← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 50

Sashe 4

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BY IBNATU-UMAR ✍️
Page 5&6
Da sallam ta tura kofar haddaɗen parlourn dayasha kayan alatu, da sauri dattijuwar dake zaune ta cire gilashinta tana kallon hanyar corridor din shigowa parlourn, da gudu ta faɗa jikinta, murmushi tayi dake nuna farin cikin ganin Ameerah din ta ɗagota daga jikinta tace Nana Khadijah! Ammina tafaɗa tana gyara zama a lallausan carpet din dake parlourn.
Ammi nayi kewar ki, nima haka Nanarh, Amma dukkan mu aiki ya mana yawa. Hakane Ammi shiyasa nace ki dawo zama damu amma kikayi fushi dani baki nemi niba, tafaɗa tana haɗe rai. Murmushi tayi tace bazai yiwu in zauna maki a gida ba Khadijah, saboda ba ke kike haife niba, cewar Ameera kanta tsaye.
Kallonta Ammi tayi taga yadda abin ke cin Ameerah , tason rashin yaddarta a koh yaushe na bata ma Ameerah rai. Amma bazai yiwu ba taje ta tare mata a gida.
Shikenan Ammi karki damu bazan ƙara maki maganar ba. Murmushi kawai Ammi tayi kafin ta kwala kiran Inna Laraba mai mata aiki.
Ganin Khadijah yasa Inna Laraba washe baki dan tason zata mata alheri. Kice ma Chef ya kawo ma Nanarh Khadija Watermelon juice din danayi ɗazu. toh Hajiya yafaɗa cikin girmamawa tana juyawa kitchen din.
Kallon Khadijah tayi tace miye ke damun ki? Babu tafaɗa kanta tsaye, dan sai taji kawai ta fasa hirar datake son yi da Ammin.
Murmushi Ammi tayi kawai ta kyaleta dan tason haushi taji.
Juice din tasha sannan tama Ammi sallama, tace da Inna Laraba tayi hakuri bata fito da kudi ba yau ba daga gida take ba.
Hijabi Ammi ta saka da kanta ta raka ta wajen. Kwata-kwata Khadijah ta mance da Mahmud sai taji kunyar kanta, murmushi yayi ya sauko ya zagaya ya tsugunna har ƙasa ya gaida Ammi, da fara'a ta amsa mai tana tambayar shi aiki da sauran su.
Sallama suka mata ta dafa kan Khadijah tace Allah ya maki albarka Nanarh Khadija, murmushi tayi tace Ameen Ammi.
Kallon Mahmud tayi tace am sorry wallahi i was too exited na mance da kai, murmushi yayi yace it's fine.
Kasan mai tafaɗa tana murmushi, bata bari yace wani abuba ta ƙara da cewa a duk sanda nazo wajen Ammi, wannan dafa kaina da takeyi tana samin Albarka batason irin daɗin dana ke jiba, in ka cire Anty Mami, babu wanda ya nuna min Motherly affection kamar Ammi, we met as strangers amma she became a mother to me. Bansan daɗin mahaifiya ba sai da na haɗu da Ammi. Nasan ciwon tashi babu uwa shiyasa banson Zayn da Zaid suyi going through something like that. Duk da cewa babu abinda Abbee ya rageni dashi, love, care, time, money and affection amma i still yarn for that motherly love.
Ammi is a blessing to me, Allah yaji kanka Abbee tafaɗa tana maida kwallarta, riko hannunta yayi da dayan hannushi yace Ameen, Abbee is in a better place, In Sha Allah karki damu.
As for Ammi you mean the same to her, banjin koh tanada yara zata so su kamar yadda take sonki Meerah, ki kwantar da hankali ki, kinji Babe? Gyaɗa mai kai tayi tana murmushi.
Sai da suka biya wajen Zaid sannan suka koma gida.
*Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja*
Rike da hannun Ummii Ruhaan ya fito daga cikin jirgin, sanye yake da rika da wando brand din Ralph Lauren farare tas, kamshin turaren sa na Tobacco vanille na tashi, kwata-kwata bai yi kama da mai shekaru 36, kamar wani matashin saurayin dan 28. Saukowa wani matashi mai Kimanin shekaru 35 ya rungumesa yace Barka, Barka da dawowa, Aminina gajeran murmushi yayi yadan tureshi yana basarwa kamar baiyi murnar ganin Aminin nashi ba, Ina wuni Ummii yafaɗa yana tsugunnawa, Lafiya Lau Imran, ya aiyuka? Alhamdulilah Ummi, ya gajiyar hanya? Gajiya tabi lafiya, muje Ummi yafaɗa yana mata jagora zuwa motar ya buɗe mata, ta shiga.
*Asokoro, Abuja*
Parking Imran yayi suka sauka, kallon Ruhaan yayi yace Ni zan shigo anjima, amma masu aikin suna ciki, har girki Chef din tayi, gyaɗa mai kai kawai Ruhaan yayi ya wuce.
Murmushi yayi yana addu'ar Allah ya shirya amininsa duk da ba yau yasan halin Ruhaan ba, amma kullum cikin bashi mamaki yake, he is full of surprises.
*AK Group*
Cikin shiga ta alfarma Khadija ta sauko daga motarta bayan daya daga cikin guards dinta ya buɗe mata kofar, sanye take da suits whine and black ta company M.M. LaFleur. Rike da whine hand bag dinta ta Gucci, gyara zaman bakin shades dinta na Raen tayi, a gefen damanta Nisah ce.
Sai kuma securities 5 na binsu a baya.
Lifter suka nufa, 6th floor suka tsaya, a katafaren meeting hall din AK Group. A waje guards din suka tsaya, kofar tayi sliding ta shiga ita da Nisah, attention ne duk ya dawo kanta, daga gefe inda sauran P.A's suke zaune a nan Nisah ta zauna.
Wani kallon wulakanci Hajiya Hamdiyya tabi Ameerah dashi, zama tayi a kujerar dake daman ta Hajiya Hamdiyya, kafin a soma gabatar Monthly Share Holder's Meeting na A.K Group.
M.D Hamdiyya ce ta kallesu kafin ta fara masu bayani cikin harshen turanci, akan merger datake so suyi da Company din Sa'ad Wambai, shiru Ameerah tayi tana saurarenta harta kai karshe. Tana son jin idan akwai wanda keda matsala da hakan.
Danna button din jikin Mic 🎙️ din gabanta Khadijah tayi tace am against it, cije lebe Hajiya Hamdiyya tayi tanajin kamar ta kashe Khadija yanzu kowa ya huta. Kafin tace,
Miye dalilinki? It's simple am i business woman i go after profit, tafaɗa tana gyara zamanta, har sun cire ran zata kuma magana, sukaji muryarta na ratsa dakin taron, Sa'ad Wambai zai fimu ribata da wannan maja dan haka bazan amince ba, koh kun amince?? tafaɗa tana cire shades dinta tana karewa sauran shareholders din kallo, a zahiri suna son yarda da maja dan zasu dinga samun Oil money ta hanyar dan Sa'ad Wambai sanar'shi kenan, amma wannan kudi bata hanyar kwarai zai fito, so idan dai ribace za'a ci ta halal sai Sa'ad Wambai ya fisu ribata, amma kuma suna tsoron ja da Ameerah.
Murmushi Anty Mami tayi tace in this kind of situation voting will be the best decision...
Wani mugun kallo Hajiya Hamdiyya ta jefi Anty Mami dashi, dama tason koh kowa zai ki yadda da zancen Ameerah, banda Anty Mami.
Murmushi Anty Mami tamata tace let's begin.
Maimakon ayi voting kowa a fili sai Haiiya Hamdiyya ta dage cewa sai dai kowa ya rubuta a takarda ya ninke yasaka a cikin poll box din data saka aka kawo. Murmushi Ameerah tayi, wato Hajiya Hamdiyya zatayi komai danyin merger da Sa'ad Wambai. Juye kuri'un Muktar yayi ya irga, da bambancin ɗaya burin Hajiya Hamdiyya ya cika, ko kadan Khadija bata damu ba dan tason za'a rina.
Anan aka gama meeting din kowa ya fice, ya rage daga Hajiya Hamdiyya, Zulaika, Nisah sai kuma Ameerah a meeting hall din.
