Sashe 33
Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsarabar Dada s Girl. Moddi ya cafe yana ware ido yana dariya ba Wanda bai San son da yake wa yaransa ba, musamman Amani da ta zama ta gaban goshinsa rigimar yarinyar shagwab arta duk yana son su. Gefe guda kuma rashin tsoro da tsiwar da take wa Safna abin yana bashi mamaki. Ta wannan b angaren kam ya sarawa Ama don bata da tsoro ko ka dan. Chocolate d in ya bi da kallo da ku din da aka siyeta ya ware ido cike da mamaki yana sakata cikin akwatinsa ya ajiyeta a inda zai ganta. Yana fa din Thank you Boss, kamar ka San Amaa ba abinda ta fi so a duniya irin chocolate Na sani Alwan ya furta tana kallonsa yana dariya. Moddi da mamaki shima ya kalleshi ya ce How do you know? Murmushi kawai Alwan ya saki ya ce Na gani a barci Bai wani bawa abin mahimmanci ba don a time d in Alwan bai sake bijiro masa da wata buk ata ba da zata sa ya dasa zarginsa a zuciyarsa Sanda suka dawo Amani ta rungumeshi daga ranar ya fara Jin wani irin zazzafan feeling a kanta. Feeling d in da kawai mata da miji ya kamata su ji shi. Rayuwarsa ta jiye tunanin Amani ya dinga bijiro masa tun yana yakice abin har yaga abin fa da gaske ne, gudun sab awa Allah yasa ya bawa Kansa mafita, mafitar da yake ganin shi Kansa ba daidai ba ce ba kuma ta dace ba, amma ba yarda zai yi dole hakan zai aikata da wani zunubin gwara wani Tafin da UMMA T ta yi a fuskarsa ya saka shi bu de ido da sauri yana kallonta. Birkitattun idanunta da suka bayyana b acin ranta tsantsa ta zube a Kansa tana furta Gaya min gaya min komai Imamu idan kuma ka b oye min wallahi ba zan yafe maka hakk in y an uwan taka ba Cikin wani yanayi ya jingina Kansa a kujera muryarsa cike da rauni ya ce Idan na fa da Miki zai zama sirri a tsakanin mu har na samu mafita? Ta ha diye wani Abu da take Jin kamar ya tokare mata numfashi. Murya a shak e kamar ba tata ba ta ce Idan na b oyewa kowa ba zan b oyewa mahaifiyar da ta haife mu ba, ko bakomai ya kamata Didi ta sani Moddi ya dinga kallonta cikin tashin hankali yana girgiza Kai ya furta Bana so Didi ta sani, ba na so ki dasa mata b acin ran da zai zama sanadiyyar ajalinta Ban San yarda zan iya rayuwa ba idan na zama silar mutuwar Didi . Ki zame mayafin Sirri na Teey Ya fa da yana matsa yatsun hannunta da sauri. Teey ta dinga kallonsa kafin ta ha diye wani yawu. Ko kafin ta yi magana ya mik e da sassarfa ya isa bayan kujera yana zagaye parlorn Teey dai ta zuba masa ido tana jiran Jin abinda ya ce Kin amince as secret na gaya maki komai Ba yarda ta iya banda ta amince d in tunda tana son ji, tana son Jin matsalolin Kiddonta ta San hanyar da zata bi ta samo masa solution idan abin bai fi k arfinta, don haka bisa ta tilas ta ce Na amince Ya zagayo gabanta yana mik a mata hannu ya ce Promise Nata hannun ta saka ya dunk ule waje guda hakan ya tabbatar da Sun k ulla yarjejeniyar alk awari a tsakaninsu ya zauna daf da ita ba tare da yana kallonta ba ya hau matsa hannunsa yana furta Tun muna yara na amince soyayyar da take tsakani na da ke mai girma ce, kin fi kowa so na a cikin y an uwana ke ce solution na duk wata matsala da ta tunkaro ni, ko a wannan karan na so naje Miki da tarin matsalolina Ban San me yake dabaibaye ni na kasa aikata hakan ba. Teey ki amince ba ganganci na yi da rayuwata sai K addara da ta saka ni jefa kaina cikin ramin da ba mai fitar da ni sai Allah, na San ni mai laifi ne Fateemah Amma wallahi Ban San yarda hakan ta faru ba Tun kafin ya ce komai hankalin Fateemah ya tashi zuciyarta ta dinga rawa ta San koma meye zai fito daga bakin Kiddo ba mai da di ba ne, muninsa mai saka k una da ra din zuciya ne, ba mamaki da zarar ta gama ji zuciyarta ta buga ta Mutu, Amma duk da haka tana son ji, tana son Jin Matsalar Kiddo ko da zata zama ajalinta don haka cike da k arfin hali ta ce Ina Jin ka Imaam a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya shiga bata labarin ha duwar su da Muhammad Alwan har zuwa yanzu da komai yake Neman ya dagule masa, ko na ce ma ya Dagule d Kafin ya gama bata labari tuni duk wata gab a ta jikinta ta fara rawa kakkarwa take sosai ga wani tarin gumi da yake tsatstsafo mata. Idanunta da suke disashewa ta zube a kan