← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 50

Sashe 42

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Are you ok? Cewar Ruhaan yana dafata. Yes, i am tafaɗa tana ƙoƙarin maida hawayenta. Rungumeta yayi yace it's fine komai yazo karshe.
Toh mu haɗu a next page 📄📄📄
ANA ZATON WUTA A MAƘERA....🔥
✒️IBNATU-UMAR ✒️

PAGE 65&66
Likitane ya fito yace masu ansa ma Ammii jinin, kuma Alhamdulillah ta fita a critical situation.
Gode ma Allah sukayi, kallon Humaira Amira tayi tace i told you, she will be fine tafaɗa tana rungumeta.
Zuwa sukayi suka ganta, an naɗe mata kai da bandage tana bacci kamar ɗazu.
Fitowa sukayi, Humaira tace su Amira suje gida.
Tafiya tayi da Zayn da Zaid. Tuƙi Ruhaan yake amma hankalinshi nakan Amira dake danne danne a iPad ya tabbata aiki take yi.
Jin yayi parking yasata ta ɗago idanunta, ganin Studio dinshi yasata kallonshi da mamaki.
Sauka yayi ya buɗe ma Zayn da Zaid suka shiga ciki, ganin sunyi gaba yasa ta sauko tabi bayansu.
Koda ta shigo basa parlour, zama tayi ta cigaba da aikin da take.
Cen sai gashi ya sauko dasu, ya masu wanka yasa masu sabbin jallabiya. Mammi kin gani cewar Zayn yana shafa rigar. Kayi kyau tafaɗa tana cigaba da aikin da takeyi. Numfashin da taji a gefen wuyanta yasata lumshe ido ta kuma buɗe su. What do you want? Tafaɗa ba tare data juyo ba, dan tasan waye. I want my wifee. Stopeettt please tafaɗa tana tureshi. Dariya yayi yace mai kike yi. Look tafaɗa tana nuna mai ipad din. Are you sure yafaɗa yana zama a gefenta. I have to do it. Banason in yadda da kowa akan wannan aikin, dan abu ne daya shafi Abbi.
I will support you baby yafaɗa yana sumbatar goshinta. Rungumeshi tayi tace Thanks. Uncle Moh why are you hugging Mammi? Cewar Zayn yana kallonsu, shi kuwa Zaid mamaki ya hanashi magana.
Uhmm bara....shiru ina magana da Mammi ne cewar Zayn yana haɗe rai. I can explain cewar Ameerah tana murmushi. Am all ears cewar Zayn yana kallon Amira.
Uhmm he, hee, hee...shin miye wai Mammi cewar Zaid cikin kuluwa. Am her husband cewar Ruhaan yana kallonsu. Kallon juna Zaid da Zayn sukeyi sukace miyyeee? Waittt Mammi Daddy fah? Kallonta Ruhaan yayi idanunshi har sun fara chanza launi, mikewa yayi ta ruko hannunshi ta zaunar dashi. Tace he is your father. Shine mahaifinku ba Mahmud ba. Lumshe idanunshi yayi ya jingina da kujerar.
Rike hannun shi tayi tana matsawa a hankali. Tamika ma Zayn dayan hannunta, ƙarasowa sukayi. Mammi bangane ba, what are you saying? Toh waye Daddy?
Okay listen to me. Ni da Dad dinku tafaɗa tana nuna masu Ruhaan, mukayi aure. Muka haifi sister dinku and we separated and I was pregnant with you guys then. And... cewar Zayn yana kallonta. Sai mukayi aure da Mahmud. Ohhh that means he is our step dad? Cewar Zayn, gyaɗa mai kai Amira tayi tace yes. It's fine I don't really like that ex husband of yours cewar Zaid yana murmushi. But i like him cewar Zayn yana ɓata fuska. Kaje ka zauna dashi ni ina tare da Father cewar Zaida yana rungume Ruhaann. Nima inason Father kuma ina son Daddy.
