← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 50

Sashe 41

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

ANA ZATON WUTA A MAƘERA.... 🔥

✒️IBNATU-UMAR✒️
Page 63&64
Whattt! Yafaɗa cikin tashin hankali. Tsakiyar titin ya juya motarshi, saura kiris ya haɗa accident yabi bayan motar Humaira dake gudun gaske. Kiranta yayi amma bata dauka. Tsaki yaja ya ƙure gudun motar shi. Saitin motarta yace Aishha keee yafaɗa a tsawace ganin yadda ta rikice tana ihun ba birki a mota. Ki dauki wayarki. Jona wayar tayi da Bluetooth din wayarta. Listen to me carefully yafaɗa cikin wani irin tone da bata taɓa jin yayi magana haka ba. Kin haɗu da wani a hanyarki koh a asibiti? I swapped the file tafaɗa tana fashewa da kuka. Huci ya furzar zai yi magana tace da P.A din Ex Vice President. Whatt! Yafaɗa yana zaro ido. Kiyi kokari ki fita a cikin gari, i will be following you, kuma karki kashe wayar kinji? Toh tafaɗa tana yin yacce yace. Dayar wayarshi ya ciro a aljihunsa ya kira Ruhaan yace birkin motar Humaira akayi tampering. Subhanallahi cewar Ruhaann yana kallon Amira dake gefenshi ta zuba mai ido. Ka nustu karka bari Amira taji zatace zata biyo Humaira. Which may be bad. Akwai wata burner phone a cikin drawer ka ta gefen inda kake ajiye laptop dinka ta dauka number ɗaya ce a ciki. Ka kira idan an dauka kace "TRACK AND HELP" Yarima na gama faɗar haka ya kashe wayar.
Cikin minti biyu Ruhaan yayi abinda Yarima yace yayi amma gabaki daya he is restless. Humaira ta daɗe cewar AMIRA cikin damuwa. I need to go tafaɗa tana mikewa. Suna tare da Yarima karki damu yanzu zasu zo cewar Ruhaan yana ƙoƙarin convincing Amira.
Cikin minti goma babu abinda ke tashi a Abuja sai karar jiniya da hayaniyar motoci.
Ganin motar Humaira ta nufi dutse yasa yasha gabanta da motarshi. Ihuu tayi ta a sakin sitiyarin ganin yadda motar Yarima ke nufar ramin, murmushi ya mata yana cire wani abu ya naɗe kanshi.
Jiniya ta fara ji na nufosu,baƙaƙen motoci sama da hamsin suka fara zagaye su. Fasa glass din motar Humaira sukayi, ta fito, harta sauko ta koma ta dauko file din. Da kyar suka ciro Yarima. Are you.....sai na wanka maki mari yafaɗa yana ɗaga hannunshi a fusace. Nausar glass din motar yayi ya fashe, nan take hannunshi ya fara jini. Am sorry tafaɗa tana fashewa da kuka. Rungumeta yayi yace it's fine don't do that again. Shiru tayi tana sauraren yadda zuciyarshi ke bugawa kamar zata fito fili. Muje yafaɗa yana riko hannunta. Aucchh tafaɗa tana dafe kaurinta, mai ya faru yafaɗa yana rage tsayinsa dan ganin koh ciwo taji. Babu wani abu buguwar kashi ne kawai yafaɗa yana karewa kafar kallo. Chak ya dauketa ya nufi motar da aka buɗe mai da ita.
Kallon driver dake tukin yayi yace Studio din Ruhaan zaka kaimu.
Saukowa yayi ya dauketa ya shiga ciki, da sauri Amira dake safa da marwa ta rasa mai yake damunta ta juyo.
Sisterr tafaɗa tana nufarsu, sauketa yayi akan kujera. Rungume Amira Humaira tayi tana hawaye. What happened? Cewar Amira tana share mata hawayen. Ki gayamin banason ganin kukan ki cewar Amira jikinta har rawa yake.
Naje asibiti... tiryan-tiryan Humaira ta bata labarin abinda ya faru. Mikewa tsaye Amira ta dauki wayar ta dake kan kujerar da Ruhaan yake jikin har tsuma yake.
Aminullah ! Duk wani dirt, duk wata harka ta saɓa doka, dai-dai da wuce traffic 🚦 kafin lokaci yayi, a nemo akan Ex Vice President, 30 minutes. Minti talatin kawai na baku. Inason duk kan wani ma'aikaci dake News Buzz kuma yanason cigaba da aiki a nan toh ya dukufa kan aikin nan.
Kashe wayar tayi tana kallon Humaira ranta na suya. Ita kadai takeda, ita kaɗai ce yar uwarta. Kwafa tayi tace you messed with the wrong person.
