di ya fashe. Mommyn ta bi bowl d in da kallo kafin ta girgiza kai tana Cije gefen leb enta ta furta Talatu Kunnen k ashi ne da ke ko? Sau nawa na ja kunnenki akan tab Min komai na kitchen d ina? Ban gaya miki Moddi baya so ba? wani irin firgici ne ya ziyarci Talatun da sauri ta girgiza kai. Iman kanta a tsoracen take musamman ganin b acin rai ya bayyana a fuskar Mommyn duk da tsufan Talatun ba zai hana Mommyn ci mata mutunci ba don hakan Sabonta ne, su kansu ma aikatan sun sha fa da don Didi da jikokinta suke zaune a gidan don ta Dada da matarsa kam da tuni sun bawa hammatarsu iska to Didi ce ta kawo su gidan ba don komai ba sai don su kula da jikokinta tun suna tsumman jarirai sakamakon rashin Mahaifiyar su da suka yi a wajen haihuwa shi kuma Dada ya kasa bada su saboda k aunar da yake musu musamman bai tab a haihuwar wasu yaran ba sai su. Ki yi hak uri Hajiya, In sha Allah ba za a sake ba Ai dama ba zaki sake d in ba in dai a gidan nan ne, a yau nake son ki tattara komatsanki ki bar gidan nan dama ido kawai na saka miki don na gaji da munafuncinki Gaban Talatu da na Imani ya fa di lokaci guda suka kalli Mommyn a tsorace. Mommyn ta ja tsaki tana furta Na baki just 30 minutes mintuna talatin ki fice daga gidan nan in dai ba dake Moddi ya gina gidan ba Daga haka ta juya bata tsaya ko ina ba sai d akin y an matan. A kan Amani ta tsaya fuskarta a ha de tana kallon yarinyar tsanar da take musu na sake hauhawa da gaske sam bata son ganin su a rayuwarta musamman a danganasu da Moddinta. Hannunta ta saka ta tsinkawa Amanin mari. Da sauri Amani ta bu de idanunta, ta bu de su cikin na Mommy da take tsaye tana huci ta furta Don Ubanki ke har yanzu ma barci kike? Wato baki ki warning da na baki ba ko? Will you stop looking at me or not? Sai na sake marinki Amani ta mik e fuskarta cike da gatsine ta furta wallahi da na rama don ni ba jakarki ba ce, wancan ma da kika yi don kin san shammata ta kika yi de baki Mommy ta yi ta furta Da kin rama? Amanin ta sake tsayar da idanunta cikin nata ta furta Exactly what I said, ki sake gwadawa ki gani Daga haka ta fa da toilet tana jan k aramin tsaki ta furta Oloshi duk da bata san kalmar da ta fa da ba. Mommy mutuwar tsaye ta yi ta kasa aikata komai wani irin b acin rai yana dugunzuma zuciyarta ta furta Bari ki fito zaki maimaita hakan a gaban Ubanki y ar iskar yarinya mai idon ibilisai Amani da take toilet tana jinta ta d an waro ido tana kallon mudubi a hankali itama ta furta Da ni nima kike zancen daga ke har Dadan ta saki murmushi tana kallon kanta a mudubi ta furta Zaku yi bayani a gaban Didisko. Daga haka ta yi saurin fara wankan tana shafa fuskarta da jin zafin marin da Mommyn ta mata. Ta rantse sai ta rama ta hanyar da Mommyn sai ta yi dakacen bata mareta ba. A nutse ta yi wankanta kamar yarda ta saba koda yaushe ta fito kuma ko mai bata shafa ba ta zura wata half gown da ka dan ta wuce mata gwiwa gashin yarda yake a cukurku de ta sake na deshi a hakan tana tsaki don ba abinda bata so irin gyaran gashi. Idon nan ko kwalli babu balle a je ga shafa jam baki ta fice da sauri tana y ar wak ar da ta zame mata jiki. KISHIYAR UWA