Sashe 47
Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gani jiya ke kika jawowa kan ki, shi yasa idan mutum ya ce abinsa sirri ne baya son a gani, yana da kyau ka janye hankalinka daga kansa, Saboda baka San me zaka je ka gani ba, yanzu da kika ga abinda ba a so ki gani in ga situation d in da kika jefa kanki nan, so are you happy? Daga haka ya koma ya zauna yana cigaba da kallonta, da kallon yarda hannunta yake rawa wajen bu de enveloped D in. Hoto ne da wasu takardu. Hoton jarirai ne guda biyu rungume a hannunsa yana nunawa Mahmeeynsu gefe guda kuma Didi ce da Umma T. Fara ar fuskarsu ta kasa b uya. Y ar riga murmushi kawai take idanunta akan jariran da y ar k walla a gefen idon nata. Ta San hoton don haka ba bak o bane a wajenta. Takardar ta tsirawa ido tana kallon sunan mahaifiyarsu a jiki da ranar da aka haifesu. Sai kawai ta lumshe ido hawayenta na cigaba da sauka. Dahdah shiru ya yi yana jin wani rauni a zuciyarsa, yarda yake jin zafin zubar hawayenta daidai yake da d igar dalma a jikinsa. Enough Ama Ya furta cikin wata irin silent voice da take fita da wani irin magana disu da yasa dole Amani ta bu de idanunta ta zube su a kansa aga mata kai ya yi kafin Ya saka handky in hannunsa yana share mata hawaye. Zuciyarta ce ta dinga bugu madadin samun sauk i a ranta sai ta dinga jin wani irin yanayi. A firgice ta farka daga mafarkinta ta kuma ture hannun Dadan kafin ta mik e da sauri, ta yi hanyar fita daga sashen nasa, sam bata ganin gabanta Ya da de zaune a wajen bayan ya janye idonsa daga kallon Amanin da ta fice a firgice. Ya sauke ajiyar zuciya yana murzar goshinsa. Yarda yake murza goshin ji yake kamar yana tafiya ne da tarin damuwarsa. Wani irin sanyi ya dinga bin sassan jikinsa. Nauyin da zuciyarsa ya yi ya dinga sauk e. A hankali yake sauke ajiyar zuciya. Da gaske ya samu hanyar warwarar matsalarsa Amma ta yaya? Ta Yaya zai amsa tarin tambayoyin da ya hango a idon Imaan da Amani .. a hankali ya mik e yana zagaye d akin ya san Imaan ta ji shi a wayar da yake magana, a idonta ya hango jin firgicin maganarsa, sai dai bata tsaya ba, bata tsaya ya yi mata bayani ba, duk da shi kansa bai San kalar bayanin da zai mata Har kwanyarta ta dauka ba. Don haka shirun shine yafi gwara ya ja bakinsa ya yi shiru kawai. Ya san shi mai laifi ne a wajen yaransa, laifin da yake tunanin ba abinda zai goge shi, a idonsu yake hango tsanarsa lokaci guda kuma a idon nasu dai yake hango tarin k aunarsa, da tausayinsa. Da gaske shi abin tausayi ne, Safna ta mayar da rayuwarsa akan irin tafarkin da take so, Ya amince ta yi winning a kansa Cikin sanyin jiki ya koma sashen Didi. Rarraba ido yake a cikin tarin y an uwansa ko zai hango y ansa. Sai dai Babu su ba alamarsu. Ba wanda ya lura da halin da yake ciki. Don murna da zakwa din aurensa da suke yi. Ya d an tab e baki kafin ya zauna a daf Didin. Da jarumta sosai a muryarsa don son ya kawar da yanayin damuwar da yake ciki ya yi magana. Kun cika gidan nan da hayaniya, and kun sani bana son hayaniya why all the noises don Allah ku tattara ku tafi, I need privacy ina son magana da Didi Dukkansu da suke wajen sai da zuciyarsu ta buga. Basa son komai zai gayawa Didin ya ce Ya fasa auren, zuciyar Didi ba zata d auka ba zai raunata mata zuciya. Ba tun yau ake nema Masa aure yake fasawa ba. Didi ma kallonsa take tata zuciyar tafi ta yaran nata bugawa bata manta wani lokaci data nema masa auren ba, a ranar auren bayan an d aura ya gudu bayan ya yiwa matar saki guda. Don haka ta dinga kallonsa, kallon da Har sai da Ya saka ya yi k asa da kansa, a hankali ya furta Ba zan fasa ba Didi, ba abinda kike tunani bane. Sai ta sauke ajiyar zuciya kafin wani murmushi ya bayyana a fuskarta. Da gaske ta San wannan karan Moddi ba zai watsa mata k asa a ido ba.. hankalinta ya kwanta, ta dinga kallon su Fateema da suke tattara kayansu da na yaransu suna mata sallama. Idonsa a lumshe yake, sam hankalinsa baya kansu yana can wata duniya da Ya yi zurfi a cikin tunaninta sai da Fateemah ta dafa shi ta an yi magana da k arfi a kunnensa. Kiddo mun tafi, saura kuma ka je ka gayawa Safna k anwar Didi zaka yi aure.. Bai bu de idon ba, balle ya bata amsa, alamun y an miskilancin na kusa, idan yaso haka yake sai ya cije ya k i magana musamman idan zuciyarsa bata cikin sukunin yin