No you won't do anything! Cewar Humaira tana kallon Amirah. Kinsan waye Rafik Adebola kuwa? Amii you should stay out of.... You be quiet! Cewar Amira a tsawace, cikin ɓacin rai take kallon Humaira. Tace baki da aiki sai boye min abubuwa masu mahimmanci, in your defense bakya son sa rayuwa a hatsare. Who do you think you are? Ke rai biyu gareki koh uku? Abi kin ajiye spare a dakin ki or are you some sort of immortal being tafaɗa tana riko kafaɗun Humaira dake hawaye. Amira tayi misunderstanding dinta, koba komai itace babba kuma tama Umminsu alkawarin kula da Amira taya zatasa rayuwar Amira a hatsari.
Nurr calm down cewar Ruhaan yana riko hannunta. Fisge hannunta tayi tace stay out of this, kaima kasan mai yake faruwa amma bakayi tunanin it's important in sani ba koh? But...malam rufemin baki tafaɗa tana ɗaga hannunta 🫸🏽
We can sort this out, duk hayaniyar nan batada amfani Amii cewar Yarima yana kallonta. Hararshi tayi tace am talking to my sister bansan wani a cikin ku ya ƙara samin baki.
Ke kuma ki ban amsa tambayar ki nake, kima tunanin kinada rayuwa biyu ne koh? Amii please stop cewar Humaira tana haɗe hannuwanta biyu 🙏🏽. Bazan bari din ba, tafaɗa tana mikewa zata fice riko hannunta Humaira tayi ta fisge ta nufi kofar fita. Tashi tayi zata bita jin zafin da kafarta tayi yasa ta saki ƙara ta koma ta zauna.
Saurin juyowa Amira tayi tace what happened? Are you okay tafaɗa tana kallon kafar da Humaira ta dafa.
Subhanallahi kinji ciwo, tafaɗa tana kallon kaurin Humaira daya kumbura. Get some ice cewar Yarima yana kallon kafar Humaira.
Kankara Ruhaan ya kawo yace sannu sister. Murmushi kawai Humaira tamai ba tare da tace komai ba.
Daura kafar yayi akan cinyarshi ya kalli Humaira yace it will hurt a bit. Nasani tafaɗa tana dauke kai. Murmushi yayi ya fara pressing ice din a wajen. Runtse idonta tayi tana jin zafin har tsakiyar kanta. Aucchh tafaɗa tana kankame hannun Amira dake gefenta. Sannu cewar Amira cikin damuwa kamar ba yanzu suka gama faɗa ba.
Neurogesic cream ya shafa mata a kafar yayi massaging dinshi. Well she is fine now, kawai ta gasa kafar da ruwan zafi daddare idan zata kwanta, kuma...
Ringing din wayarshi ne ya kaste zancen nashi.
Amsa sallamar Mukarram yayi, whatt? Shine abinda ya faɗa yana mikewa tsaye.
Yanzu kuna wani asibitin? Okay tom gamu nan zuwa.
Waye a asibiti? Cewar Amira tana kallon Yarima. Kuzo muje dai yafaɗa yana daukan Humaira yayi waje.
Cikin sauri suka rufamai baya itada Ruhaan.
Parking Yarima yayi ya sauko ya ruko hannun Humaira dan yasan ba zata iya tafiya ita kaɗai ba.
Kallon Mukarram dake zaune yayi tagumi tayi. Sannan ta kalli Zayn dake kuka ga jini a jikin rigarshi. Da gudu Amira ta karasa wajen Zayn tace mai ya faru. Shiru yayi yana kuka still bai ce komai ba. Mammi cewar Zaid yana rungumeta ta baya. Juyowa tayi tace What happened? Ammiii yafaɗa yana nuna mata kofar ICU din. Innalillahi Wa Inna Ilayhi Raji'un. Mai yasamu Ammi din? Tafaɗo akan bene and she is bleeding heavily. Jiri ne ya debi Humaira da badan hannunta na cikin na Yarima ba sai dai suga ta faɗi. Aishh, Aishhh yafaɗa yana bubbuga fuskarta.
Ruwa Mukarram ya kawo da sauri ya zubama Humaira a fuska. Numfashi taja tace Ammii mai ya sameta? Tana ina? Kofar I.C.U din ya nuna mata, mikewa tayi duk da zafin da kafarta ke mata ta nufi dakin.
Tana shirin shiga likitan na fitowa, tureshi tayi ta shiga ta ruko hannun Ammii dake kwance akan gadon a jona mata na'urori a kirjinta. Rufe bakinta tayi ta fashe da kuka, dafata Yarima yayi, juyowa tayi ta fada kirjinshi ta fashe da kuka. A hankali ya daura hannunshi a bayanta yace kiyi hakuri she will be fine, In Sha Allah.
Riko hannunta yayi suka fito waje. Jini tana bukatar jini kuma basu da jininta a Blood Bank cewar Mukarram cikin damuwa.
