Sashe 10
Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Page 15&16
Muje karsu binneta ban ganta ba, tafaɗa tana mikewa kamar mai taɓin hankali, so take tayi kukan koh zata ji sauki a ranta amma ta kasa. Aunty Mami ta rasu? Ganin abin take kamar wasa, Innalillahi Wa Inna Ilayhi Raji'un, Nisah duk wayanda suke da mahimmanci a rayuwa sunata nisantar rayuwa, ni kadai zan rayu a DUNIYAR MU? Ban rasa komai na jin dadin rayuwa ba, amma na rasa mutane masu daraja a rayuwata.
Tafe take kawai tana zance kamar wacce ta zare, Nisah na binta a baya, ganin ta nufi gate yasa Nisah rikota tasata a mota. Shiru tayi sai ajiyar zuciya take yi amma ta kasa magana, kallon Ruhaan tayi tace ya kaisu gidan Aunty Mami.
Parking yayi suka sauka suka shiga ciki, duk wanda ya kalli Ameerah sai ya tausaya mata, sanda taga gawar Anty Mami, zauce wa ne kawai ba tayi, ji take kamar uwarta mahaifiya ce ta rasu.
Rungume gawar tayi tana mata addu'a, duk mutanen dake sauraren addu'ar da take ma Aunty Mami suna jin raunin dake cikin muryarta. Kuka takeson yi amma ta kasa sai ajiyar zuciya kamar ta haɗiyo zuciya haka take ji.
Kan a tafi a binne Aunty Mami ma mutuwarta ta yaɗu a social media da duniya. Duk inda ka duba Instagram, Tiktok kai harda whatsapp status. Labarin mutuwar A'isha Idris Kurfi ake yi, kowa baida abin faɗa akanta illa alheri. Kasancewarta mace mai hidima ga musulunci da musulmai.
Mutane da yawa sunji mutuwarta, haka aka tafi binneta. Tayi jama'a sosai.
Mahmud na jin mutuwar shima yazo gidan, sosai hankalin shi ya tashi ganin yadda Ameerah ta zabge ta rame a yini ɗaya. Duk yanda yaso lallaɓata koh ruwa ta sha taƙi. Kullum anan Ameerah ke yini amma da dare Mahmud zai zo ya dauke ta su koma gida.
Ana yin uku yan uwa suka watse, dama ba yan uwan kusa bane. Da duk yan uwan su na jiki babu su, duk sun mutu. Ammi ma sau biyu tana zuwa gidan gaisuwar, ganin ta nema yasa Ameerah ta dan iya cin abinci.
Mutuwar Aunty Mami yasa duk wata masifar Ameerah babu, ga wani irin sanyi data yi. Ga miskilancinta daya ƙaru. Yau kimanin kwana ashirin da biyar kenan da rasuwar Aunty Mami , gabaki ɗaya Ameerah ta zama wata iri, aikin ma bata zuwa. Mukhtar ne ke kokarin ganin komai ya tafi dai-dai kafin ta dawo hayyacinta.
Zazzaɓi ne ya rufeta misalin karfe uku na dare, buɗe idanunta da suka mata nauyi tayi, kai hannu tayi koh zataji Mahmud amma bataji alamar mutum a wajen ba.
Tashi tayo zaune ta a dafe kanta dake barazanar tarwatsewa saboda wani irin mugun ciwo da yake mata.
Fitowa tayi ta shiga ɗakin Mahmud dake kallon nata, nan ma baya nan, har zata fita taji motsi a wajen closet din shi, sliding tayi a hankali, dafe saitin zuciyarta tayi saboda yadda ta buga da karfe. Sauraren abinda Mahmud ke cewa ta cigaba dayi, ai bacci take yanzu wallahi bazata sani ba. Ki nuna min, toh bara nayi switching video call, a'a tsoron mai kike ji abinda a video call zamuyi ba zina bace aii. Hasbinallahu Wani'imal Wakil tafaɗa tana dafe bangon wajen, Sex video call Mahmud keyi? Innalillahi Wa Inna Ilayhi Raji'un.
(Note: Babu inda aka ce sex video call halal ne a muslunce, zina zina ce, zina harta ido akwai, abinda da yawa matasa da yan mata keyi a yanzu kenan, wanda sunsan bai halatta ba, amma suka mai kwaskwarima saboda san zuciyarsu). Hanyar fita daga ɗakin tayi, jiri ne ya ɗebeta ta bige vase din dake gefen bakin kofar.