Maganar. Shafa gefen kumatunsa ta yi, sai kuma ta Ja hancinsa tana furta To Uban miskilanci, saduwar alheri. Ya d an murmusa kawai ba tare da ya bu de idonsa ba. Ya furta Akwai sak o a account d inki, share it with Your sister Ta k asan ido yake kallonsu duk suna ficewa Har ta kai k ofa ta tuna bata yi sallama da su Amani ba. Sai kawai ta dawo zuwa dakinsu na b angaren Didin. Jin kamar suna magana k asa k asa yasa ta tsaya ta lab e tana jin su. Iman ta ce Sha biyu na dare za mu gudu, idan yaso ko garin su Mahmeey sai mu je. Fateemah ta waro ido, kafin ta tura k ofar ta shiga da sauri suka ago suna kallonta sai kuma suka sunkuyar da kai. Akwatin gaban Imaan ta kalla sai kuma ta kallesu d aya bayan d aya gabanta na fa duwa ta furta Guduwa za ku yi? asa suka yi da kansu. Jikin Fateemahn a sanyaye ta zauna daf da su. Nasiha ta dinga musu da alk awarin ba abinda zai faru In sha Allah. Moddi ba mahaukaci bane, na San ko giyar wake ya sha ba zai aikata muku komai ba. Imaan tana hawaye ta labarta mata komai. Wani irin waro ido ta yi a gigice ta mik e ta koma parlorn Didin, da wani irin duba take kallon Moddi Kfin ta furta Imaam kana cikin hankalinka kuwa? Didi kin san abinda yake shirin aikatawa? Da sauri Ya kalleta a idanunta Ya hango da gaske abinda duk ta sani zata gayawa Didi, Ya runtse idonsa kawai Free pages Saura few pages fa! Ku hanzarta samba do ku dinku. 2118666253 UBA JIKAR NASHE HADARIN GABAS NAZEEFAH SABO NASHE 08033748387. BRIGHT PENS SECOND BATCH Idanu ya sake warewa ganin Fateemah har ta fice daga parlorn ba tare da ya san me suke tattaunawa ba. Ya sake lumshe idonsa ganin Didin kawai ta zuba masa ido, sai yaga kuma ta mik e ta nufi d akin da su Amanin suke. Tura k ofar ta yi jikinta a sanyaye ta zuba musu ido. Su in ma kallonta suke. Ta zauna a gefen gadon tana kallon akwatinansu sai ta saki murmushi kawai, murmushin da su Amani suka dauka na mamakin abinda zasu aikata ne. Za ku gudu saboda Didi ta Gaza a wajen baku kulawa ko? Za ku gudu saboda k una tunanin zan iya bari a cutar da ku ko ni na cutar da ku ko? Sai ta girgiza kai ta furta In dai ina raye ku saka a ranku ba abinda zan bari ya cutar da ku, ina son ku ina tausayin maraicinku.. ku k ara min lokaci komai yazo k arshe, na san kuna da matsala Fatima ta gaya min komai, ina kuma kan bincike akan abin duk Wanda yake da saka hannu a ciki Allah zai yi maganinsa. Komai yazo k arshe Moddibo zai yi aure jibi, da matar da nake tunanin ita zata zame masa alheri a rayuwarsa, matar da zata so ku taso mu ta kuma sake dunk ule zumuncinku waje daya. Farin ciki ya cika zuciyarsu gaba d aya suna jin a ransu kamar da gaske duk wata matsalarsu ta zo k arshe. Kada ku k ullaci Babanku, bashi da laifi ko ka dan son zuciya ne ya shigo cikin lamarin ku yi hak uri kun ji. A wannan gab ar dai Imaan ta jita kawai ba don ta yarda da abinda ta ce ba, saboda da kunnuwanta ta ji abinda Dadan yake fa da a waya. Sai kawai ta ja ajiyar numfashi ta sauke tana kallon idon Didin da itama ta zuba mata ido, tana son ta gayawa Didin komai sai dai bata San ta inda zata fara ba, maganar ta girmi kwanyarta. Didi ta shafe kansu ta sake fita. Iman kallon Amani take da idonta suke lunshe sai kawai ta samu kanta da Shafa gefen fuskarta Amanin ta Ware ido tana kallonta a hankali ta furta Menene? Amanin ta girgiza kai kafin ta furta Bakomai. Duk da akwai komai din wani irin zafi take ji a zuciyarta Wanda ta tabbatar na Kishin Dada ne, sai dai tana fatan aurensa ya zama silar yayewar matsalarta. Haka aka dinga shirin biki gadan gadan ba tare da Sun bari Safna ta sani ba. Sai dai a ranar ta fahimci abinda ake shirin aikatawa don da tashin hankalin da take ciki yasa bata Saka ido a kan mutanen gidan ba, mafita kawai take nema. Mafitar da zata wargaza kwanciyar hankalin zuri ar Lami do ta saka musu firgici da b acin ran da ba zasu tab a mantawa da shi ba. A zaune take gefen gado hannunta rik e da robar rubutu ta tsurawa rubutun ido tana d an murmushi k asa k asa. A hankali ta furta Da gaske komai yazo k arshe kamar yarda Malam ya ce.. Sai kawai ta saki wata irin mahaukaciyar dariya daidai lokacin wayarta ta dinga ringing ido ta zubawa wayar tana jin wani irin matsananciyar fa duwar gaba. Hannu na rawa ta saka ta au wayar ganin sunan Alwan da ya bayyana b aro-b aro a screen in