← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 50

Sashe 5

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

BY IBNATU-UMAR ✍️

Page 7&8
Fita Imran yayi ya sameshi tsaye ya rungume hannunwansa, wai kace yau akwai ruwa da kankara...harararshi Ruhaan yayi yace sai anjima. Baki sake Imran ke kallon shi, dama abinda kazo gayamin kenan?..... No, Ba zan shiga ba gaskiya... maganar shi ce ta makale jin Imran yace bazakaga Little din taka ba kenan? murmushi yayi daya ƙara ma fuskarsa kyau, ya sauko daga motar, yace naso nazo mata da abu wallahi. Taɓe baki Imran yayi yace gulmar tsiya, mutum sai iyayi sai kace mace.
Koh kulashi Ruhaan bai yiba suka shiga ciki, fitowa Jamila matar Imran tayi suka gaisa, amsa mata yayi batare daya kalle taba koda wasa. Imran ne ya fito rike da yarinya yar kimanin shekara biyar, tana hango Ruhaan ta tafi da gudu ta faɗa jikinsa tana murnar ganinsa.
Uncleee yazo!! Ta faɗa tana rungume shi, murmushi yayi idanunshi na cika da kwalla ya dauketa ya daura akan cinyarshi yace princess ya school? Bata rai tayi tace ba daɗi Uncle Moh, amma tunda kace na dinga zuwa, ina zuwa kullum ka tambayi Mama ma tafaɗa tana kallon Mamanta data ajiye ma Ruhaan tray dauke da kayan motsa baki da zobo.
Jan hancinta yayi yace na san zaki je ai princess. Sauka tayi daga jikinshi ta zuba mai zobo a cup ta mika mai, amsa yayi ya sha duk da bai yi niyyar cin komai ba, hira ta mai sosai, sallama sukayi da Jamila, Imran ya fita ya rakashi.
A hanyar shi ta komawa yaga wata motar makaranta da yara cike, alamar excursion zasu ta lalace. Har ya wuce dan shi mutum ne daya tsani shiga abinda bai shafe shi ba, sai kuma yaji kawai bazai iya ba, juyawa yayi ya faka motarshi ya kalli drivern, dake tsaye da wasu mata biyu da maza biyu da alama malamai ne.
Sallama ya masu suka amsa, tambayar su yayi mai ke faruwa, bayani suka mai....move yafaɗa yana kallon drivern dake tsaye yana kokarin duba matsalar.
Yaso mai musu amma kwarjinin daya gani a fuskarshi bazai iya sashi yace mai a'a ba....cikin minti sha biyar ya gama ya shiga ya tada coaster bus ai kuwa sai gashi ta tashi, ihun murna yaran sukayi, suna ta gode mai haka ma malaman su.
Wata yarinya ce mai kimanin shekara bakwai ta sauko daga motar ta kalli Ruhaan da hannu ta mai alamar ya rage tsayin sa, murmushi Ruhaan yayi ya rage tsayinsa dai-dai ita, peck tamai a kumatu tace Thank you Mr Handsome, murmushi yayi ya riko I.D din yarinyar , Khadijah Ibrahim Jikamshi, yafaɗa a ranshi, a fili kuwa riko hannunata yayi yace DU'A.
That's not my name tafada tana bata fuska, am sorry but i can't say your name cewar Ruhaan yana rike kunnuwansa, murmushi yarinyar tayi tace why?zai yi magana yaji horn din driver... bye Uncle, ta faɗa tana wuce wa ciki, har ta shiga coaster bus din Ruhaan na tsaye yana kallonta. Leko wa tayi ta window tace Mr Handsome, juyowa Ruhaan yayi yana jiran yaji mai zata ce, your name? Cewar yarinyar tana kallonshi, Mohammad Ruhaan yafaɗa da dan karfi, kashe mai ido tayi, tamai blowing kiss, kasa motsi Ruhaan yayi saboda gesture din da yarinyar tayi, abu ta wurgo mai tace we will meet again, smileee cewar yarinyar da karfi, dariya Ruhaan yayi sosai sanda yaga wani cartoon character da ta wurgo.
For the first time after 6 years, i met someone that remind me of you, yafaɗa yana murmushi. Har zai tafi, yaga I.D card din yarinyar a kasa, da mamaki ya dauka, koda ya juya har sunyi nisa.
A aljihunshi yasaka I.D din da niyyar zai aika a akai school dinsu.

