Sashe 42
Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba sai gidan su Safna. Tunda ta fito ya ji zuciyarsa ta yi wani irin sanyi. Fa dan ma da ya yi niyyar zuba mata ya ji ya kasa. Wani irin soyayyarta mai zafi ce take fisgarsa. Murmushi ta sakar masa ha de da turo bakinta alamar kiss sai kuma ta hau waige waige ganin ba kowa sai kawai ta yi saurin rungumarsa tana ja baya ta furta I missed you dear, kawai kuma sai ka guje ni bayan ka gama jiyar da ni da dinka. arfin hali ya yi ya tattaro dukkan nutsuwarsa ya gyara zamansa yana fuskantarta. Cikin muryar da ta bayyana rashin wasa ya ce Safna Why? Me yasa kika aikata abinda kika aikata? Gira guda ta d aga masa sai kuma ta saki murmushi tana furta Me na aikata Dear? Ya sake tsare girarsa sosai kafin ya ce Vedion da kika turawa Tee, a ina ma kika samu numberrta? Sai da ta yi dariya mai ha de da shashshek a sannan ta yi k asa da murya tana furta A duniya na samu Imaam, na ga idan ba haka na yi ba shirin gudu kake ka bar ni, ni kuma na shirya aurenka duk da ina ji a girme na girmeka da shekara guda, amma haka zan aureka don ina son ka, ka yi min kai ne maha dina. Na San dai zan sha fama a gida kafin a amince na aureta Amma na amince zan d au duk wani challenges matuk ar zan cika buri na Kallonta kawai yake kafin ya saki ajiyar zuciya har ta gama zubar ta sannan ta ago tana kallonsa. Ka amince za ka aure ni? Ta fa da tana Kama hannunsa. Wani irin lumshe ido ya yi bai San sanda ya d aga kai ba. Yana furta Sure.. wani irin ihu Safna ta saka bata San sanda ta kai masa Sumbata a baki ba tana furta Yes wo . Na San dole ma zaka amince. Sai da ya au hanyar gida sannan ya dinga Jin kamar shawarar da ya yanke na amincewa Auren ta bai dace ba. Kamar ya yi azarb i don wannan hurumin Didi ne. Amma sai ya samu kansa da rashin ganin kuskurensa. Hakan ne ya dace. Safna ce zab insa ita kuma ta dace da tsarin rayuwarsa Sai dai bai san me su Didi suke shiryawa ba. A safiyar ranar Didi ta shigo d akinsa hannunta d auke da dakakkiyar shadda fara k al. Babbar riga da y ar ciki da suka sha aikin har da hula da takalmi sababbi. Ta mik a masa tana kallonsa. Tashi maza, ga ruwan wanka can Fatima ta saka maka a ban daki. Da sauri ya dubeta yana kallon kayan hannunta. Ina zamu Didi? Unguwa. Ta furta masa kanta tsaye. Ganin fuskarta ba yanayin wasa yasa ya mik e ya nufi toilet d in. Mamaki ya Kama shi ganin y an uwansa duka cike a gidan su da yaransu. Ya tab e baki yana tunanin taron na menene ake yi? Wankan ya yi ya kuma shirya tsaf cikin babbar rigar da ta masa kyau sosai ta sake fito da k imarsa ta namiji cikakke duk da yarintar fuskarsa bata b uya ba. Yana fitowa suka saka masa gu da a Kai. Ma sha Allah ka ga angon y ar riga. Allah ya tabbatar da alheri yasa a ce gwara da aka yi Cak ya tsaya da numfashinsa yana zubawa Jay ido cikin wani irin firgita ya ce ar riga kuma? Eeh, Y ar riga In sha Allahu yau za aura muku aure da ita, ita ta dace da kai. Na tabbata ba zata raina abinda Allah ya bamu ba Zuciyarsa ta dinga wani irin bugu Yanzun ma bugun zuciyar tasa take yi. Musamman da Didi ta ora hannunta a saman kafa darsa hakan yasa ya dawo daga tunanin da ya lula. Ya bu de idanunsa da suke fitar da maik on hawaye yana kallon Didin. Itama kallonsa take. Tana furta Tunanin me kake Moddi? Ya ja ajiyar zuciya kafin ya girgiza Kai ya ce Komai ma Didi. Didi ta jinjina Kai kawai kafin ta mayar da hoton y ar riga ta ajiye tana dubansa ta furta Goben dai da wuri zaka kawo su Magajiya ko? Don Sam bana son zaman ka daita. Sannan ina son ka fita ka samo almajirai da zasu kwana suna saukar kur ani a gidan nan. Don na lura sosai Moddi lamarinka sai na dage da addu Ya jinjina Kai yana furta a samo Didi. Cikin muryarsa take Jin wani irin weakness. Ya mik e ya fita daga d akin a hankali. Zuciyarsa kuwa tunanin y ar riga ne kawai a cikinta. Yana fatan Allah yasa bata tafi da Jin haushinsa a ranta ba. Da Kansa ya saka a samo Malamai ya kuma bi shawarar Didi bai gayawa Safna zancen tashin ba, sai a kashegarin ranar. A d akinta ya sameta fitowarta daga wanka kenan tana Shafa mai. Ya bita da kallo yana mamakin wata irin k iba da take sake yi Sam bata controlling jikinta. Ta daga Kai