Sashe 14
Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ANA ZATON WUTA A MAƘERA......🔥
✒️IBNATU-UMAR ✒️
Page 23&24
Abdulkarim Kurfi shararren dan kasuwa ne, mai tarin ilimin addini, bai yi wani zurfi a boko sosai. Amma yanason ilimin boko, hakan yasa yayi ma kanshi alƙawari zai nemi kudi tukuru yayanshi suyi karatun boko dana addini mai zurfi.
Yataso a wajen Malam Adamu Kurfi, duk da bashi ya haifeshi ba. Dan shi kanshi tsintar shi yayi yana jinjiri. Da yake matar malam Adamu bata da kirki hakan yasa kwata-kwata Abdulkarim bayajin dadin zama da ita. Amma kwata-kwata bai taɓa nuna ma Malam Adamu balle ya kaiga gayamai dan mutum ne mai hakuri da kuma zurfin ciki.
A haka ya taso cikin tsangwamar ya'yan gidan da kuma mahaifiyarsu.
A na haka Allah yama Malam Adamu rasuwa, sunji mutuwarsa sosai musamman Abdulkarim da bai da wanda zai kira nashi a yanzu. Aka yi rabon gado, kuma kamar yadda kowa ya sani shine, Abdulkarim baida gadon Malam Adamu saboda ba dan shi bane na cikin shi.
Ana watse wa daga sadakar bakwai, Matar Malam Adamu ta koreshi. Korar kare, tace kuma kar ya sake tako kafa yazo inda suke. Dama yasan hakan na iya faruwa, amma duk da haka abin ya mai ciwo.
Koh tsinken shi basu bari ya dauka ba daga shi sai kayan jikinshi.
Allah ya taimake shi dama yana zuwa kasuwa, toh sai yake tara kudin aikinshi a wajen Alhajin da yake mai aiki.
Yana zuwa kuwa ya amshi kudin shi a wajen Alhajin kudin sun kusa dubu ɗari a wannan lokacin. Duk da cewa Abdulkarim bai wani manyanta ba a alokacin da kwata-kwata shekararshi 20. Amma yayi tunanin ya fara neman na kanshi da wannan kudin.
Tasha ya tafi ya hau motar Kano dan suna yawan zuwa cen da marigayi ya saro kaya.
Babu kalar wahalar da Abdulkarim bai sha ba Kano wajen neman na kai. Amma da yake Allah ya dafa mai, komai ya taɓa cigaba yake yi. A cikin shekaru biyar Abdulkarim yazama ɗaya daga cikin sanannu a Kantin Kwari.
Shekaru naja dukiyar Abdulkarim na daɗa albarka, ya zamana har waje yana zuwa ya saro kaya.
A hankali a hankali ya fara buɗe wasu shagunan yana saka amintattu na kula mai dasu.
Ana cikin hakan hankalinshi ya karkata kan harkar hatsi, wannan shine sanadiyyar buɗe A.K GROUP. Wanda ada yake Abdulkarim Kurfi Company. Daya baya ne ya koma Abdulkarim. Khadijah Group. A.K Group.
Company ya bukasa, har packaging hatsi suke yi suna fitar dashi waje. A hankali shima ya samu karɓu. Cikin shekaru goma Abdulkarim ya zama mai kudin gaske.
Dattijon da Abdulkarim ya bama ajiyar kudi a cen Katsina shine ya zamo mai kamar uba, yake bashi shawara kuma yake jibantar lamuransa.
Kamar ko yaushe duk karshen wata yana zuwa wajen baba dattijo. Shiryawa yayi tundaga Abuja har Katsina yaje wajen BABA DATTIJO. Gaishe yayi, yasa yara suka fara shigo da abubuwan arzikin daya taho mai dashi. Fura mai sanyi yasa aka kawo ma Abdulkarim. Godiya yama Baba ya tankwashe kafafunshi ya fara shan furar. Abdulkarim cewar Baba yana kallonshi. Na'am Baba yafaɗa yana maida hankalinshi kan dattijon. Abdulkarim Allah ya bada abubuwa da dama da mutane da yawa suke nema basu samu ba. Amma kasani hakan bashi ke nufin Allah bazai jarabce ka. Allah yana jarabta mu ne mafi akasari da abinda muka fiso dan ya kwada karfin imanin mu. Idan hakan yafaru dakai ka tuna waɗannan kalaman nawa.
