Sashe 9
Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Toh mu haɗu a next page 📃📃📃
ANA ZATON WUTA A MAƘERA.....🔥
✒️IBNATU-UMAR ✒️
Page 13&14
Suna dawowa saiga kiran Ameerah tace yazo ya dauketa, maida tecno dinshi yar dubu ashirin yayi cikin aljihu ya kallesu yace sorry kids, zanje in dauko mamanku. Uncle Moh please kaje damu, suka faɗa suna marairaice fuska. Shiru yayi kamar mai tunani yace banason hayaniya zakuyi shiru? Eh baza muyi magana ba suka haɗa baki wajen faɗa.
Buɗe masu bayan motar yayi suka shiga.
A nutse yake tuƙi har ya isa News Buzz.
Uncle Moh cewar Zaid yana leƙen fuskarshi, Na'am yafaɗa yana kallonshi.
Muje ciki pleasee, no kujira yanzu zata zo. Yafaɗa yana kallon Nisah data nufo motar rike da files. Gaba ta buɗe ta saka, kallonsu Zayn tayi tace daku aka zo? Gaisheta sukayi, ina Mamii cewar Zaid yana kallonta, tana ciki zaku shigo? Uncle Moh mu bita? Gyaɗa masu kai kawai yayi, yehhh suka faɗa suna bin Nisah ciki.
Faɗa sosai take ma Faith akan letter da'aka turo dashi sati daya kenan bata gaya mata ba. Tayi misplacing dinta, can't you put things right? What is wrong with you faith.... shiru tayi sanda idonta ya sauka akan su Zayn dake tsaye a gefe sun sha jinin jikinsu dan bata taɓa daga masu murya ba, balle faɗa har haka.
Ganin yadda suka tsorata yasa ta aro murmushi tace oyoyoo da gudu suka nufeta suna murna. Waya kawo ku? Tafaɗa tana kallonsu da murmushi, haɗa baki sukayi wajen cewa Uncle Moh ne!! Ku muje toh tafaɗa tana haɗa yarkacen ta cikin jakarta.
Ta kalli Faith da duk ta rude tace mata ta nemo letter dinnan, sannan ta kamo hannun su Zayn suka wuce.
Cikin sauri ya sauko ya buɗe masu suka shiga, yayi ma motar key suka dau hanyar gida.
Parking yayi ya buɗe mata, sauka su Zayn sukayi da gudu sukayi gida, tafiya ta fara yi taji jiri ya ɗebeta, saurin dafe motar tayi tana lumshe idanunta, Ma'am are you okay? Yafaɗa yana kallonta, Am fine tafada tana wucewa cikin gidan.
Juyawa yayi ya fita daga gidan, bakin titi ya nufa ya hau machine, kamar tafiyar minti goma ya sauka.
Wani ne ya sauko daga wata bakar mota mai kyan gaske sanya da uniform dinsa na driver, ina wuni yallabai yafaɗa yana kallonsa, Gyaɗa mai kai kawai yayi ya buɗe motar ya shiga, ina muka nufa? Gida yafaɗa yana fuskar dayasa ma fuskarsa, gyara gashin kansa daya hargitse yayi.
Parking drivern yayi ya sauko ya buɗe mai, cikin gidan ya nufa da sallama a bakinsa. Ina wuni Ummii yafaɗa yana zama gefen kafarta, Am fine Ruhaan tafaɗa tana shafa kanshi. Ba zaka ci abinci bane tafaɗa tana kallonshi, na koshi Ummii sai zuwa anjima bari na watsa ruwa Magrib ta kusa yafaɗa yana shigewa ciki.
A bangaren Ameerah kuwa itama bacci tayi a daddafe ma tayi wankan. Kiran sallar Magrib ne ya tashe ta, bayi ta shiga tayi alwala tayi sallah. Tana zaune Mahmud ya shigo rike da lapcoat dinsa a hannu. Sannu da zuwa tafaɗa tana kallonshi da murmushi, murmushin shima ya mayar mata, tashi tayi ta amshi lapcoat din hannunsa da niyyar sata a laundry, shi kuma ya shiga bayi.