tana kallonsa kafin ta ja mayafinta ta rufe jikinta don ita kanta ba zata so ya ganta ba kaya ba. Gaba d aya halittunta sun canja. Gefen gado ya samu ya zauna kafin ya sauke idonsa kan ta ya furta Ki shirya za mu unguwa. Ta saki murmushi tana furta Tom, ka jira ni a waje, yanzu zan fito. Bai sake kallonta ba ya fice daga bedroom D in. D akinsu Amani ya nufa. Sai da ya yi nocking k ofar sannan Amani da take tsaye hannunta rik e da comb tana taje kanta ta furta Mama Talatu shigo mana. Idanunta ya sauka akan na Dada da yake tsaye yana kallonta da sauri ta janye nata idanun sanda yarda gabanta ya tsananta bugu. Shima janye nasa idon ya yi yana furta Ku shirya zamu tafi. Ta d an waro ido tana furta Yanzu kuma Dada? Ai basu gama kai mana kayan ba. Bai amsa mata ba ya fice daga d akin. Ta bi shi da kallo tana sake shak ar k amshin turarensa. Sai kuma ta saki murmushi ita ka dai tana tab e baki fa da take son yi da zuciyarta, amma ta kasa yarda laifin na zuciyarta ta ne. Sanda Iman ta fito ta gaya mata Dada ya ce su shirya wani irin farin ciki ne ya lullub eta ta tsani gidan da duka abinda yake cikinsa, ta tsani Safna, tana fatan komawarsu sabon gida yasa zasu koma da kowane bak in ciki ba, banda ma maganar aurensu Didi ta dakatar ita da zata fi so ta yi aurenta ta huta. Tsaf suka shirya cikin kyakykyawar shiga yau Amani ma hijab ta saka kamar Imaan. Suka fito parlorn. Safna na ganinsu ta ha de fuskarta sosai tana jin wani bak in ciki. Kafin ta kalli Moddi ta ce Da su za a ne? Madadin amsa mata da baki, d aga mata kai kawai ya yi. Ta saki wani k aramin tsaki tana hararar Moddin k asa k asa. Ta lura kwana biyun nan wani Izza yake ji Amma zata yi maganinsa. Wata irin mota mai masifar kyau shiga. Tunda kuma ya fara driving bai ce komai ba. Baka jin komai sai surutun Amani da Ya cika motar. Zuciyar Safna a tunzire take da Amanin sosai. Ga Moddi bai gaya mata inda za su ba. Tafiyar sam bata mata ba, don haka kawai take jin gabanta na wani irin masifar fa duwa. Don haka cikin hassala ta ce Wai ina za mu ne? Unguwa Ya bata amsa ba tare da ya ko kalleta ba. Sai ta ja baki ta tsuke a ranta take lailayo ashar tana zuba masa. Amani tana baya farin ciki duk ya cikata jin Dada bai gayawa makirar matar inda za a ba. Da alama bata san ina za su ba, bata San ma za su koma sabon gida ba. Hakan yana nufin akwai Daru kenan Bai tsaya ko ina ba sai a harabar gidan. Safna ta dinga Ware ido tana kallon gidan da ya yi masifar tafiya da imaninta. Sai dai gefe guda wani irin tsoro ne ya shigeta. Bata manta garga din Bokanta ba. Kada ki sake ki tare a sabon gidan nan sai kin zo mun Miki aiki, idan ba haka ba komai ma zai iya faruwa. Aikinmu da duk abinda kike tak ama da shi zai warware . Jikinta Har rawa yake da tuna hakan. Don haka da sauri ta kalli Moddi ta ce Ina ne nan? Ba dai sabon gidan mu ba ne? Ba dai tarewa muka yi yau ba? Ya bita da kallo yana mamakin sauyawar yanayinta. Madadin amsa mata sai ya saka kawai zai shiga gidan. Da sauri ta ja hannunsa tana girgiza masa kai jikinta na rawa ta furta Kada ka shiga Imaam, wallahi akwai matsala, ya zaka kawo ni gida ba tare da sani na ba. Me kake nufi ko zuwa muka yi mu gani mu koma. Ya an janye hannunsa yana furta Mun dawo kenan, akwai matsala ne? Saura k iris fitsari ya zubo mata. Ta wani irin zaro ido tana girgiza kai ta furta Me? Wallahi ba zan shiga ba, wannan ma ai rainin hankali ne, ta ya zaka ce min na dawo gida ba wani shiri Ya an k ura mata ido kafin ya saki wani murmushi Ya furta Shiri? Shirin me zaki yi? Duk wani shiri na gama shi a gidan nan, akwai duk abinda za ki buk ata a ciki. Didi ma tun jiya ta tare wannan karan fitsarin sai da ya zubo. Ta runtse ido tana tuna sauran maganar da ta z auna mata daram a kwanya. Ta haddace ta kamar karatu. Barin Uwarsa ta zauna inuwa d aya da shi, ina tabbatar miki kamar shigar ki matsaloli ne ba matsala ba. Dole ki raba Uwarsa da gidan sa Idan bata manta ba shine dalilin da yasa ta dinga zubawa Didi rashin kunya da rashin mutunci har ta gaji ta tattara ta bar gidan. Sannan yanzu ya gaya mata wai Didi na ciki. Kai ina ai ba ma zai yiwu ba. Gaba d aya duk ta rikice hakan yasa Moddi ya tsaya yi mata kallon mamaki su kansu