Sashe 21
Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Toh mu haɗu a next page 📄📄📄
ANA ZATON WUTA A MAƘERA....🔥
✒️IBNATU-UMAR✒️
Page 33&34
Tasan cewa Abbee bai buƙatar izininta kan yayi aure, amma she felt betrayed a yanayin closeness dinsu da Abbee how can he make such a big decision without telling her. Da haka bai faru ba tazo ta gani da bazai gaya mata ba kenan.
Buɗe kofar ta da akayi yasa ta juya dan ganin waye. Ganin Aunty Mami yasata rugawa da gudu ta fada jikinta ta rungumeta, sai ajiyar zuciya take saukewa. Khadijah baiwar Allah kiyi hakuri, kowani bawa da irin jarabawar shi.
Wannan abin daya faru yasa Ameerah taja baya Abbee. Wanda a nashi bangaren sosai abin ke damunshi. Ana haka Ameerah tazo ta fara ciwo, koda likita ya dubata nan ya gano ciki karami a tattareda ita. Murna sosai sukayi musamman Abbee da Ameerah. Kallon Abbee dayace ya kamata a sanar dasu Abbu tayi tace Abbee idan dai da gaske you still regard me as your daughter kuma kana kaunata karka gayama kowa daga cikin Ahalin Ruhaann. Amma Ameerah dole su sani ai...eh amma ba yanzu ba Abbee. Toh kawai Abbe yace bai kuma ɗaga maganar ba dan baison tashin hankalin Ameerah dama gashi ba wani lafiya gareta ba.
Haka suka cigaba da rainon ciki harda Aunty Mami. Har Ammi na zuwa duba Ameerah time to time kuma tana kawo mata abubuwan tabawa irin na masu ciki.
Hajiya Hamdiyya nunawa Abbe da Ameerah so take sosai, amma kwata-kwata duk da haka Hajiya Hamdiyya taƙi kwanta ma Ameerah a rai.
A wannan lokacin yawanci Amira na spending time dinta a zane ne. Wani zubin ta zana Ummi koh Humaira koh Dua. Wani zubin kuma ta kanyi zanenta akan Nature. Hakan na dauke mata hankali daga tunani sosaii.
A haka har Ameerah ta sauka lafiya, ta haifi maza yan biyu Zayn da Zaid.
Murna sosai Abbee da Aunty Mami sukayi. Ammi ma tayi murna sosai.
A haka a fara rainon yara har suka shekara 2. A yanzu Ameerah ta ajiye aikinta a lawyer a gefe tunda aka samu tangarda a wani shari'a da tayi inda ta buɗe NEWS BUZZ gidan jarida.
Yau Ameerah ta tashi da safe da kanta ta tuka motarta zuwa wajen aiki, data tashi ta wuce gidan Ammii sai wajen tara ta fito a gidan ta nufi gida.
Chak motarta ta tsaya a bakin titi, dauko wayarta tayi ta kira Mukhtar dan tayi duk yadda za tayi taki tashi, ganin wayar a kashe yasa taja tsaki. Kwata-kwata ta mance tasa charge.
Mahmud ne yayi parking motarshi, da murmushi ya mata sallama. Haɗe rai tayi ta amsa. Tambayarta yayi mai ya faru da motar yaga ta tsaya a hanya. Kamar tamai banza sai kuma ta bashi amsar cewa itama bata sani ba. Tayin lift ya mata tace a'a ta gode. Ganin ya matsa yana son taimakonta tace ban wayarka, miƙa mata yayi ta saka numbern Mukhtar ta kira. Jin muryar Ameerah yasa ya amsa cikin girmamawa, bayani tamai yace gashi nan zuwa. Bama Mahmud wayarshi shi tayi tamai godiya.
Kin tafiya yayi har saida Mukhtar yazo, matsawa yayi ta bashi number su dinga gaisawa. Bashi numbern tayi dan batajin magana.
