Sashe 11
Hadarin Gabas Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Imani ta saki baki tana kallonta kawai bata san sanda hawaye ya fara wanke fuskarta ba, Jikin Amani ya yi sanyi ta d an ware ido tana kallonta tana furta To me nayi kuma? Ce miki aka yi yanzun zan mata illa? Bata fasa hawayen ba kamar yarda tsoron da take ji bai fasa bayyana akan idanunta ba Ba zaki daina irin wannan kalamin ba? Kina tunanin da Mami tana nan zata ji da din abinda kike yi? Ya zama dole ki amince da Mahmoud ki yi aure Wallahi ko wasu halayen naki zaki canja su shima Dada ya huta da saka shi magana da kike. Amani bata mata magana ba ta koma gadon ta kwanta idanunta a lumshe wani irin barci take ji sosai don da daddare ba barcin take samun yi sosai ba idan ba irin wannan lokacin ba saboda tsabar b acin rai ko abinci bata nema ba tun wanda ta tsakura da safe. Imani ta bita da addu ar shirya a ranta kafin ta mayar da kai itama ta kwanta idanunta akan hoton mahaifiyarsu da ta zuba mata ido kamar ta san a cikin kewar rashinta take wani abin da tana raye ta tabbata Amanin ba zata yi shi ba. Sai Yamma can Dada ya fito daga d akinsa jikinsa sai baza k amshin turare yake. Idanunsa suka fa da kan na Mommy da take zaune ta fece wanka sai zabga k amshin turare take. Murmushi ta sakar masa tana furta Sannu da fitowa Moddi Allah yasa dai ka bar fushin da kake yi a cikin d aki. Ya d an saki ajiyar zuciya yana zama a can gefe kansa ne yake d an sara masa. Mommy ta taso gefensa ta zauna tana saka jikinta ka dan a nasa ta shafa k irjinsa ta furta Moddi ka yi hak uri please In sha Allah ba zaka sake samun b acin rai ta dalilina akan Amani zan rik eta kamar y ar cikina Ajiyar zuciya ya saki yana jin kaso casa in na cikin b acin ransa yana tafiya ya shafa kanta a hankali ya furta Promise.. Ta saka hannunta cikin nasa a kunnensa ta ra da masa Yes promised! Ya lumshe idonsa yana kai mata peck a lab banta Allah ya baki iko Ameen ta furta tana ji a ranta wannan abinda ta yanke a zuciyarta shine abinda ya dace tuntuni Mommy mayaudariyar mace ce data san salo salo da take bi wajen mallakar Moddi, shi kuma a rayuwarsa baya son hayaniya don haka sam baya son maganar k ara aure, ya lura kuma shine abinda y an uwansa suka fi so a yanzu, sai dai shi da kansa ya san bai isa ba, bai isa ya yi maganar k ara aure ba, bayan masifar Mommy shi kansa ya san yana yin kasuwancinsa ba zai bar shi ya ha da mata biyu ba, bayan haka ma akwai wani b oyayyen dalili mai girman gaske da zai hana shi kasa auren Hadarin gabas .. Mai hankali ya lek a yamma yanzu aka fara ku bini a hankali kada mu yi garaje a cikinsa, abu guda da na sani ba zaku yi Dana sani a cikin bibiyarsa ba. JIKAR NASHE HADARIN GABAS NAZEEFAH SABO NASHE Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/HBqR4GFrqIMH7TjAy8IYgj (ku yi joining group. Ba mamaki daga yau iya groups Dina Zan dinga posting.) 08033748387. Safna sam hankalinta kasa kwanciya ya yi, hakan yasa ta shiga tunanin yarda suka dinga yi dai Malamai kala kala akan aikin Amanin, kowane Malami gaya mata yake aikin ba zai yiwu ba saboda yarinyar tana da Jinnu a tare da ita. Da k yar ta samu Malamin da ya ci alwashin zai mata aiki akan hakan. Ta yi amanna da Malamin nan fiye da Imanin da ke cikin zuciyarta. Ta tuna ranar da ta kai masa kukanta. Kallonta Malamin kawai yake kafin ya maimaita abinda ta ce cikin sigar tambaya. Kika ce kina so a mayar da ita karuwa? A saka mata son bin maza ta yarda Uban da ya haifeta ma zai tsaneta? Safna ta jijjiga kai Haka nake so Allah gafarta Malam, so nake ka mayar da ita haka, ka saka mata matsananciyar sha awa ta yarda zata kasa controlling kanta Har sai ta bi maza. Ya saki ajiyar zuciya kafin Ya buga k asa sai kuma ya saki murmushi na hango nasara wannan karan Safna, tabbas aikinmu zai ci ba kamar lokutan baya da kike asarar ku dinki ba. Aiki zai ci amma ban ce miki yau ko gobe ba, ke dai ki zuba ido, kada ki yi garaje. Murmushi ne Ya kub rce mata tana jin tsantsar farin ciki yana bin zuciyarta a hankali ta furta Sai yanzu hankalina ya kwanta, burina zai cika Malam Wannan kenan ta tuna tana sakin ajiyar zuciya a hankali ta furta sai yaushe aikin nan zai ci ne?