Kallon Hajiya Hamdiyya tayi tace what are you planning with that cunning mind of yours? Murmushi Hajiya Hamdiyya tayi tace yaro bai san wuta ba sai ya taka. A ganin ki ni zaki juyani ne yadda kika saba juya mutane? Toh kinyi kaɗan! Cire shades dinta tayi, ta mata wani mugun kallo da sai da tasha jinin jikinta, jakarta ta dauka ta fice.
A bakin kofar taga Anty Mami tsaye tana waya, rungumeta Ameerah tayi tana murmushi, murmushi itama Anty Mami tayi ta kashe wayar, tana kallon Ameerah tace Mamana anya kuwa? Murmushi tayi tace miye kuma nayi Anty Mami? Kullum kiyi ta karewa kamar kudin guzuri, kinama samun lokacin kanki kuwa? Murmushi tayi tace chillax Anty Mami, am fine.
Murmushi Anty Mami tayi tace nadai kyale ki bawai danna yadda ba, amma gaskiya you need to be creating time for yourself, kema mutum ce kamar kowa kina bukatar hutu Ameerah.
Toh Anty Mami, murmushi tayi ta riko hannun Nisah dake gefen su tace ki dinga sata hutawa dole, murmushi Nisah tayi tace Anty Mami batajin magana ne ai, hararta Ameerah tayi, dungure mata kai Anty Mami tayi tace ai nasani dama, Auchhhhh Anty Mami zafi, sannu yi hakuri cewar Anty Mami cikin damuwa ganin yadda Ameerah ta kwaɓe fuska kamar zatayi kuka.
Murmushi Ameerah tayi, ta riko hannun Anty Mami har suka fita, suka shiga lifter, sai hira suke kamar wandanda sukayi shekara basuga juna ba, bayan kwata-kwata watan Anty Mami Ɗaya a France, jiya ta dawo, sai ga sanarwar meeting ba yadda ta iya dole tazo.
Bye bye Anty Mami sai munzo kwance jaka cewar Ameerah tana rufewa Anty Mami kofar motarta bayan ta shiga. Karki damu bamai kwance jaka sai ke ai Uwata ta kaina, murmushi tayi sukayi sallama ta wuce motarta, buɗe mata securities sukayi tashiga suka rufe.
Murmushi Anty Mami tayi tunawa da tayi ganin cewar Ameerah din data buɗe mata kofar mota, ta shiga ta kuma rufe mata. Itace wanda ake rawar jikin budewa mota. Tasan cewa da mahaifiyar Ameerah nada rai, babu abinda Ameerah bazata mata ba, tunawa da dan uwa kwa ɗaya jal, yasata jin kwalla, saurin sharewa tayi ganin Ameerah na ɗaga mata hannu batason ta ganta tana kwalla, murmushi tamata ta tada motar ta ta nufi gida tana ma Dan uwanta addu'ar samun rahamar ubangiji.
*Asokoro,Abuja*
Zaune suke a dinning table bayan sun gama cin abinci, kallon Ummii Ruhaan yayi yace Ummi gaskiya ni zan nemi aikin yi, na riga na saba da kazar-kazar, amma Babana mai zakayi da kuɗi, in banda abinka? Miye ka nema ka rasa? Babu kawai banson zama hakane. Ai shikenan, Allah ya taimaka, amma ni banson aikin nan naka. Karki damu Ummi. Na tafi wajen Imran yafaɗa yana mike ya nufi hanyar waje.
A parking lot ya tsaya, ya buɗe kofar ɗaya daga cikin motocin dake wajen ya fice.
Horn dinga yayi sai da mai gadi ya leko ya ganshi, ya koma ya buɗe mai ya shigo.
Parking yayi ya sauko, ya dauko wayar shi ya fara dialing numbern Imran, dauka Imran yayi zai fara mai iya shige, yace ka fito waje! Yana faɗin haka ya kashe wayar.
Hararar wayar hannunsa Imran yayi kamar Ruhaan dinne wayar, sannan ya kalli matarsa yace kinga kallar rainin hankalin nashi da nake faɗa koh? Ya hakuri baban Khairat kaje kaji mai ya faru, kasan dai haka kurin bazai zo nan ba.
Toh mu haɗu a next page 📄📄📄
ANA ZATON WUTA A MAKERA...🔥
Chapter 4 · 0% Book details