Cikin kankanin lokaci Mahmud ya shiga ran duk wanda ke kusa da Ameerah ciki harda Zayn da Zaid da suke yara. Kowa yasan irin son da yake mata.
A bangaren Ameerah kuwa kawai mutunci take ma Mahmud bawai dan tanson shi ba. Amma ganin yadda ya nace yasa ta bashi dama. Ba'a jima ba kuwa akayi bikinsu. Ameerah ta yarda da auren Mahmud ne kawai dan ta manta da Ruhaan a rayuwarta amma abinda ta kasa ganewa shine koh Zayn da Zaid sun isa tuna mata da Ruhaan.
Mahmud na nuna ma su Zayn da Zaid so sosai, wanda hakan yasa ya samu wani irin matsayi a zuciyar Ameerah. Auren Ameerah da Mahmud nada wata biyu ta haɗu da Nisah. Nisah classmate dinta ce a sanda take jami'a. Basu wani magana amma suna mutunci. Hakan yasa bata matsayin P.A dinta.
Ranar wata asabar da Ameerah bazata taɓa mantawa ba, lokacin koh shekara da aure basu yiba. Zasu tafi da dare Zaid yace shi wajen Abbee zai zauna duk yadda tayi dashi ya bisu yaƙi. Haka suka tafi itada Zayn da Mahmud. Da safe kiran Mukhtar ne ya tashe ta yace mata yakai Abbee asibiti ya faɗi. Koh wanke fuska Ameerah batayi ba Hijab kawai ta daura ta nufi asibitin. Ikon Allah ne kawai ya kaita lafiya.
Mukhtar ne yazo ya shigo da ita, kallonshi tayi tace mai ya samu Abbee?
Shock ne acute cardiac arrest yasamu. What happened, why suddenly? Tafaɗa tana tura kofar dakin da Abbee ke ciki. Akan Zaid dake kwance unconcious a ƙasa ta sauke idonta. Ihu tayi taja baya ganin farin kumfa na fita a bakinsa. Ɗaga shi tayi tana jijjigashi tana hawaye. Saurin daukar shi Mahmud yayi ya juya ya fita dashi, ta tashi tabi bayansu taji karar machine din dake monitoring Abbee.
Hannunshi ya ɗago yana son mata magana. Rike hannushi tayi jikinta na rawa tana hawaye tace Abbee please karka tafi ka barni Abbe. Daya hannunshi yasa ya cire oxygen din da'aka samai, ganin yana son yin magana yasa Khadijah matsawa da kunnenta kusa da bakinshi. Abbee ta faɗi a firgice, ganin hannunshi dake cikin nata ya saki. Abbee nahh ta faɗa tana hawaye.
Haka aka dawo da Abbee gida aka mai wanka, aka kaishi gidan shi na gaskiya Ameerah naji na gani. Zaid kuma ya shiga coma.
Koh kwana uku da mutuwar Abbee ba'a yiba Hajiya Hamdiyya ta fito da zalamarta ta dukiya a fili. Sosai ran Ameerah ya ɓaci, ta rasa mai yasa tun asali bata son Hajiya Hamdiyya ashe ga dalili nan. Ga halinta nan ya bayyana.
Ran bakwai Hajiya Hamdiyya taso da malamai akan dole a raba gado, daga Aunty Mami har Ameerah ba wanda ya kulata. Abinda ya bama Hajiya Hamdiyya mamaki shine duk dukiyar Abbee babu abinda ta tsira dashi illa wasu shares na company dinshi da kuma gidan da suke zaune, Sai gidan gona guda ɗaya. Saboda kusan komai na Abbee da sunan Ameerah yake siya.
Tun daga nan tsan-tsan kiyayya Ameerah da Hajiya Hamdiyya suke nuna ma juna, ya zamana koh Inuwa ɗaya basa iya zama.
Wannan shine tushen labarin KHADIJAH ABDULKARIM KURFI.