Murmushi Amira tayi tace ku zauna a nan kuyi wasan ku. Ta riko hannun Ruhaann da idanunshi ke rufe har lokacin taja shi daki.
Zawjj tafaɗa tana taɓa fuskar Ruhaan, buɗe idanunshi da sukayi jajir yayi. Saurin dauke idanunta tayi, juyoda fuskarta yayi yace look ke kika ja ai. Nasan ranka ya ɓaci but ba laifi na bane. Kai kamin boye-boye ai... that's why you gave them a new father? I didn't karka samin magana a baki. Kuma ai na masu bayani yanzu kaji. Nima kimin nawa bayanin ya faɗa yana tura kofar. Wha..tt.. tafaɗa tana tashi janyota yayi ta fado jikinsa yace where are you running to? The kids tafaɗa tana nuna kofar. Let them be, babu abinda zai samesu a gidan nan yafaɗa yana sata a jikinsa. Ina zuwa kaji Yayana tafaɗa tana ɓata fuska dariyar data taso mai ya haɗiye yace Yaya? Yau Baby Girl kece min Yaya? Ikon Allah. We are just going to cuddle ba wani abu ba yafaɗa yana jan hancinta. Ni ban yarda da kai ba kai ɗin? Indeed you know me yafaɗa yana pecking goshinta jan bargon yayi ya rufesu.
Daure da towel ya fito daga toilet ya nade Ameera cikin katon towel.
A kan gadon ya direta, ya hau shafa mai. Jin knocking yasashi lekawa yana kallon Zayn dake kallonshi. Father ina Mammi? Tana zuwa yanzu yafaɗa yana mai murmushi. Juyawa Zayn yayi ya tafi. Kallon Ameera yayi yace hala anan kikeson ki kwana? Harararshi tayi tace wallahi saina rama. Are you.....🤭? Yafaɗa yana fashewa dariyar mugunta. Karka ƙara min magana tafaɗa tana mikewa duk da zugin da kafarta ke mata.
Kayanta ta saka ta fito daga dakin. Zayn ne yace Mammi bacci kikayi? Eh tafa tana haɗa tarkacenta a cikin hand bag dinta.
Fitowa yayi yana zuba kamshi, fuskarnan a daure kamar kullum amma da ka ganshi, kasan yana cikin farin ciki.
Muje in kaiku yafaɗa yana haɗiye dariyar dake cinshi. Mammi ni a wajen Father zan kwana babu school gobe cewar Zaid yana riƙo hannun Ruhaan. Banza tayi dasu ta fice waje, binta Zayn yayi ya dauki jakarta. Buɗe mata kofa Ruhaan yayi ta shiga, ya buɗe ma su Zayn baya, sannan ya zagya ya shiga wajen tuki.
Parking yayi a kofar gidan yace bazaki bari inyi jinya ba? Wata muguwar harara ta watsa mai. Sauka tayi, Zayn ya bita. Leƙowa Zaid yayi ta window yace Mammi sai da safe. Banza tayi dashi ta shige ciki.
Murmushi Ruhaan yayi, yayi reversing motar ya fice a gidan.
Mall yakai Zaid ya sai mai kayan sawa dana wasa. Duk abinda Zaid ya dauka sai ya daukar ma Zayn. Kallon Ruhaan yayi yace Father kallonshi Ruhaan yayi, shiru yayi sai kuma yace it's fine. Rage tsayinshi Ruhaan yayi yace who am i to you? My Father yafaɗa yana murmushi. Toka tambayeni duk abinda kakeso zan maka. Okay yafaɗa yana murmushi. Ina son ball but Mammi ta hana. Uhmm let it be our little secret. Yehh yafaɗa yana tsalle murna.
Sai bayan Maghrib suka gama yawonsu dan a hanya ma sukayi sallar. A bakin Wani haɗaɗɗen gida yayi parking. Horn yayi mai gadiya bude masu gate. Saukowa yayi ya buɗe ma Zaid ya sauko. Wowww Masha Allah yafaɗa yana kallon gidan. Murmushi Ruhaan yayi yace you like it? Noo..why cewar Ruhaan yana kallon shi. I love itt!! High five tafi sukayi suka shiga cikin gidan. Mai gadin ne ya shigar da kayan parlourn farko. Sama suka wuce, mai zakaci? Uhmm mashed potatoe and steak.