Abu taji a cikin lapcoat din, hannu tasa ta ciro, kallon turaren tayi tana mamakin mai kuma yake da wannan, fitowa yayi, yayi saurin amshewa yace Bashir ne ɗazu da yazo office ya manta, ina ga na Umm Farha ne. Ban tambaye ka ba ai....wannan dogon jawabin na miye tafaɗa tana tsare shi da ido. Babu komai fah kinsan na saba gaya maki every single little detail shiyasa, amma in ranki ya ɓaci kiyi hakuri na cika ki da surutu. Duk sai taji ba dadi, hakuri ta bashi, ta fita ta duba koh an haɗa komai a dinning din.
Washegari da safe, ta fito a shirye kamar kullum looking decent and gorgeous, kallon Uncle Moh dake gaisheta tayi ta amsa. Ma'am how was your night? Yafaɗa yana kallonta, my night? Is that your business? Refrain from asking me such questions in the future.... Tafaɗa babu alamar wasa a fuskarta.
Sorry Ma'am yafaɗa yana buɗe mata kofar, ko da ya kaita office ce mai tayi ya dawo gida....kamar jiya su Zayn sun kawo mai abinci yau ma. Kullum haka Ameerah kemai, a hankali wata irin shakuwa ta shiga tsakaninsa da yaran. Ya zama magana ɗaya biyu zasu yi sai sunce Uncle Moh kaza, Uncle Moh kaza.
Yau weekend shiryawa Ameerah tayi ita dasu Zayn zasuje gidan Anty Mami da bata jin dadi daganan suje wajen Ammi.
Uncle Moh ne ya tuƙa su, gidan Anty Mami suka fara zuwa, duk ta rame sosai hankalin Ameerah ya tashi harda kukanta. Haba maman babanta miye na tada hankali, cuta ai ba mutuwa bace uwata, kiyi hakuri kibar kuka kinji? Tafaɗa tana kallonta, toh Anty Mami tafaɗa tana share hawayen ta sun jima a gidan da zata tafi Anty Mami ta bata ajiyar mukulli, tace ta tafi dashi ta ajiye mata. Amsa tayi tasaka a jakarta. Ledoji da yawa yan aikinta suka biyosu dashi na siyayyar da tama su Zayn, godiya suka mata aka saka kayan a booth suka nufo gidan Ammi.
Parking yayi ya buɗe masu, da gudu Zayn yayi cikin gidan yana kwala ma Ammii kira, murmushi tayi sanda taji muryar Zayn, dan nema tafaɗa tana murmushi.
Da gudu ya faɗa jikinta yana mata surutu. Ameerah data shigo rike da hannun Zaid ce ta tureshi tace ɗaga min uwata malam, tafaɗa tana rungumeta. Murmushi Ammii tayi tace kin dai ji kunya.
Inna mai aikin Ammi ce tazo dauke da tray cike da kayan ciye-ciye ta ajiye ma su Zayn. Kallon Ammii Zaid yayi shi duk a tunanin shi da gaske Ammi ce ta haifi mamansu Grandma Uncle Moh yazo ya gaishe ki? Murmushi tayi tace waye kuma Uncle Moh ? AMMIII sabon driver nane, kullum basuda magana sai ta Uncle Moh, da yake yanzu ana hutu suna zama tare dashi.
Ahhh ya zama dan gida ai, kira shi mu gaisa cewar Ammii, da sauri Zaid ya fice Zayn na binshi a baya. Inna dan miƙo min hijabi na tafaɗa tana kallonta.
Sosai Ruhaan yayi mamakin abinda sukace, amma sai ya bisu. Sallama yayi aka amsa mai.
