← Book details Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 57

Sashe 28

Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

d in bai d aga waya ba ya saki tsaki ya yi cilli da wayar. A lokacin kamata ya yi ya mik e ya Yi sallah sai dai ya kasa. Hannu kawai ya saka cikin sumar kansa yana yamutsawa a hankali. A safiyar ranar da al amarin zai faru. Safna..ta ziyarci wani Daji a Bidda da ke jihar Neja. .. Motar su tana tsayawa a k aramin Dajin Safna ta saki ajiyar zuciya tana jin tazo inda duk wata buk atarta zata biya. Boss lady dai kallonta take tana sake jaddada mata Ki nutsu Safna ki gaya masa duk abinda kike so, wallahi aikinsa kamar yankan wuk a ne. Ta d aga kai Dole ma ai, nifa naga abinda na gani k awa. Tsawa fa Moddi yake min kamar ba wanda da yake tsoro na ba. Ba ma wannan ba, ni yanzu burina na cikawa Alwan buk atarsa ko na samu ya zube min manyan ku din da ya alk awarta min. Idan har na samu haka wallahi Boss lady ni da duk wani nawa mun yi hannun riga da talauci. Tunda suka shiga wajen suke jin tsigar jikinsu na tashi sabida wasu irin abubuwa da suka dinga karo da su a bukkar. Sun kusan minti biyu zaune kafin matar ta dago da jajayen idonta tana kallonsu. Mun san Me ke tafe da ke Kin yi wani kuskure a rayuwarki, da baki zo nan ba ina tabbatar miki komai zai iya faruwa Kin amince da ya yi arziki duk da duhun da aka ce miki an gani a k arshen arzikin nasa .Me kike so a yi? Safna ta ha diye wani yawu mai kauri ta furta Burina kawai a mallaka min shi mallaka ta har abada .kuma ina son na haihu da shi abin ya fara damuna Ba zaki haihu da shi ba har abada! Bokanyar ta fa da da k arfin gaske. Za mu mallaka miki shi irin mallakar da kike so sai dai mahaifiyarsa a tsaye take a kansa sai kin yi takatsantsan. Haka Bokanyar ta zauna ta ha da mata duk wasu surkulle ta bata tana jaddada mata yarda zata yi amfani da su. Kada a samu kuskure! Safna ta gya da kai. Sai yaransa ina son a raba shi da su ya ji ya tsanesu Bokanyar ta buga wani abu da sauri ta wurgar ta furta Ba zamu yi aiki akan haka ba an garga demu ku tashi ku bamu waje Safna yawu ta ha diye da k yar me yasa duk bokan da ta je masa da son irin wannan aikin sai ya ce ba zai iya ba. Ni dai ki taimaka ko karuwai ku mayar da su sannan ina son a Azalzala soyayyar junansu a tsakanin Amani da Moddibo har su kusanci junansu na cika burin Alwan, ko nima Nawa burin zai cika, duk Inda na je har yanzu ban samu Cikar burina ba. Wani kallo Bokanyar ta mata tana furta Wannan an gama, ki je zaki ga abinda zai faru Safna ta mik e jikinta na rawa duk da farin cikin da yake cin ranta sai ta ji tsoro da fargaba kuma sun shigeta. ta furta a ranta Duk bala i sai na mayar da yaran nan karuwai ko ta halin k a kuwa, tunda ni ba zan haihu ba gwara kowa ma ya rasa. Ai Hajjan ba zata yi alfahari da karuwan jikoki ba. Musamman a ce Uba ne ya kusanci y arsa, ya aikata zina da ita, kuma ita zan saka ta yi ta bibiyarsa.Ta fa da a ranta tana cije leb enta. Boss lady ta kalleta Lamarin yaran nan abin mamaki. Me yasa duk cikar bokaye basa iya aiki a kansu, sai yanzu burinmu zai cika. Safna lumshe idonta ta yi tana furta Da sannu zan samu inda zaa min wannan aikin, don na sha alwashin in dai ina raye sai na mayar da su karuwai musamman Amani Ina bayanki wallahi, ni kaina na tsani shegiyar yarinyar nan, ga kyan tsiya kamar ita ta k era kanta A haka suka koma gida suna ta aikata mugun abin su. Tana zuwa gida kuma ta aikata duk abinda Bokanyar ta ce, sannan ta fara shirin komawa gidanta cikin farin ciki da tunanin yarda zata juya Moddibo Da safe basu tashi da wuri ba, dalilin rashin samun isashshen barci da ba su yi ba. Har Mama Talatu ta gaji ta shiga d akin nasu wajen k arfe 11:30 don ta tashe su. Iman ta bu de ido da k yar ita ta fara tashi sannan Amanin. Mama Talatu tana kallonsu ta furta Ku kuwa yau lafiya kuke? Ku baku tashi ba shima mai gidan har yau bai fito ba? Iman bata yi magana ba sai shiga toilet da ta yi. Amani Kuma ta d an rik e kanta tana jin a yau dai kam kunya ba zata barta ta fita ta ga Dahda ba. Mama Talatu ta ce Amma dai Magajiya baki da lafiya ko? aga mata kai kawai ta yi. Ko da na ji, don ga idonki nan ya nuna haka, Allah ya baki lafiya ki yi wanka sai na kawo miki abincin