Sashe 31
Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Bouquet 💐 din ta mika mata, amsa Humaira tayi tana shinshina furannin tayi murmushi tace my favourite. I know cewar bakuwar tana murmushi. Gift bag din ta buɗe ta ciro take away din abinci, da gani a waje mai tsada ta siyo. Buɗe take away din tayi ta saka spoon ta deba takai bakin Humaira tace haa... murmushi Humaira tayi ta buɗe bakinta ta bata. Karowa zatayi Humaira tace Bestt no please banjin yunwa wallahi dazu ma Amii taso zubamin abinci nace mata.....sauran maganar ce ta makale mata ganin wani irin mugun kallon da Amira ke binsu dashi. Kallon inda Humaira ke kallo Bestt tayi saurin rufe fuskarta da novel din hannunta Amira tayi, wace cewar Bestt a hankali dan bataga fuskar Amira ba, dan ta rufe fuskarta da novel din hannunta. She is my younger twin sister Issy, tafada tana murmushi, for real? tafaɗa tana zaro ido. Gyaɗa mata kai Humaira tayi, tashi tayi ta nufi Amira da murmushi a fuskarta tace Hii tana miƙa mata hannun damanta. Sauke Novel din Amira tayi tana kare mata kallo tace Hi batare data bata hannun ba. Bata sauke hannun ba ta kuma miƙa mata tace Hii, ko ɓaci ranta bai yiba. Hi Amira tafaɗa tana ɓata hannu. Murmushi Issy tayi tace Welcome Back Dear. My name is Islam Bintu Mus'ab. I am the your sister's bestfriend and her only friend. Idan kina son jin labarin yadda Bestt tayi missing dinki ki sameni zan baki labari. Rana bata taɓa wucewa ba ba tare datayi maganar ki ba. Issy ta jima kafin ta masu sallama Mukkaram yarakata ta tafi. Kallon Amira data maida hankalinta kan novel dinta Humaira tayi tace Amii. Banza Ameera tayi da ita kamar bata ji taba. Amii am talking to you, wani banzan kallo Amira ta mata tace talk to your best friend not me. Murmushi Humaira tayi tace haba Amii wani keda idan ba keba. No kinada ita mana Issy take kowa? Kinga ki dena damuna karatu nake. Eh naga alama shiyasa littafin yake up side down ai. Tsaki Amira tayi sanda ta kalli littafin taga hakane. Rufeshi tayi ta cilla kan couch din dake dakin. Amii zo kiji tafaɗa tana nuna mata gefenta. Karki ƙara kiran sunana fah tafaɗa tana haɗe rai. Toh ni bari inzo tafaɗa tana daura hannunta akan cannula din da'aka samata. Stop Stop Stop cewar Amira tana rike hannun ta. What are you doing? Kinada hankali kuwa? Murmushi Humaira tayi tace thought you didn't want to come to me. Enough please cewar Ameerah tana haɗe rai. Amii Issy is very important to me tafaɗa tana riko hannuwanta. Idan zaki dinga mata wannan behaviour din bazan ji dadi ba wallahi. Nasan itama bataji dadi ba amma kuma komai ya shafeni Issy bata wasa dashi, shiyasa ta basar da abinda kika mata. Dan Allah karki kuma. Tunda muna tare yanzu nasam zakina ganin Issy time to time. Kallonta Amira tayi da idanunta da suka fara chanza launi zuwa ja tace she is more important to you than me? Zaro ido Humaira tayi da mugun mamaki tace waya gaya maki haka? Basai an gayamin ba i offered you food but you refused. Amma ita da tazo dashi you did not refused and you were calling each other with creepy and annoying names. I don't like her! Tafaɗa tana zuciyarta na suya. You don't love me, you just love me because am your sister but ita kuma you choose to love her. Amii bafa yara bane mu, ita zataji ba dadi tazo takanas saboda ni kuma ke....ohhh my feelings don't matter to you sister? Tashi zatayi Humaira ta riko hannunta tace sit please Amii am not done talking. Amiii i love you to the moon and beyond. You're my twin sister! As far as Issy is concerned bazaki taɓa haɗa matsayinki da nata a wajena ba. You're my one and only sister. You are my life Amii. Ke kaɗai nike da🥺 i can sacrifice my life for you. Taya ma zaki haɗa matsayinki da nata? Murmushi Amira tayi tace better. Waitt were you jealous? Cewar Humaira tana kallonta. Amira is a very straightforward person hakan yasa ta kalleta tace i have to naga kamar ta fini matsayi a wajen ki. Impossible dear tafaɗa tana shafa kan Amira da hannunta dake sanye da cannula. You're my life. You're the only one i have🥺 She is a jealous person sukaji muryar Ruhaan dake shigowa yana faɗa. Hade rai Amira tayi tace mai kazo yi anan? Ka fita tafaɗa bacin rai na bayyana a saman fuskarta. Nazo maku da magana mai mahimmanci.... Toh mu haɗu a next page 📄📄📄