Saurin fitowa yayi yana gyara zama wandonsa, babe lafiya yafaɗa yana taro Ameerah dake shirin faɗuwa, you're weak mai yasa kika tashi. Kallonshi tayi wai irin kallon kyama da sai da yasha jinin jikinshi, Ameerah relax karki nuna mai kin gane, there is more to this, kuma in kika nuna mai kin gane bazaki taɓa gano sauran abubuwan da yake yi ba.
Kallo kawai ta bishi dashi ba tare data ce mai komai ba.
Mai kike so yafaɗa yana kallota, ruwa tafaɗa batare data kalli fuskarshi ba.
Ruwa ya dauko ya buɗe, ya nufi bakinta dashi, amsa tayi maimakon tasha daga hannushi, tasha da kanta.
Sai da safe tafaɗa tana mikewa zata fice, nima yanzu na shigo, zafi ya dameni, wanka nakeso nayi, ina nan zuwa. Cen babu toilet din da zakayi wanka tafaɗa tana tsare shi da ido. A'a nafison nan ne kawai yafaɗa yana murmushi. Tun yaushe kenan? Tafaɗa tana watsa mai wani irin kallo mai tsuma mara gaskiya. Baby wai zargina kike yafaɗa yana ɓata fuska. When did i say that tafaɗa fuska ba fara'a. Baki faɗa ba amma naga alama. Toh tunda ban faɗa ba a dena ƙadar da zancen da bai fito daga bakina ba.
Babeee yafaɗa yana kallonta, hannu ta ɗaga tace sai da safe bansan muja maganar nan, ya zako min da wani irin zance. Na taɓa zarginka a iya zaman mu? A'a yafaɗa yana kallonta. Toh akan mai zaka ce ina zargin ka yanzu? I know you will never cheat, amma kanasani in fara having second thoughts yanzu. Yi hakuri yafaɗa cikin sanyin murya.
Fita tayi ta saki wani irin murmushi da ita kaɗai tasan ma'anar shi.
Tayi mugun mamakin abinda taji, amma bazata yanke hukunci ba tukunna sai tanada hujja.
A bangaren Mahmud kuwa kwana yayi tunanin yasan Ameerah da wayon tsiya, anya bata gane ba kuwa? Kai ina Khadijah nada kishi data gane da bazata yi mai shiru ba. Da wannan tunanin bacci ɓarawo ya sace shi.
Koda ta tashi da safe kiran Daddy Tahir ne ya shigo wayarta. Gaishe shi tayi, yace mata ga address ya tura mata tazo karfe biyu na yamma da duk wani abu na Aunty Mami dake wajenta, ana so a raba gado, kar a barta da nauyi.
Murmushin takaici tayi tace mai toh kawai ta kashe wayar, sai ranta ya ƙara ɓaci kwata-kwata kwana nawa da rasuwarta koh wata ɗaya ba'a yiba har sun fara tunanin gadonta.
Kiran Mukhtar tayi ta gayamai, dan duk inda zata da bata saba zuwa ba, sai sun bincike wajen kafin ta isa.
Misalin karfe biyu Ruhaan yazo a matsayin driver dinta, sanye da baƙaƙen suites dinshi kamar kullum. Buɗe mata yayi ta shiga yaja motar zuwa gidan da za'a yi taron.
Parking yayi ganin Mukhtar a waje da securities su wajen biyar. Ma'am sun hana kowa a shiga a cewar su ba taron siyasa za'a yi ba, rabon gado za'a yi.
Kuma wai bazaki shiga da bodyguard koh security ba. Sai dai a harabar gidan zaki iya shiga da security ɗaya sai driver ɗaya su jiraki a waje.
Anya bazaki koma ba? A'a zanje tafaɗa tana kallon katoton gidan.
Mukhtar be ya shiga ya zauna gefen Ruhaan matsayin driver, shi kuma Mukhtar security.
Parking yayi ya sauko ya buɗe mata, Misss yafaɗa yana kallonta, wani abu kamar pen 🖋️ yasa mata a hannu yace in kina buƙatar inji abinda ke faruwa ki danna blue button din. In kina buƙatar taimako ki kunna jan.
Thanks tafaɗa shigewa ciki, wayar over-over ya kunna. Shiga motar yayi ya zauna gefen Mahmud ya fito da kafarshi ɗaya waje. Mai kake shiryawa ne? Ka fi kowa sanin bazan cutar da ita ba. So sit quietly and watch. Kaii bakasan ina na gaba da kai bane? A shekaru da kuma wajen aiki. Hushh 🤫 bana son hayaniya.