Shigo mana dannan, dummm yaji gabansa ya faɗi amma sai ya shanye. Shigowa yayi ya durkusa ba tare daya kalli kowa ba yace ina wuni, amsa mai Ammii tayi dai-dai Inna na mika mai glass cup dauke da ruwa. Sakin kofin yayi ya ɗago ya kalleta, nan take jijiyoyin kansa suka fara tashi idanunsa da suka fara rine wa yayi saurin kullewa, ba wanda ya kula da yanayin daya ke ciki, illa sannu da suke mai, suna kuma tambayar bai yanke ba. Babu komai yafaɗa yana ƙaƙalo murmushi.
Bara na koma yafaɗa da niyyar miƙewa, a'a bari kaci abinci tukunna cewar Ammii da fara'a, abinci aka zubamai a dinning ya nufi cen ya zauna sai jujjuya abincin yake gabaki ɗaya ya kasa ci. Kallon yadda Ameerah ta zama wata yarinya gaban Ammii yake, yana mamakin ina tasanta, taya sukayi building kallar wannan bound din? Da gani kuma kasan akwai kauna mai karfi a tsakaninsu.
Bazai yiwu ba yafaɗa yana taune lips dinsa.
Da kyar Ammii ta barshi ya tafi, ya koma waje. Sannan suk Ameerah suka fito suka tafi da wasu kayan niƙi-niƙi.
Parking yayi suka nufa ciki, koh su Zayn basu mai magana na yau dan sun ga kamar ranshi a ɓace yake.
Yau haka kawai Ameerah ta tashi da faɗuwar gaba, kiran Ammi yayi sun dade suna waya, sannan ta kashe. Kallonta Nisah tayi tace lafiyar ki Meerah? I don't know tafaɗa tana mikewa zaune, hannu tasaka ta share hawayen dake fita a idon Ameerah tace wannan kukan na miye? Kuka kuma tafaɗa tana juyawa da kujerarta ta kalli mirror. Sai kawai ta fashe da kuka, Subhanallahi cewar Nisah tana kallon Ameerah, ban san mai ya faru ba Nisah, my heart is heavy, tafaɗa tana fashewa da kuka.
Files din data aika Ruhaan gida ya dauko mata, ya shigo dasu. Tsayawa yayi yana kallonta, ajiye files din yayi har ya juya zai fita, sai kuma ya koma. Jug din ruwan daya gani a kan table din ya zuba mata a cup, ya tsaya yana kallonta. Haɗe rai tayi, ta dauki tissue ta goge fuskarta. Have this, yafaɗa a sanyaye, taso yin banza dashi amma kuma sai taji bazata iya ba. Amsa tayi ta sha sai taji zuciyarta tayi sanyi. Thanks tafaɗa tana kallonshi. When you're sad the Qur'an should be your companion. Yana faɗin haka ya wuce, da kallo ta bishi tana tuna wani abu dana shuɗe a shekarun baya.
Yana fita ya wuce Central Mosque dan yin sallar juma'a.
Aikinta ta cigaba dayi, tana cikin aikin sai ga kiran Daddy Tahir mijin Anty Mami, dauka tayi da sallama, karar faɗuwar wayarta ne yasa Nisah juyowa, cikin sauri ta nufi Ameerah ganin tayi baya zata faɗi itama.
Kallonta tayi tace Meerah! Meerah! Lafiyar ki kuwa? Wayarta kawai take nuna mata tama kasa magana. Daukan wayar tayi, jin abinda ya faɗa yasata itama ta ruɗe.
Meerah ki nustu, ki tattara nustuwar ki waje ɗaya, kar ciwon ki ya tashi tafaɗa tana ɗagota.
Ganin idanunta na kafewa, tana nunfashi da kyar yasa Nisah dauko Inhaler din ta cikin sauri ta taimaka mata dashi.
Toh mu haɗu a next page 📃📃📃
Shin mai Ruhaan yake yi a gidan Ameerah matsayin driver?
Shin Anty Mami da tayi recommending dinshi, tasan shi waye?
Miye a tsakanin Ammi da Ruhaan da har baison alakarta da Ameerah?
There is more to this, ku biyoni dan jin yadda zaka ƙare....
ANA ZATON WUTA A MAƘERA......🔥
✒️ IBNATU-UMAR ✒️