← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 50

Sashe 16

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Page 25&26
Anyi suna, yan uwa da abokan arziki, sunzo anci an watse, kyaututtukan da Abdulkarim ya raba ita kanta Aisha sai sa tayi mamaki duk da tasan cewa kyauta halinsa ce.
Sai dai kuma mai, kwana goma da Allah ya dauke Nanah Khadijah, Allah ya mata rasuwa.
Sosai mutuwar ta taɓa su, musamman ma Abdulkarim ita ke daure wa tana rarrashin sa.
Suka cigaba da kula a Aisha.
Bayan kwana bakwai da haihuwar Khadijah ta fara rashin lafiya sosai, asibiti yace suje taƙi tace babu wani abu.
Sauka ƙasa yayi masu aiki duk sunyi bacci. Yaji dadin hakan dama shi bayason suna haduwa shiyasa ma idan suka ma Khadijah aiki suke komawa ɓangarensu.
Tea ya dafa mata, ya hada mata shayi. Biscuits ya dauka ya nufi sama dan yakai mata. Ciwon ya sauka har sun fara bacci Khadijah ta fara kuka, a hankali. Duk ruɗewa sukayi dan sun rasa mai yake damunta, mukullin mota ya dauko suka tafi asibiti.
Kallonsu likitan yayi yace. Babyn ku ma dauke da VSD ma'ana tanada hole ( dan rami ) a zuciyarta. Hakan yasa bugun zuciyarta bazai zama dai-dai dana mutane ba, sannan discomfort kaɗan zata samu ya zame mata matsala.
Ba'a abinda za'a iya yi? Cewar Abdulkarim, Babu gaskiya magunguna zamu bata, bata kai sanda za'a mata aiki ba. Akwai shekarun da zata kai ace za'a mata aiki. Amma nata bai kai ayi ba, barinta haka shine mafi alheri. Amma kar damuwa ta mata yawa. Ku kula koh yawan kuka ba'a son tanayi. In Sha Allah sallamar su likita yayi, jiki a sanyaye suka koma gida.
Kallon Khadijah data zubama babyn ido yayi ya amsheta yace zata zama mai karfin zuciya, zata zama abin kwantance wajen nuna nagarta, zata zama jajirtacciyar ya, mata kuma jajirtacciyar uwa.
Zata zama shugaba ta shugabanci mutane da dama AMEERAH yafaɗa yana kallon Khadijah da idanunshi da suka kaɗa.
Murmushi kawai Khadijah tayi.
Haka suka cigaba da kula dasu, duk wanda ya gansu sai sun birge shi.
Yara suka taso cikin kauna da kuma kulawar iyayensu.
Har suka shekara shidda.
Da farin ciki Alhaji Abdulkarim ya shigo gidan rike da hannu wata mata mai kimanin shekaru 35. Yana ta kwala kiran Khadijah. Saukowa tayi tace nikwa mai ya faru ne kake ta kirana haka. Taji ba dadi sosai ganin shi rike da hannun wata, amma sai ta fuske, murmushi matar tayi ganin kishi a idon Khadijah. Aunty ina wuni tafaɗa tana murmushi. Aunty kuma ai saidai muyi sa'anni cewar Khadijah tana kallonta. Ganin tayi shiru yasa Khadijah cewa bismillah zauna mana. Zama Alhaji Abdulkarim yayi riƙe da hannun matar. Ruwa ta kawo mata da zobo mai sanyin gaske ta koma gefe ta zauna ta haɗe rai. Yar Aljanna cewar Abdulkarim yana kallon Khadijah ganin yadda ta haɗe rai. Ina son sanar maki da magana mai mahimmanci ne, ki bani aron hankalin ki. Ta ina ma zan fara, yafaɗa cikin ɗauki da kuma murna... Kin sani cewa bani dakowa dake sai Humaira da Ameerah, hakane?. Duk yadda taso saida hawayen daya taho mata sai da ya zubo. Saurin sharewa tayi tace hakane, kuma nasan cewa kana so ya'ya ni kuma bazan iya haifa maka wasu ba. Kar kaji nauyin faɗamin cewa ka auro wata, koh kaɗan bazaka ga ɓacin raina ba. Amma kar manta alƙawari ni marainiyace karka ci amanar maraici! Tana gama faɗin haka ta mike ta wuce sama tace Allah ya sanya alheri. Dariya suka fashe da ita daga matar har shi. Ganin da gaske wucewar za tayi yasashi cewa, Dawo ki zauna Khadija ban gama magana ba! Jin yadda ya kaurara murya yasa Khadijah dawowa ta zauna. Tashi yayi ya rike da hannun matar ya nufi Khadijah ya rungumeta yace har abada babu wacce ta isa tayi kishi da ke Khadijah. Bana ce maki ina neman dangina ba? Kallonshi kawai tayi dan bata mason answer da zata bashi ba. Hannunta yasaka cikin na matar yace wannan yar uwata ce, Allah ya haɗani da dangina bayan tsayin shekaru Khadijah shiyasa na rasa ta ina zan fara gayamaki saboda murna. Wannan jininace daga ni sai ita iyayenmu suka haifa kuma Allah ya masu rasuwa.
