← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 50

Sashe 13

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Mu haɗu a next page 📃📃📃

ANA ZATON WUTA A MAƘERA......🔥

✒️IBNATU-UMAR ✒️
Page 21&22
Ajiye motar yayi ya fice, waya yayi driver yazo ya dauke shi. Ina zamu sir, Airport zaka kaini. Kiran waya yayi, in buƙatar tafiya saudi nan da minti goma yana gama faɗin haka ya kashe wayar.
Kusan awa ɗaya suna jiran kiran daga likitar da zata duba Ameerah amma shiru. Na tsani wulakanci wallahi, nafasa ganinta cewar Ameerah tana haɗe rai... Kirane ya shigo wayar Nisah cikin sauri ta dauka. Gaisawa su kayi da likitan tace sanda aka aiko da sakon tana O.R ne shiyasa, suzo yanzu dan anjima kaɗan zata tashi.
Godiya ta mata ta kashe wayar, da kyar ta samu Ameerah ta yadda suka je, dan da tace bazata taje ba dan batason wulakanci.
Parking Nisah tayi da yake ita ta tuƙa motar. Saukowa sukayi, suka shiga cikin babban asibitin. Reception sukaje, Nisah na tambayar receptionist din office din Dr. Aisha Humaira Jikamshi. Tambayar su tayi, suna da appointment suka ce mata eh, duk da haka sai da ta bincika. Tsaki Khadijah tayi yafi cikin kwado, nuna masu hanyar office din tayi.
Mantawa tayi ta gaya masu tana break ne yanzu, sai nan da minti goma zata fara ganin patient. Kallon kofar da'aka rubuta Dr. AISHA HUMAIRA JIKAMSHI sukayi. Zasu yi knocking kawai suka ga an buɗe kofar kaɗan amma ba'a fito ba. Nidai Mummy kawai kizo muje musha ice-cream, Khadijah karki dameni ina da patient na gaya maki, ni bansan wayace a kawo ki nan ba. Zan kira Muntarin inji, Mummyy karki kirashi nina nace kince ya kawo ni nan, a fusace ta juya ta riko yarinyar tace ban hanaki karya, Mummy toh.... bige mata baki tayi tace ina magana kina magana saboda na zama sa'ar ki? Baya taja tana gunguni, hannu ta miƙa zata riƙota kawai taga an shiga tsakaninsu. Bata ga fuskar Ameerah ba da yake ta bata baya, rungume yarinyar tayi, sai da yarinyar tayi shiru sannan ta cirota a jikinta. Laa Beautiful Aunt tafada tana murmushi, kallon yarinyar tayi tana tunanin inda ta santa. Ganin haka yasa yarinyar cewa Aunt a school dinmu na ganki a playground. Ohhh cewar Ameerah tana murmushi, how are you cutie,am fine tafada tana murmushi. Kallon ikon Allah Dr. Jikamshi ta tsaya yi, excuse me tafaɗa tana kallon Ameerah. Juyowa Ameerah tayi sai da ta girgiza da ganin fuskar Dr. Jikamshi amma sai tayi fuska. What? Is this how you treat children? Kina likita kina cin zalin yarinyar tafaɗa tana nufarta. She is my daughter cewar Dr. Jikamshi tana kallon ikon Allah...and so ? Dan yarki ce sai kici zalinta, duk yadda taso Ameerah ta saurareta taƙi.
Zama tayi a kujerarta ta tsaya tana kallonta, tana tunanin abubuwa da dama da suka shuɗe.
Murmushi kawai takeyi tana kallon Ameerah dake mata masifa kamar zata daketa akan yarta. Ita kuma yarinya na gefe tana ta zuba murmushi.
Nisah tace calm down Ameerah itace likitan da zata dubaki fah? Banso tafaɗa tana haɗe rai. Well it's your choice cewar Dr. JIKAMSHI tana murmushi, juyawa Ameerah tayi zata fita. Tace amma babu likitan dazai dubaki cikin asibitin nan, kuma no one is as good as me. Juyowa Ameerah tayi ta fuske kawai ta zauna akan kujerar patient din.
Fita Nisah tayi ta basu waje, zama Ameerah tayi tana cika tana batsewa, murmushi Dr. JIKAMSHI tayi tana danna computer sosai take ƙoƙarin danne dariyarta. Name ? Tafaɗa tana kallon Ameerah. Khadijah AbdulKareem Kurfi. Woww namesake cewar yarinyar nan tana tsallen murna. Ammi shiga ciki cewar Dr. Jikamshi fuskarta a daure. Tama mance da yarinyar na office din. Sunne kai tayi ta wuce dakin dake cikin office din.
