← Book details Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 57

Sashe 19

Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

zubawa su Ama wannan abin su tafi da shi school? Idanu suka waro suna kallon juna. Tsawar da ya sake saki ne ya saka su saurin amsawa da rawar baki duk da Suna jin shakkar Safnan ba su fasa cewa Hajiya ce ta yi umarnin haka Ya juyo ya mata wani kallo da ya kusan sakata fitsari a wando. Bai yi magana ba illa cije leb ensa na k asa da ya yi ya fice yana jan hannun yaran. Zuciyarsa na wani irin tafarfasa shi ka dai ya san hukuncin da zai yiwa Safna idan ya koma gidan yana jin k arshen zamansu ne ya zo. Don ba zai laminci a dinga zaluntar masa yara ba Safna tana ganin ya fita ta juya tana kallon Mama Talatu da Laraba. Ta k unduma wani zagi kamar ba za su yi sa a da uwarta ba. Ni kuke son ku kashewa aure ko? Wallahil azeem k arshen zamanku a gidan nan ya zo Haka ta dinga zaginsu tana ci musu mutunci ba su ce mata komai ba. Sai dai zuciyarsu fal take da murnar tonuwar asirinta yau. Don kam Safna muguwa ce ta bugawa a jarida ba irin azabar da bata bawa yaran Allah ne ka dai ya yi da kwanansu a gaba. Sau tari daga su har yaran ba sa sake cin wani abinci bayan wanda Zata basu da rana sai kuma garin Allah ya waye. Haka suna ji suna gani za su yi ta jin k amshin abu amma haramiyarsu. Ko idan Babansu ya kawo abu zai sa ta d iba ta bi su k aramin parlorn da suke zama a tsakar gida da daddare ta shiga da kayan da din ta ajiye ta ce kuma duk wanda ya ci sai ya ha du da fushinta. Wani lokacin Amani ce duk hanata da zasu yi sai ta ci tun bata iya k uni har ta fara sakarwa Mommyn k uni kuma duk abinda zata mata ba zata yi kuka ba, sai dai ta yi ta cizon leb enta tana huci kamar yarda ta ga Dahdansu yana yi. Har tsarki da ruwan borkono ta tab a yiwa Amani ranar ba su yi barciba kuma duk kukan yarinyar ta hanasu su gayawa Ubanta kai muguntar Safna garesu ba zata k irgu ba.. idan suka yi nufin gayawa Hajja sai su ji kamar an k ulle musu baki sun kasa Suna kallonta ta shiga d aki ta saka Hijab ta fito rik e da jaka. Bata ko kallesu ba ta fice daga gidan. Suma ba su damu ba don sun san ta saba fita idan baya nan don haka ba wani sabon abu bane a wajensu suka saki ajiyar zuciya a fili suka fara tsine mata da son Allah ya tona mata asiri komai daren da dewa Yana fita ya biya super market ya siya musu kayayyakin da di da yawa sannan ya sauke su a makarantar da suke zuwa. Irin private school d innan ce mai sauk in ku di.. Suna sauka a machine d in Amani da bata shiru da bakinta ta kalleshi Dahda kullum zaka dinga bamu k wai da shayi mai madara ka siyo mana kayan da di mu je da su makaranta?y an ajinmu duka da kayan da di suke zuwa, ba da tuwo da kwaki ba. Imaam sai da ya yi da gaske sannan ya amsa mata saboda yarda wata k walla ta fara zubo masa Zan muku duk abinda kuke so Ama ya fa da yana sumbatar gefen kumatunsu. Ya rungume su sannan suka shiga aji. Yau zuciyarsu fal nisha di ba rashin walwalar nan da suke zuwa da shi makaranta. Imaam ya bi bayansu da kallo yana share k wallar da take zuba a idonsa, ya furta Allah ka yafe min cikin raunin murya don sai ya tattara laifin gaba d aya ya d ora a kansa yana ganin koma me ya faru laifinsa ne da baya bincika halin da yaran suke ciki musamman sanin da ya yi basu da mahaifiya. Kai tsaye zuciyarsa ta ba shi shawarar ya mayar da yaran nasa gidan Hajja hankalinsa zai fi kwanciya. HADARIN GABAS NAZEEFAH SABO NASHE 08033748387.
Chapter 19 · 0% Book details