Yafaɗa yana hawaye, share mai hawayen Khadijah tayi tace Allah yaji kansu, kayi hakuri. Bakomai yafaɗa yana murmushi, nan suka sake suka fara hira, suna nan zaune saiga su Humaira sun dawo daga makaranta. Da gudu Ameerah ta shigo tana faɗin Ummii, Ummiii fadawa jikin Khadijah tayi tana murmushi, murmushin itama ta mata. Humaira ce data shigo a nutse ta kula da bakuwar fuska ina wuni tafaɗa tana tsugunnawa. Murmushi tayi tace lafiya lau. Da ido Humaira ke tambayar baban nasu wace wannan. Murmushi yayi yace she is your Aunt Mami. Aunty Mami cewar Ameerah tana jingina da jikin Khadijah yadda ta fadi sunan kamar ta santa. Aunty Mami how are you? Am fine dear tafaɗa fuskarta dauke da fara'a.
Freshen up guys cewar Abbee yana kallonsu, Humaira zoki rike hannu kanwarki ku tafi cewar Khadijah. Ummi nidai gaskiya ba kanwar ta bace minti uku kawai ta bani cewar Ameerah tana ɓata rai. Riko hannunta Ummii tayi tace Khadijah inaso kimin alƙawari, you will always listen to your sister. Itace gaba dake, ki dena faɗa da ita. Pinky promise cewar Ameerah tana mika ma Khadijah karamar yatsar ta, yes pinky promise cewar Ummii.
Murmushi Humaira tayi tace Ummii bari ki gani nan da minti uku zaka karyar wannan alƙawarin. Biyota Ameerah tayi da gudu Humaira tayi sama tace catch me if you can.
Be careful cewar Abbee yan leken su.
Duk yadda Abbee yaso Aunty Mami ta kwana taƙi saboda mijinta na gari.
Badan yaso ba yakaita gida.
A kwana a tashi shaƙuwa mai karfi ta shiga tsakanin iyalan Abbee da kuma Anty Mami.
Musamman Aunty da Ameerah.
Ameerah da Humaira kuwa kullum cikin faɗa suke.
Abbe ne ya fito rike da akwatin shi, sanye da suites zai tafi Australia akwai contract din da zai yi signing.
Humaira ce rike da hannunshi ta rungume kamar tayi kuka, ita kuma Ameerah ta zauna kana suitcase din. Abbee please karka tafi cewar Humaira. Shafa kanta yayi yace haba maman mamanta. Ke da zaki lallaɓa kanwarki, niba kanwarta bace Abbee cewar Ameerah tana pouting face.
Am your sister kuma nima sister din Abbee ce, koh Abbee ai sunan mu ɗaya da Aunty Mami. Murmushi yayi yace eh, riko hannun Ameerah yayi ya saka a na Humaira, Aisha Humaira yafaɗa yana kallonta. Abbee tafaɗa kamar zatayi kuka dan tunda suke dashi bai taɓa tafiya ba tare dasu ba. Ameerah is your responsibility, zata ki kula da ita yafaɗa yana kallon Humaira. Murmushi tayi tace eh Abbee. Lakatar hancinta yayi yace Yawwa Kanwata.
Ameerah listen to your sister. Toh tafaɗa tana pouting face. Riko hannunsu yayi ya saka ana Khadijah dake kallonsu. Sahibaaa yafaɗa yana kallon cikin idanunta, murmushi tayi tace na'am Dan Aljanna ga amanar rayuwata nan na baki,ki kula dasu kwana biyu kawai zanyi just 48hrs. Tom zan kula dasu, girgiza mata kai yayi basu zaki ce ba, ku zaki ce. Murmushi tayi tace toh zan kula damu. Murmushi yayi ya rungumesu gabaki dayan su. Yana jin mixed feelings a tattare dashi.
Fita yayi, Mukhtar dake jiranshi a bakin kofa ne ya amshi akwatin yasaka a bayan mercedes din dazata kai Abbee airport.
Driver na tuƙi Mukhtar an gaba shi kuma Abbee na baya, su wuce gate uku na gidan sun fita har sun kan titi. Yace da driver ya juya yayi mantuwa.
Chapter 16 · 0% Book details