Miye matsalar ki, irin taki cewar Ameerah tana kallon Dr. JIKAMSHI, kallon ban gane ba tama Ameerah. Toh gani nayi idan ba mai psychiatric problem ba waye zai dinga bullying yar yarinya kamar Khadijah. Murmushi Dr. JIKAMSHI tayi tace i hope kina ma yaranki faɗa, that's not your business cewar Ameerah. Toh ya akai Khadijah ta zama business dinki......cuz shiru tayi batasan mai yasa ba take feeling tanada wani irin bond da yarinyar. Cuz....cewar Dr.Jikamshi tana kallonta, cuz she is a baby, tafaɗa tana kallon Dr. Jikamshi murmushi kawai tayi tace miye ke damunki?
Gyara zama tayi tace taya kikasan inada yara? Murmushi tayi tace kowa ya sanki a social media. Miye ke damunki? Ta kuma maimaita mata maganar. Bansani ba nima am just hearing and seeing things, kamar na haukace. Daman cen a haukace kike cewar Dr. JIKAMSHI. Mai kika ce? Cewar Ameerah tana kallonta, bance komai ba tafaɗa tana murmushi. Bayani Ameerah ta mata tiryan-tiryan tun daga sanda ta fara jiye-jiye da gane-gane. Shiru Dr. Jikamshi tayi cikin damuwa tace zata mata MRI tukunna.
Bin bayan Dr JIKAMSHI tayi suka fita a office din, kallon Nisah dake waya tayi tace sai mun dawo. Okay 👍.
Duk inda suka wuce gaishe da Dr. JIKAMSHI akeyi cikin girmamawa. Ita dai Ameerah ta haɗe rai har suka isa wajen yin MRI (hoton ƙwaƙwalwaa) din.
Cire gyalenta Ameerah tayi kamar yadda wacce za tayi MRI din tace tayi.
Rasa inda zata ajiye tayi, murmushi Dr. Jikamshi tayi ta amshi veil din, ta rike tana tsaye tana kallo suka shigar da Ameerah cikin Machine din.
Cikin mintina ƙalilan suka gama, aka fito da ita. Saukowa tayi ta yatsina fuska ban gyalena ai ba naki bane koh tafaɗa tana fisge gyalen. Murmushi Dr. JIKAMSHI tayi, ganin abubuwan da take ta ma Dr. Jikamshi yasa mai yin scan din cewa amma Dr sister dinki ce koh? Murmushi kawai Dr. JIKAMSHI tayi batace komai ba. Allah ya kiyaye sukaji muryar Ameerah tana faɗa ta fice. Bin bayan ta tayi, suka koma office dinta.
Results din zai dauki lokaci zaki jira ne koh kuma zaki dawo gobe? Zan jira tafaɗa tana karewa office din kallo.
Kinada wani medical history? Cewar Dr. Jikamshi tana kallon Ameerah. Asthma sai kuma VSD cewar Ameerah dake kallon kofar ɗakin da Khadijah take. VSD kina nufin ventricular septal defect? Cewar Dr. JIKAMSHI tana kallon Ameerah, whatever you call it, that's it.
A bayanin da kika min harda stress ke causing maki wannan gane-gane amma bari result din ya fito mu gani.
Khadijah ce ta leƙo tace Mummy yunwa nakeji, maganin mara kunya kenan kinga da ba kiyi karya ba da an kaiki gida kina cen kinci abinci kin huta......mummyyy tafaɗa tana ɓata fuska. Zo cewar Ameerah tana murmushi, da gudu tazo duk hararar da Dr. JIKAMSHI ke mata taƙi bari su haɗa ido. Are you hungry tafaɗa tana leƙa fuskarta. Eh cewar Khadijah tana murmushi. Wayarta ta ciro a jakarta ta kira Mukhtar tace ya mata take away tana asibiti. Kuma karya zo da kowa. Toh yafaɗa cikin GIRMAMAWA bayan ta gayamai sunan asibitin.
Kallonta tayi tace Baby yanzu za'a kawo maki abinci. Ki dena harararta, cewar Ameerah tana kallon Dr. JIKAMSHI. Daga ke har ita idan naga dama zan hada ku in zane ku bama harara kaɗai ba.
Saboda kuɗin nawa ne! Kalmar nawa ne din datace ya daki Ameerah sosai amma sai ta fuske, am not yours, you're saboda ke patient dina ce tafaɗa tana kallonta.
Mummyy karki daki beautiful Auntie cewar Khadijah. Banza tayi da ita bata kula taba.