Apron Ruhaan ya saka, ya shiga kitchen Zaid na zaune yana kallonshi ya gama girkin. Loma ɗaya ya kai baki, ya lumshe ido yace best bestt. Murmushi Ruhaan yayi yana jin wani irin farin ciki.
Wayar ya dauko ya kira Amira dake asibiti ta koma ta amshi Humaira taje gida tayi wanka.
Whatt? Murmushi yayi yace on your data. Video call ya kirata ya nuna mata Zaid. Hi Mammi yafaɗa yana washe hakora kamar ba Zaid mara fara'a ba. Mammi ke baki iya girki ba. Amma Father ya iya sosaiii. It's so delicious 😋. Congratulations 🎉 tafaɗa tana hararshi. Kaii Mammi am sorry toh a kinga baki taɓa mana girki ba. Sai dai cereal 🥣 kika haɗa mana.
Mammi has Pyrophobia cewar Ruhaan yana kallon Zaid. Oppss sorry Mammi bada sane na bane. Dariya tayi tace wannan wace irin Hausa kake yi kuma? It's fine sweetheart.
Matsawa gefe yayi yace how are you doing? Ban sani ba tafaɗa tana harararshi. Wannan hararar ta miye wai? Kinason idanun su faɗo ne kimin asara? Murmushi yayi tace am still angry with you! Bawani dadin baki da zakamin.
Toh bama Sister ta tayani baki hakuri. Humaira data fito daga wanka yanzu Amirah ta kalla tace bari ta gama, abu takeyi. Tom zan gaya mata laifin da kikace na maki, ta baki hakuri. Better kuma...whatt tafaɗa tana kallon shi dan sai yanzu ta gane mai yake nufi. Muhammad Ruhaan tafaɗa cikin ɗaga murya. Baby Girl yafaɗa yana murmushi. Sai da safen ka. Okay take care, a kula da abuna. Gerrouttttt Abeegg tafaɗa tana kashe wayar.
Kallon Ammi dake kwance har yanzu bata farka ba Amira tayi sannan ta kalli Humaira tace sister kizo kici abinci. Let's talk about this first Amii. Ina kika je ɗazu? Mukarram yaje gida yana ta jiran ki, ki bashi abu ya kawo min...Muna Studio din Ruhaan cewar Amira tana saurin katse Humaira. Allow me to die noowww! Kina neman birne ni da raina.
Na kira ki, Zayn ya dauka yace wai kina... Sisterr tafaɗa tana toshe kunnuwanta. Murmushi Humaira tayi tace ashe dai da gaske ne. Waitt....whatt?
Mai kike nufi? Murmushi Humaira tayi tace babu wanda yace min wani abu, kuma ni ban kira wayarki bama. I just want to catch you, kuma kin faɗa.
Ku dai bi a hankali, cewar Humaira tana murmushi. Kallon Amira tayi kwalla tab cikin idanunta tace bafa ni bace, shine fa. Na shiga uku, kuka zaki min cewar Humaira tana dariya. Daga magana?
Nidai banso cewar Amira tana kwalla. Am sorry toh cewar Humaira tana rungumeta.
Gobe zan shigar da ƙara, tafaɗa tana miƙa ma Humaira wani file. Amsa tayi tagama karantawa ta miƙa ma Amira tace amma i think we should hire lawyers. Amii shekara bakwai kenan rabonki da shiga court room, can you do this? Koda yake basai na tambaye ki, nasan idan kikayi niyyar yin abu zakiyi. Amma nidai dan girman Allah komai zakiyi, include me. Okay sister cewar Amira tana murmushi.
Toh mu haɗu a next page...📄📄
ANA ZATON WUTA A MAƘERA....🔥
✒️IBNATU-UMAR ✒️
Chapter 42 · 0% Book details