Kiddo, tana son ta gano gaskiyar abinda ta gani a k wayar tasa idanun. Tsoro ne sosai a cikinsu tsoron da ya bayyana har a sassan jikinsa ta hanyar sanyin da gabbansa suka yi. Bata tab a ganin karaya a tare da Moddi ba tun tashinsa har girmansa sai yanzu da yake zube a gabanta cikin Neman mafita . Raunatattun idanunsa ya zuba a kanta yana fatan Tee d in ta samo masa mafita, mafitar da zata zama alheri gareshi da ahalinsa gaba d aya hawayen take zubarwa kafin ta d ago cikin karayar zuciya da ta murya ta ce Idan har na gane abinda ka fa da Moddi, ka jefa kanka ne cikin k ungiyar matsafa masu Neman ku di ta ko wani hali. Me yasa Moddi? Me yasa naka ajiye kanka inda Allah ya ajiyeka ba? Ya kake so Didi ta ji a sanda ta sameka da wannan laifin? Zuciyarta zata buga zata samu matsala sosai da lafiyar ta ka sani ko? Me yasa tun kana yaro ka zama Kai je jarrabawar Didi? Kai ka dai ne namiji Amma Kai ne kake wahalar da ita, bata Jin da Dinka ko ka dan saboda ka auri matar da za a kira k arfen k Ban San me zan ce maka ba, Ban San wace shawara zan baka ba Ta fa da tana dafe k irjinta da ya matsa matsa mata da wani irin bugu. Shi Kansa kasa magana ya yi bayan idanunsa da suka yi jajur jijiyoyin Kansa suma Sun bayyana tashin hankalin da yake ciki. He wish ace duk abin nan mafarki yake yi ba gaskiya ba. Abubuwa da dama Sun bayyana Alwan a matsayin mutumin kirki ba zai ce ya tab a samunsa da wani mugun abu ba, Amma me yasa ya kasa yarda da shi? Dole zai saka ayar zargi a Kansa ya kuma zama dole ya raba jiya da shi anzo gab ar da Sam ba zai iya mu amala da shi ba koda hakan yana nufin rasa rayuwarsa ta yaya zai saka masa sha awa da son yarinyar . Sai ya datse leb ensa da k arfin gaske yana Jin takaicin abinda yake ji d in yana saka jikinsa wani irin zafi kamar mai zazzab i da sauri kuma a wani irin fisge ya mik e ya nufi k ofa dole ne ma yaga Alwan a Daren nan ya gaya masa ba zai iya ba, ba zai iya aikata abinda yake so ba, sannan daga yau kuma ya bar harka da shi koda zai mayar da shi bashi da komai ne . Duk da kiran da Teey take masa bai juya ba. Ta runtse idonta bayan Jin fisgar motarsa da k arfin gaske. Ya Ilahil alameen! Fateema ta fa da tana runtse idonta zuciyarta na cigaba da wani irin matsanancin bugu (Masu tambaya Hadarin gabas Free ne? Aa ba free bane, book 1 ne free book 2 and 3 paid ne. A saka ku di ta wannan account din 2118666253 UBA. 500 mutane na musamman a cikin gida na musamman 1k ne as Usual. Na gode k warai. Hadarin gabas zai zubar da ruwa mai tarin yawa biya ku dinki ba zaki nadama ba, baa fara komai a labarin ba duka wannan sharar fage ne JIKAR NASHE HADARIN GABAS PAGE 19. 08033748387. NAZEEFAH SABO NASHE Ko gida bai je ba, ya nufi Airport direct saboda sometimes haka kawai yana siyan ticket ma ya yi booking koda ba tafiya zai yi ba saboda irin wannan tafiyar ta afujajan. Bai nemi ko driver ba, haka ya ajiye motar a parking space na airport d in ya zura key d insa a aljihu. Ma aikatan airport d in sai gaisuwa suke kawo masa, ba ya cikin sukunin da zai iya yi musu kyautar da ya saba musu ta bajinta, don haka kawai d aga musu hannu yake, a fuskarsa suke hango damuwa don haka basu damu ba musamman sanin cewa ba halinsa ba ne. Ya ci mugun sa a har an fara boarding jirgi ya shige direct zuciyarsa na wani irin hucin b acin rai, tana kuma bugawa da k arfin gaske. Burinsa ganin Alwan ya Kuma yi baran baran da shi, ko zai cire musu k ullin da ya k ulla tsakanin sa da Amani. Tunda suka shiga jirgin har jirgin ya tashi idanunsa a lumshe suke, bai kuma bu de su ba kamar mai barci sai dai ba barcin yake ba tsabar damuwar da ta cika masa zuciya ne yasa baya buk atar ganin komai. Yana jin ana tambayarsa ko akwai abinda yake so, idanunsa a lumshe ya girgiza kai. Duk da yana buk atar ruwa yana buk atar ya sha ruwan ko don yarda mak oshinsa ya bushe sai dai b acin ran da yake ciki ba zai bari ya sha ruwan ba. A haka dai Allah ya taimake shi jirginsu ya yi landing a Nmadi azikwe airport ba tare da zuciyarsa ta tarwatse ba. Sai da ya bari aka gama turmutsutsun fita sannan ya bu de lumsassun idanunsa da suka masa wani irin masifar nauyi da yake jin su sosai. Hannu ya saka ya ciro black shade d insa