A bangaren Ameerah kuwa ciki ta shiga, wasu mata biyu suka mata jagora zuwa cikin, doguwar corridor cike da securities suka dinga wuce wa har suka shiga ciki, buɗe mata kofar akayi, shiga tayi,tana shiga taji an murza key ta waje.
Kallon kofar tayi sannan ta kalli mutanen dake cikin ɗakin.
Hi hun 💓 cewar Mahmud dake kallonta da murmushi, da mamaki take kallonshi.
Murmushi ya kuma yi yace nazo ne a matsayin muharramin ki.
Hi sister cewar wani saurayi mai kimanin shekaru 33 oppss my bad ashe kince na dena ce maki sister saboda bamu haɗa komai ba, babanki ne kawai ya auri mamana. Kallon Hajiya Hamdiyya tayi sannan ta kalli Daddy Tahir.
Gaisawa sukayi da lawyern Aunty Mami. Wannan safe din wasiyyar client dina A'isha Idris Kurfi ce a ciki, wanda ta bani hannu da hannu, kuma ta shaida min cewa ɗaya daga cikin magadanta nada mukulli. Ciro mukullin da Aunty Mami ta bata Ameerah tayi ta miƙa masu. Buɗewa yayi ya ciro takarda, ni A'isha Idris Kurfi na mallaka ma Khadijah Abdulkarim Kurfi kashi 9 cikin goma na dukiya ta. Banda abinda na mallaka na A.K Group. Sauran kashi dayan ayi rabon gado shi. Sannan duk wata dukiya ta ta A.K group mallakin Khadijah Abdulkarim Kurfi ce.
Bazai yiwu ba cewar Hajiya Hamdiyya tana buga table din gabanta, shares din dana zo nema za'a ce an bama wata.
Murmushi Ameerah tayi ta kalli Hajiya Hamdiyya tace zan iya sanin mai ya kawo ki wajen nan? Dan baki da hurumin zuwa nan. Shares din A'isha zaki siyar min. Bazan siyar ba tafaɗa tana kallonta ido cikin ido. Kallonta Daddy Tahir yayi yace zata bako offer mai kyau what's the use of holding onto it, kin san cewa ko min dadewa sai ta kwance company a wajen. Ohh really i can't wait tafaɗa tana daura ƙafa ɗaya kan ɗaya. Ohh dama ka dauka bata da wasiyya shine kukayi yarjejeni ya akan cewa zaka siyar mata da shares din Aunty Mami. Toh kunyi karya, takarda Hajiya Hamdiyya ta ciro ta kalli wannan saurayin tace Naseer ka saka ta tayi signing koh taƙi koh taso. Danna blue button din pen din da Ruhaan ya bata tayi. Bazan siyar ba, da sauri Ruhaan da Mukhtar suka kalli juna, jin ta kunna abin, 500million da kinyi signing za'a maki wiring kudin account dinki. Bazan siyar ba, Hun kawai ki basu abinda suke so kinga dai bazasu bari ki fita ba sai kinyi signing. Kuma kalli yafaɗa yana nuna mata tab dinshi sun tura D.S.S News Buzz, a firgice ta kallesu, yess you know what that means. Sirrin manyan mutanen dake News Buzz idan ya fita, ke da News Buzz da duk wani na kusa dake kun tashi aiki.
Minti 30 zai kai D.S.S News Buzz, minti goma zai kaiki News Buzz which means you have 20 mins to decide. Zaki bar abinda kika gina na tsawon shekaru bakwai ya ɓaci, saboda wasu shares da koh kwatan darajar company dinki basu yi?. Fisge pen din hannunta Naseer yayi ya kashe. Dif su Mukhtar suka dena jin abinda ke abinda ke faruwa a wajen.
Kallon juna sukayi, akwai matsala cewar Ruhaan yana kallon Mukhtar, murmushi yayi yace kai kanka baya ja ne, maganar kuɗi sukeyi maƙudai duk da Miss ta yadda da mu, amma bazata bari muji sirrin taba ai. Shiru yayi yana tunani aranshi " Khadijah bazata taɓa saida abin wanda keda mahimmanci a wajenta koda bai da daraja, sannan ambition dinta is not something that can't be bought".
Sauka yayi ya buɗe booth din babu komai daga guduma sai kuma lema bakinta mai shegen tsini. Lemar ya dauka ya nufi ciki, binshi Mukhtar yayi yace karka shiga, zaka rasa aikin ka wallahi. Babu abinda Miss ta tsana kamar shishigi, ta fison ta bada umarni kafin a aiwatar da komai.
Banza yayi mai ya shige ciki, corridor din ya nufa, saurin nufoshi securities din su kayi.