karyawarki cikin d aga mata kai ta yi don bata jin yau zata iya fita su yi ido biyu da Dahda. Dahdan yana zaune a parlor Iman ta fito cikin shigar casual shirt. Ta durk usa ta gaishe shi daga gefe. Ya amsa mata yana sipping hot coffee a hankali, idanunsa akan Laptop d insa ya furta Amani fa? How is she feeling? Iman kanta kunyar Dahdan take ji ta furta Da sauk Ki tasota ta sha tea, idan kun gama shan tea d in kuma zan yi meeting da ku.. Iman kanta sai da ta ji fa duwar gaba. Ya d ago yana kallonta ya ji dalilin shirunta. Ki je mana.. Da sauri ta mik e har tana yi kamar ta kifa ta tafi da sauri wajen kiran Amanin. A zaune Amanin take ta tafka Uban tagumi, tunani ne kawai ya cika mata kwanya irin tunanin da idan kana yin sa kake jin kamar kwanyarka zata tarwatse.. Ki zo in ji Dahda.. Sai da cikinta ya wuntsila tsabar shiga firgici ta dago da k yar ta furta Ki ce ina barci.. ragowar maganar ta mak ale mata ganin Dahdan a tsaye a bakin k ofar ya rungume hannunsa a k irji. Tun kafin ya yi magana ta mik e da sauri tana fidgeting yatsunta. Ido kawai ya k ura mata ya juya ya fita daga d akin. Amani bata san ta saka Hijab ba tsabar razana ta bi bayansu da sauri tana jin kamar zata fa di sabida yarda k afarta take har dewa. Dinning ya nuna mata bayan tazo ta tsaya masa a kai. Duk da idonsa a lumshe yake ta san me yake nufi ta je ta ci abinci. Ba musu ta isa dinning d in.. Duk ta zama wani sukuku kamar ba Amani Uwar tsiwa ba. Cin abincin take kawai ba tare da tana banbance taste na zak i da gishiri ba. Ta dai samu ta caccakala ka dan ta kurb i ruwan tea d in. Kafin ta ajiye cup d in ta kifa kanta a saman dinning d in. Ku zo nan. in da Dahda ya ce ya k ara mata bugun zuciyatta. Ta ajiye ta mik e a hankali ta bi bayan Imaan. Suka zube a gabansa. Tsawon mintuna biyar yana danna wayarsa. Kafin ya dago Imaan ya fara kallo kafin ya mayar da kallonsa kan Amaan da gaba d aya bata da nutsuwa. Yana zagaye fuskarta da kallo yana tambayar Imaan d in. How long ta dauka tana kalar wannan mafarkin? Ba Amani ba hatta da Iman sai da tambayar ta razanata. Ya sake furta Are you dumb Amani? Ta girgiza kai Ta da de zai kai One year Ya mayar da kallonsa kan Imanin ya furta How is she react a cikin mafarkin Imaan ta ha diye wani yawu mai d acin gaske. Ta ja baki ta tsuke don wallahi ko me aDahda ya mata ba zata iya bu de baki ta gaya masa ba. Shi bai san jiyan ma mugun k ari ta yi wajen yakice kunyar ta yi ta gaya masa ba. Dahda ya mayar da kallonsa kan Amani da ta cukuikuye gefen mayafinta ta matse shi tsam a hannunta. Hakan ya nuna aure kuke so? Tunda kun fara irin wa dannan mafarkan? Imaan ta ware ido Amani kuwa ji ta yi zuciyarta ta daina bugun da ya kamata don Kallon da Dahdan yake mata jefa ta yake cikin wani irin yanayi. Na baku dama ku fitar da Miji nan da sati biyu, ku tashi ku tafi ku ba ni waje.. Imaan ta dan bu de ido Dahda karatun fa? An fasa.. Ya fa da yana lumshe ido ha de da murza goshinsa HADARIN GABAS NAZEEFAH SABO NASHE 08033748387. BRIGHT PENS... 2nd batch Zazzafar tafiya mai abin ban mamaki, tawayen jerin marubuta hu u a sabuwar tafiyar ta second batch. *HADARIN GABAS* Nazeefah Sabo Nashe ARFE A WUTA* Ayushercool *ZAYTOON* Zee kumurya *MUTALLAB* Nimcyluv Sarauta. Page 16. Ganin yarda yanayin launin idonsa ya sauya ne yasa suka San a duk maganganunsa ba wasa. Jikinsu a salub e suka mik e da niyyar barin wajen. Dadan ya bi su da kallo da lumsassun idanunsa kafin ya saki ajiyar zuciya. A zahiri ya furta Ya Ilahi! What is this? Tunda suka shiga d akin zama suka yi a gefen gado kowa zuciyarsa cike da tunani. Imani bata da fargabar aure don tuni zuciyarta ta aminta da Mus ab d an gidan Umma J.. Amani ce mai fargaba. Fargabar da ta kasa b uya a saman fuskarta ta dinga sakin huci a hankali k irjinta na wani irin bugu. Tabbas ta San wannan ranar zata zo ranar da zata auri wani ba Dada ba, Amma ta ya zata iya yakice bahagon tunanin soyayyar Dada a ranta. Abinda take ganinsa da kamar shirme sai dai a yanzu ta tabbatar da gaske son Dada take Imani ido ta bita da shi ganin yarda take zubar da hawaye idonta a lumshe ga k irjinta yana sama da k asa alamar sauyawar bugun zuciyarta. Cike da rauni ta dafa cinyarta tana furta Bata amsa ba
Chapter 28 · 0% Book details