Sashe 43
Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
su Amanin kallonta kawai suke. Har Moddi Ya k arasa gabanta yana murmushi ya ce Akwai sauran shiri ko? Ya fa da k asa k asa sai kuma ya girgiza kai Kin shigo kenan Safna. Idan kuma kika fita nan da kwanaki masu yawa ma ba tare da izinina ba, ina tabbatar miki a bakin aurenki. Ta ji wata irin hajijiya tana neman kada ita. Tana kallon su Amani suka bi bayansa Amanin na sakin dariya k asa-k asa. Sai da ta dafa bango tsabar yarda taji ana wujijjigata kada fa mafarkinta ya tabbata kada wannan gidan ya zame mata BAK IN GIDA ganin Sun mata nisa yasa da sauri ta mik e ta bi bayansu. Tana aikin turawa Malaminta Message. Hannunta duk rawa yake a haka ta isa babbar k ofar da taga sun shiga. Inda anan babban parlorn da ya raba sassan su da na Didi yake. Didin na zaune a saman kujera su Umma Tee zagaye da ita. Amani da sauri ta fa da jikin Umma Tee d in. Duk murna ta gama bayyana a saman fuskokinsu. Suka d ago suna kallon Safna da yake tsaye kamar ruwa ya ci ta. Sai fidgeting yatsunta take. Didi ta saki wani murmushi tana furta Maraba lale, shigo mana Safna. Wani abu ya dunk ule mata a zuciya sai kawai ta juya da sauri ta nufi d aya k ofar da ta tabbatar nan ne part d inta. A zafafe ta mayar da k ofar ta kulle tana sakin huci da wani irin Zare ido. A tsorace take ta tsorata da komai ma, idan ba kallon tsoro ta yiwa Moddi ba, sai taga kamar kallon tsana yake mata. Da wani irin hanzari ta fara kiran wayar Malamin nata. Bugu guda ya d aga don shima yaga message d inta. Safna kada ki shiga gidan nan, idan kika shiga komai ma zai iya faruwa, idan na ce komai ina nufin komai, kada ki shiga Safna ta runtse ido tana furta Na shiga Malam, Na shiga ka gaya min ba abinda zai faru Daga d aya gefen Malam ya ce Akwai Matsala, idan zai yiwu ki fito yanzu tun kafin abinda ake gudu ya faru Malam ba zai yiwu na fito ba, ya ce idan na fito a bakin aure na Muryarta ta tsaya cak ganin Moddi a tsaye a gabanta yanayinsa ya nuna ya ji duk abinda ta ce. Don kallonta yake da birkitattun idanunsa da suka bayyana tsananin fitinarsa da rashin mutuncinsa, kamar kallon farko da ya fara yi mata sanda suka fara ha duwa. Hantar cikinta ta ka JIKAR NASHE HADARIN GABAS NAZEEFAH SABO NASHE 08033748387. BRIGHT PENS 2nd batch.. Da wa kike waya? Ya yi amfani da bu daddiyar murya wajen tambayarta. Murya bata mata kama da ta Moddinta da ta sani ba, wani ne wannan daban, da ya jirkita zuwa wata halitta mai furgutarwa gareta. Bata tab a ganinsa a wannan yanayin ba don haka razanar da ta shiga ba ka dan ba ce. A fusacen Ya sake cewa Ba kya ji ne? Ki yi magana mana . Ko sai na bayyana Miki wanene ni? Ta ha diye wani yawu sannan cikin muryar da ta bayyana rashin gaskiyarta zalla ta furta Da k awata nake fa, da wa zan yi waya. arya kike. Ya fa da direct yana kallon cikin idonta. Wata irin tsanarta yake ji a ransa. Ta sake tsorata da yanayinsa don gani take zai iya kai mata duka. Ka yiwa girman Allah ka kyaleni Imam me na yi maka ne? Cije leb ensa ya yi sai kuma ya wancakalar da ita gefe yana jin idan har ya cigaba da tsayawa kusa da ita zai iya zama ajalinta, a yarda yake jin zuciyarsa na wani irin zafi . Da wani irin sassarfa ya fita daga d akin. Sai sannan Safna ta ja ajiyar numfashi ta shak i iska. Kafin ta furzar da huci. Wani irin zafi take ji a ranta. Ita yau Imaam ya yiwa haka? Ta cije bakinta wasu hawaye da ta tabbatar na bak in ciki ne suka zubo mata. Ta zauna tallafa da kumatunta tana jin tunanin da yake cikin zuciyarta shine kawai abinda ya kamata ta yi. Ba dai burin y an uwan Moddibo su tozarta ta ba, burinsu ya yi aure ya haihu zata biyo musu ta yarda suke so. Wannan hawayen ta rantse ba zata zubar da su a banza ba. Da wani irin zafin nama ta shiga kiran Lady boss. Bata wani b oye mata komai ba, ta zayyano mata abinda ke faruwa. Cikin mamaki Lady Boss ta furta Kan Uba! Shi Imaam D in ne ya aikata miki haka? To me ya shiga kansa? Rashin mutunci, ko na ce Uwarsa da y an uwansa suma sun je sun yi nasu k ulunboton to wallahi wannan karan na shirya musu zan tabbatar musu ni gaba nake da su a iya shege, zan b ata musu sunan dangin da suke alfahari da shi, da ina jin ba zan iya