Miye blood group dinta cewar Yarima yana kallon likitann. AB- which is very rare. Da sauri Ameerah ta kalli Ruhaan shima kallonta yayi. Murmushi Yarima yayi ya kalli Ruhaan zaiyi magana Ruhaan ya kaste shi ta hanyar cewa zan bata jinin, muje ku gwada ni.
Dafe kanta Amira tayi tana tunanin abubuwa da dama. Bin bayan likitan tayi bayan ya raka Ruhaan lab din dakanshi. Magana tamai wadda ni banji ba, sannan ta koma wajen su Humaira.
Sister tafada tana cirewa Humaira tagumin da tayi. Amii cewar Humaira tana rungume Amira tana sake sabon kuka.
Wallahi da za'a buɗe kirjin Amira damuwar datake ciki tafi ta Humaira. Gabaki ɗaya hankalinta a tashe yake. Dakyar ta iya buɗe baki tace it's fine, kiyi shiru please.
Bayan na gwada Ruhaan, aka fara diban jininshi. Shigowa dakin Amirah tayi ta zauna a gefenshi. Kallonta yayi yace Are you okay? I don't know tafaɗa tana dafe kirjinta. Keee karki soma, yafaɗa yana kallonta. Kallon shi tayi da mamaki. Eh haka nace karki kuskura ki saka damuwa sosai a ranki har ciwon ki ya tashi. Gyaɗa mai kai kawai tayi.
Ɗaya hannunshi ya miƙa mata ta rike, matsawa ciki yayi ya janyota ta faɗo gefen hannun hagunshi. Just sleep yafaɗa yana dafa kanta. Banjin bacci tafaɗa tana mikewa zaune.
Shiru sukayi daga shi har ita ba wanda ya kuma cewa wani ƙala.
Har aka gama diban jinin, aka tafi dashi dan sama Ammii. Sannu tafaɗa tana riko hannunshi. Auchh yafaɗa yana ɓata fuska, subhanallahi da zafi? Eh mana. Am sorry tafaɗa tana sake mai hannun. Aucchh da zafi. Nafa saki tafaɗa tana kallon shi. Wayyo hannuna, yafaɗa yana dariya. Ɗakamai duka tayi tace so dramatic. Kira ne ya shigo wayarta. Matsawa gefe tayi ta amsa wayar, ta kusa minti 10 kafin ta kashe.
Muje tafaɗa tana miƙa mai hannunta, kee wai kin manta waye nine? Nine BURKAN fa! Dibar jini litre 3 ba wani abu bane a wajena yafaɗa yana mikewa tsaye, ya ruko hannunta suka fice.
Ganin su Yarima gaban TV yasashi karasawa, yana faɗin lafiya.... baki sake yake kallon TVn. Juyawa yayi ya kalli Amirah dake sipping ruwa a hankali yace youuu! Of course it's me Khadijah Abdulkarim Kurfi tafaɗa tana murmushi mai kyan gaske da zai iya rantse anfi shekaru shidda rabon da yaga irin wannan murmushin a fuskarta.
Amii what have you done? Cewar Humaira tana kallonta. He messed with my sister so I can play this game with him tafaɗa tana kashe mata ido ɗaya. 1,2,3,4,5 tafaɗa tana kallon wayarta ringing wayar ta fara. Murmushi tayi ganin mai kiranta, dauka tayi tace A very good afternoon to you sir. Saurin cire wayar tayi daga kunnenta ta kashe. Ƙara kira yayi, dauka tayi tace ba'a min ihu a kunne. Mai kake so? Ki cire videos da pictures din da kika daura a gidan jaridar ki.
The only thing i have left in this world is my sister. Kai kuma kayi yunkurin kasheta. Do you think i will just seat and watch?
Bayan ga haka kaine mutumin daka kashe mahaifanmu. So enjoy the social torture kafin ka tafi gidan yari.
Kinsan waye ni kuwa? I don't need to know. Amma kai kana underestimating dina.
Kaje wajen manyan da kake takama dasu su gaya maka wacece mai News Buzz. Wallahi message ɗaya zansa a tura kaf connection dinka sai ya rushe babu mai taimakon ka. Enjoy 😍 tafaɗa tana kashe wayar.
Kiran Mukhtar ne ya shigo wayarta yace Miss a bisa umarnin ki mun saki videos din kudin da VP ya sata, video din sanda ya bada umarnin a kashe sir, video din sex scandal dinshi. Yanzu haka Kasa ta rikice akan wannan videos din. Kuma insight din videos din a social platform dinmu yaban mamaki sosai. Murmushi tayi tace keep it up. Sannan zan tura maka list din wasu sunaye yanzu ina son ka tura masu text message cewa basu ba taimakon Rafik Adebola. Ka haɗa da duk wani weakness dinsu da mukeda a News Buzz ka tura tafaɗa tana kashe wayar.
Chapter 41 · 0% Book details