Nagode Baba In Sha Allah zan rike. Kuma har kullum bazan fasa gaya maka ba, kayi Aure, kayi Aure. Abdulkarim Aure shine cikin mutum. Shi zai ƙara maka daraja. Sosa keya yayi kamar kullum yau ma ya haka ya kuma cema Baba Dattijo. Aure lokacine.
Suna nan zaune, wata yarinya mai kimanin shekaru sha takwas ta fito sanye da hijab dinta. Durkusawa tayi ta gaishe shi ba tare data kalli inda yake ba. Baba ina wuni tafaɗa tana kallon Baba Dattijo. Lafiya lau yar albarka. An dawo kenan daga makarantar. Eh Baba tafaɗa tana murmushi. Tashi ki shiga ciki toh. Tashi tayi a nutse ta wuce cikin.
Da kallo Abdulkarim ya biya, kwata-kwata ya mance ma a gaban wa yake. Tun da yake bai taɓa kallon ya mace ta birgeshi ba kamar wannan yarinyar. Kallo ɗaya ya mata ta shiga ranshi.
Murmushi Baba Dattijo yayi, yayi gyaran murya. Kunya ce ta rufeshi yayi murmushi kawai ya dauke kai. Baba na dauka ba yara a gidan, ina kasamo yarinya karama. Yar wajen ɗana ne dayarasu kwanaki Abdullahi. Kasan dama hannun shi take da yake uwar ta rasu tun tana karama.
Baba toh....sai kuma yayi shiru yana sosa keya. Murmushi Baba yayi yace toh mai? A'a Baba babu komai yafaɗa yana murmushi. Kafaɗa karkayi nauyin baki dai cewar Baba yana gutsirar goranshi.
Baba zaka bani ita? Harararshi Baba yayi yace kaya ce ai jikar tawa da zan baka. Murmushi yayi dan yasan halin Baba da tsokana. Baba ina nufin zaka bani aurenta.
Gyara zama Baba yayi ya dan haɗe fuskar shi kaɗan, ganin haka yasa Abdulkarim gane cewa magana mai mahimmanci baba yake so yin.
Abdulkarim! Na'am Baba yafaɗa yana sauke idanunshi ƙasa. Ga Khadijah nan amana a hannunka, ka sani marainiyace ba uwa ba uba. Idan har auren ka da ita ya tabbata kai ne gatanta. Ka rike ta amana, karka ci amana. Kar kaci amana, Kar ka ci amana. In Sha Allah yafaɗa cikin sanyin jiki.
Shikenan bari na mata magana na turo maka ita ku dai-daita.
Baba na shiga Khadijah ta fito, zama tayi nesa dashi ta gaishe shi. Amsawa yayi yana kallonta. Allah ya mata baiwar kyau, dake fisgar mutane. Masha Allah yafaɗa a ranshi.
A fili kuwa hira ya dinga janta dashi akan karatunta nan kuwa yaga ta biye mai, hakan ne yasa shi ya gane cewa tana son karatu. Cikin hirar sune ya gane cewa ta gama sakandari.
Sun dade suna hira ganin lokaci na tafiya, yasa shi tashi zuwa motar shi bayan yace mata yana zuwa. Waya ya dauko sabuwa mai kyau da tsada ya bude ya saka daya daga cikin sims din shi wanda ba'a sanshi dashi ba.
Ya bata yace ta saka charge idan ta cika ta kunna zai kirata. Kin amsata tayi duk yanda yaso ta amsa taƙi. Khadijah nifa sonki nake da aure bawai cutar dake zanyi ba, yafaɗa cikin rashin jin dadin abinda tamai.
Ganin yadda yaji ba dadi yasa tace mai, Baba zai min faɗa shiyasa naƙi karɓa ba wai dan ina tunani zaka cutar dani ba.
Sallama sukayi yace tama Baba magana, wayar ya bama Baba yace a bama Khadijah baba yace sam a'a sai dai idan ya aure ta yabata a gidanshi. Sai sa ya nun ma Baba ɓacin ranshi sannan ya yadda ya amsa yace zai bata.
Kwata-kwata Abdulkarim bai boye wa Khadijah wayeshi ba, ya gaya mata shi maraya ne, ba'a san iyaye shi ba. Hakan yasa ta ƙara tausayinsa, sai kuma a hankali tausayin ya koma so.
Watan Khadijah da Abdulkarim uku da haduwa aka daura aurensu.
Ba'a yi wasu yan kai amarya ba, shi ya dauki matarshi suka tafi Kano daga kuma suka hau jirgi suka taho Abuja.