Ba jimawa results din ya fito, magunguna ta rubuta mata, daidai Mukhtar na zuwa, amsar take away din tayi ta bama Khadijah ta shafa kanta.
Katin ta Dr. JIKAMSHI ta bama Ameerah tace ki kirani idan da wata matsala. Sannan nan da kwana bakwai idan kin shanye magungunan ki dawo.
A bangaren Ruhaan kuwa bai samu yayi tafiyar ba, amma kudiri a ranshi jibi zai tafi.
Washegari kamar kullum yazo aiki duk da weekend ne.
Su Zayn ne suke ta fito da kayan barbecue. Hada abin sukayi basu iya kunnawa ba, sanin bazasu iya din bane yasa Ameerah ce masu indai suka haɗa suzo su kirata zata masu gashin kaza a kan barbecue grill.
Rokon Ruhaan sukayi ya kunna masu, kunna masu yayi, suka koma ciki suka kwala ma mata kira tazo ta masu.
Saukowa tayi dama tayi marinating kajin niyyar ta tayi amfani da air fryer sukace a'a shine tace suje su kunna.
Daurawa tayi Ruhaan na gefe yana kallonsu, suna hidimarsu.
Tashi yayi yaje yayi sallah ya dawo, dai-dai itama Ameerah tana dawowa. Tana duba kajin su Zayn na gefe suna wasan su.
Kallon pipe din gas din yayi yaga kamar a yanke yake. Koda ya kura ma abin ido kuwa hakan take. Da gudu ya taho yana ta ku matsa, ku matsa. Saurin tashi su Zayn sukayi dayake sun fi kusa dashi. Sun ji mai yace, Ameerah kuwa kwata-kwata bata jin shi.
Tureta yayi a wajen dai-dai abin na exploding, wuta ta naso fuskarshi. Arghh 😣 yafaɗa yana dafe fuskar karyar daya saka data fara konewa.
Cikin sauri masu aikin gidan suka fito aka fara yunkurin kashe wutar. Garden din ya nufa ya cire fuskar yana shafa inda ya kone a gefen kasumbar shi. Juyawar da zai yi yaga Ameerah a bayan shi. Kasa motsi tayi saboda ganin fuskarshi. Ruhaannnnn tafaɗa cikin ɗaga murya tana binshi da wani irin mugun kallo. Mai ya kawo ka nan? Kazo ka saba da yarana sun shaƙu dakai da fuskar yaudara? Mai yasa kake ƙara min proving a koh da yaushe cewa kai mayaudari ne!! Tafaɗa idanunta na chanza launi. Ki saurareni.....baka da abin faɗa min leaveee tafaɗa a fusace tana kallonshi. Imann yafaɗa yana kallonta, kar sunan nan ya ƙara fitowa daga bakin ka. Leave!! Naji zan tafi amma kinsan kinmin ba dai-dai ba koh? Mai na maka tafaɗa tana dauke idonta daga kan fuskarshi, ya'ya na kika haifa ba tare dana sani ba, kika basu sunan wana ƙato, yafaɗa a fusace. A firgice ta kalleshi tace waya ce maka ya'yan kane, murmushin kin raina ma kanki hankali yayi yace koh makaho ya kallesu, yasan jinina ne. Why, mai yasa Imaan, baki gayamin ba? Ba yaran ka bane tafaɗa tana dauke idonta daga kanshi, Baki iya karya ba Imaan ban sanki da karya ba. Nagaya maka yara ba naka bane ka kayale ni, tafaɗa a kausashe tana hawaye. Imaan banga mai na maki da zaki tsane ni haka ba, ni ya kamata in dinga jin haushin ki Imaan...kin mata abinda ya faru da Duaa....Imaannn yafaɗa a kausashe, Mohammad Ruhaan tafaɗa tana kallon cikin idanunshi da wata irin ƙiyayya. Kamar basu bane suka so juna kamar bazasu rabu ba. Banson komai daya danganceka banson tuna komai daya shafeka. Ruhaann kamin abinda bazan taɓa iya yafe maka ba. Just leaveee me alone. Ka kyaleni da ya'yana. Akan mai bayan nima ina da hakki akansu.....
Tushen Labari.
Asalin....
Mu haɗu a next page 📃📃📃
Miye Alaƙar dake tsakanin Ruhaan da Ameerah?
Miye Alaƙar dake tsakanin Hajiya Hamdiyya da Ameerah?
Shin da gaske su Zayn ya'yan Ruhaan ne koh na Mahmud?
Chapter 13 · 0% Book details