BA UWA BACE cak ta tsaya da wak ar da take ta tsuke fuskarta duk da gabanta ya fa di ganin Dadan a zaune bai sa ta karaya abu guda da ta sani yau da k yar idan Dada bai sumar da ita ganin yarda yake watsa mata mummunan kallo da fusatattun idanunsa.. Ta maze ta d an kalleshi tana furta Barka Da safiya Dada.. ta ja kujerar Dinning don zama ta ci abincin. Ba tare da ta sake kallon Dadan ba. Wata tsawa da ya sakar mata da har hakan yasa Imani sakin cup d in da take shan tea ta d ago tana kallon Dadan Pack your things and live this house ba zan zauna da stubborn child irin ki ba, na gaji da halayenki ki koma gidan Didin da take d aure miki wani waje, and mind you don t ever come close to this house again Bata fasa cin abincin ba kamar yarda Tsawar Dadan da hargaginsa basu wani firgita ba.. Ta kwashi plate d in abincin duk da ba ci zata yi ba don ta k ular da Dadan da matarsa ne. Ta saki murmushi cikin wata murya da ta bayyana tsantsar rashin jinta ta furta Thankyou Dada am leaving Ta wuce cikin corridor da zai kai ta d akinsu. Ba Imani ba harta Dada da Mommy kallon mamaki suka bita da shi. Mommy ta ciji leb enta tana kallon Dada ta furta You see, kaga yarda ta raina mutane ko? Wallahi ku kuke k yaleta Ai inaga wata rana kai ma zata ce zata dukeka Bai kulata ba sai dai yanayin fuskarsa kawai zaka kalla ka san ransa ya yi k ololuwar b aci. Imani jiki ba laka ta mik e ta bi bayan y ar uwarta hankalinta a tashe tana tunanin menene akan Amanin da yau rashin kunyarta ta zo kan Dada mutumin da mutane da dama suke jin shakkar ha da ido da shi, ji fa abinda ta masa Kuma ko a jikinta JIKAR NASHE HADARIN GABAS NAZEEFAH SABO NASHE. 08033748387. Bai kula duk surutan da Mommy take masa ba ya ci gaba da cin abincinsa hankalinsa kwance, duk da a k asan ransa wani irin b acin rai ne yake fisgar zuciyarsa don har yana jin kamar suya a cikin zuciyar tasa. Mommy ta k araci mitarta ta mik e ta shige part d inta tana fa din gantalallun yara kawai! Dada wani irin kallo ya bita da shi kallon da yake bayyana alamun garga dinsa gareta. Ya girgiza kai sau tari ba ya magana sai dai ta idanu hakan ya zame masa jiki ga duk wanda ya san shi kuma ya san shi akan irin wannan halayyar. A ransa ya sake maimaita kalmar gantalallun yana jin b acin rai ya cije bakinsa a hankali ya furta you will explain clearly. Ya mik e yana goge hannunsa da hand towel bayan ya wanke hannun duk da ba da hannun ya ci abinci ba. Kansa tsaye ya nufi d akin su. Yana jin duk hukuncin da zai yiwa Amani ba zai gamsar da shi ba idan ba mugun duka ya mata ba. Yarinyar tana da taurin kai da kunnen k ashi a wannan halayyar sun yi ban ban da y ar uwarta. Imani na zaune saman sallaya ta idar da sallahr walaha kenan da Alk ani a hannunta. Dahda ya tura k ofar d akin da k arar k ofar ya saka zuciyar Imani bugawa. Amani kuwa ba abinda ya dameta irin mayataccen k amshin turarensa da yake tuna mata wancan yanayin na cikin mafarkinta. Fuskarsa a ha de ya shigo d akin idanunsa a kan Imani ya ce fita Parlour Imani, and what ever da zaki ji ya faru don t try open this door Imani idanunta ya kawo ruwa ta yi raurau tana kallonsa zuciyarta