aikata abinda Alwan ya saka ni ba, amma yanzu zuciyata tana jin zan iya fin haka ma, zan iya sakawa Moddi ya yi zina da Uwarsa ma ba y arsa ba. So nake na samu Makamin da zan hana shi aure. Na shirya wannan karan Lady Boss, kuma Didi ko da bala i sai na rabata da D an nata, sai ta gwammace bata ma haifeshi a duniya ba Lady Boss da take jin komai ta saki dariya ta ce Yanzu za ki iya kenan da kika ji Uwar bari, dama can ai ke kika saka tausayinsa a ranki da kishin ba kya son Ya kusanci wata matar. Idan banda haka Uwar me ye a cikin Uba ya yi zina da y ar sa, y ar ma da ba taki ba, y ar da ba kya so. Ai ko da Uwarsa aka ce ya yi Ban zata za ki yi wannan da dewar baki aikata ba. Riba biyu fa kenan ga ku di ga b ata masa suna. Safna ta ja ajiyar zuciya tana furta Ki jira nan da kwanaki ka dan za ki ji dadda dan labari, zan saka zur ar Lamid o a cikin Bak ar rayuwa, da sai sun gwammace ba su takale ni da fa Bana jin ki, na San za ki iya. Lady Boss ta fa da. Safna ta Zare wayar kafin ta sake mayar da kiran kan Malaminta. Ya tabbatar mata zai yi aikin da take so, zai kuma aiko mata da kayan aikin ta birne a cikin gidan inda kowa ba zai ganta ba. Amma ta tabbatar a sanda zata yi aikin kowa na barci cikin tsakiyar dare. Ba shakka ba komai ta ce ta amince Da tafiyar sassarfa Ya koma sashen Didin, inda ya bar y an uwansa. Yau kam zuciyarsa fresh yake jinta, cikin tarin soyayya da k aunar y an uwansa. Kamar wani labulai ne aka yaye a cikin zuciyarsa ya bu de idonsa daga duhun da ya mamaye ganinsa. Ya dinga Jin abubuwan da Ya aikata bai kyauta ba. Jikinsa a sanyaye ya zauna daf da Didi da Kan Amani yake samanta. Tana sosa mata gashin. Idanun Amanin a lumshe tana shak ar k amshin Dahdan. Zan yi magana da ku, yaran nan su bani waje. Moddi ya fa da cikin wata irin Husky Voice da take d auke da karyewar harshe mai da din sauraro. Duk yaran wajen suka mik e, banda Amani da ta yi kamar barci take. Ta gefen ido ya kalleta kafin ya furta Ke ba zaki tashi ba ne? Don ya san sarai ba barci take ba. Idonta ta sake lumshewa sai kuma ta mik e daga jikin Didin ta tafi cikin d akunan da suka kasance nasu. Moddi sai da ya ji rufe k ofarta sannan ya mayar da kallonsa kan y an uwansa. Da ku zan fara, Don Allah idan da Wanda yake rik e da ni a ransa ya yi min uziri Ya yafe min.. Ba Wanda bai zuba masa ido a wajen ba cikin wani irin tsananin farin cikin dawowar d an uwansu cikin hayyacinsa. Didi kuwa murmushi take saki hannunta cikin na Moddi da ya damk e sosai. Tana jin yarda jikin nasa yake rawa. Mun yafe maka. Shine abinda suka dinga fa da. Sai kuma ya zube a gaban Didi. Ya kama hannayenta kasa furta komai ya yi sai hawaye da ya fara zuba sharrr daga idonsa. Didi ta kama shi tana girgiza maka kai. Ban tab a rik e ka da komai ba Moddi, na yafe maka abinda na San ka aikata da Wanda ban sani ba Na amince Didi zan yi aure, zan auri duk matar da kike son na aura na amince ko gobe ki d aura min aure zallar farin cikin da zuciyar Didi take ciki ta kasa b uya a saman fuskarta kawai sai ta rungume Moddin a jikinta tana furta Barakallahu fika Moddibo, Allahu Akbar Allah ka nuna min girmanka, ka nuna min komai yana faruwa ne cikin buwaya da izzarka tabbas kai Alhakimu ne mai yawan hikima ka cancanci a kiraka Alwahhabu mai kyauta da k ari. Almujibu mai amsar addu ar bayansa. La Sharika laka, Allah ka cigaba da kare min zuri ata. Ba ni da boka bani da Malam. Ameen suka amsa gaba d aya Umma dee ce kawai bata wajen. Moddibo ya d an saki murmushi kawai kafin ya mik e ya bar parlorn. Shikkenan hirar ta koma kan kalar matar da ya kamata su samowa Moddibo kowa ya dinga fa dar albarkacin bakinsa. Na irin matar da ta dace da Moddin. Driving d in take idanunta sanye da black shade da ya yi masifar yi mata kyau, ya kuma sake bayyana gayunta. Chewingum take ci. Fuskarta cike take da damuwa. Ta samu gefen Titi ta yi parking hannunta ta saka ta Zare shades D in da ya saka ba a ganin jan idanunta suka yi. Muryarta a dashe ta ce Alwan ka kasa cika min buri na, me yasa? Da Kai na yarda duk wani hope d ina yana wajenka. Ka San dai rashin cikar burina yana nufin komai ko? Alwan ya saki ajiyar zuciya ransa a b ace ya fara furzar da huci shi kansa zuciyarsa