Koda Zayn ya koma gida Ameerah na gidan Anty Mami so basu haɗu ba. Sauka yayi ya saka numbern Khadijah a landline ya kira, dauka tayi tace Hayati ka dawo kenan, bata rai yayi yace Haba Ummii shine kika tafi kika barni? Ya hakuri dan albarka ina hanya yanzu kaji, freshen up and eat your food kaji good boy? Nidai zai kinzo, Mahmud daya shigo yanzu ne yayi murmushi ya amshi landline din yace karki damu zai ci Babe, stay safe yafaɗa yana ajiye landline din.
Kallon Zayn da yayi pouting face yayi yace Zayn be a good boy muje yafaɗa yana tasa keyarshi a gaba har dakinshi.
Wanka yayi ya shirya, ya nufi dinning, dai-dai lokacin shima Mahmud dayaje yayi wanka ya sauko.
Abinci Mahmud ya zuba mai ya tsare shi sai da yaci, ko barin wajen basuyi ba sai ga Ameerah ta dawo, pecking kan Zayn tayi, ta gaishe da Mahmud, da murmushi ya amsa mata.
Kallon Zayn tayi ta ruko hannunsa tace come and tell me about your day.
Murmushi yayi yace Ummii motar mu ta lalace a hanyar excursion dinmu, but a nice uncle helped us yafaɗa yana murmushi, murmushin itama tayi tace toh ka gode mai koh? No i didn't get the chance to do that, amma wannan yarinyar mai iyayi ta class dinmu Khadijah taje tamai magana.
Well it's good then, karka damu kaji? Toh Ummii, i have his picture tooo yafaɗa yana tashi da gudu yaje sama ya dauko camera dinshi, Ummii banyi printing hoton ba amma kinganshi yafaɗa yana kokarin karasowa kusa da ita, batare daya kula da chef daya taho da juice din Ameerah ba.
Karo sukayo da chef din camera ta faɗi, juice din ya zube a kanta.
Da sad face ya kalli Chef din dake ta bashi hakuri ya tsugunna zai dauki Camera, Ameerah ta ƙaraso wajen ta dauka, tace ma Chef din yaje, ruko hannunshi tayi yace don't cry, zata gyaru ai, Ummiii kalli fa ta fashe kuma juice ya shiga ciki, yafaɗa yana kwalla.
Don't cry over a spilled milk, kalleni tafada tana daura shi kan cinyarta, mai nake gaya maka a koda yaushe? Share hawayen shi yayi yace duk abinda ya faru da mutum haka Allah ya ƙaddara, mai kyau koh mara kyau. Good tafada tana kallonshi, so karka damu idan bata gyaru ba, zan siyo maka wata.
Murmushi Mahmud dake kallonsu yayi, yace iyyee uwa ta gari, hararar wasa tamai tana murmushi. Shikuma Zayn ya sauka ya wuce wasan shi.
Hajiya Hamdiyya ta dage da Maja, inda ita kuma Ameerah kebi ta bayan kasa tana wargaza mata duk wani shirin ta.
A shirye a Ameerah ta fito cikin atampa super embellished mai colour combination din sky blue, coffee brown and pink.
Tayi kyau sosai, musamman daurin Zara Buhari datayi, yayi fitting dinta.
Gyalenta sky blue mai girma ya yafa, ta dauki bag dinta ta Da Milano.
Tana tafe suna hira da Nisah suka fito daga News Buzz. Motoci securities dinta suka buɗe da niyyar binta, kallonsu tayi tace bata bukatar su bita, PTA zata. Sir Muktar warn us to strictly guard you. Kankace ido tayi ta watsa mai mugun kallo mai cike da gargadi, sannan ta kalli Nisah tace sai na dawo.
Murmushi Nisah tayi ta ɗaga mata hannu, jan motar driver yayi suka fice daga Company.
Hanyar Heart Pearls Academy suka dauka, minti goma sha huɗu ne tsakanin News Buzz da Heart Pearls.
Saukowa tayi a hankali, kafin ta fara tafiya cikin nutsuwa da aji. Hanyar class din su Zayn ta nufa, yana hangota ya fito da gudu ya rungumeta, murmushi tayi ta ciroshi a jikinta ta ruko hannunsa suka shiga ciki. Gaisawa tayi da homeroom teacher dinsu, kusan awan ta daya a makarantar ta gama abinda za tayi ta fito.
Yara ne ta hango a field suka wasa, juyawan da zatayi tayi karo da wata yarinya, saurin riko hannunta tayi ganin zata faɗi, am sorry cewar Ameerah tana murmushi. Murmushi yarinyar ta mayar mata tace you're beautiful 😍, You're beautiful too tafaɗa tana mamakin kamar yarinyar da wani data sani.
What's your name? cewar Ameerah tana murmushi. Dariya tayi tace Khadijah, murmushi tayi tace mai babban suna, bye girl cewar Ameerah tana jin kamar ta tafi da yarinyar, so cutee 🥰, Allah ya sani tanason diya mace amma Allah yabata kuma ya amsa.
Juyawa tayi ta fito waje motar ta na barin wajen, motar Ruhaan na isowa.

Toh mu haɗu a next page 📃📃

ANA ZATON WUTA A MAƘERA.... 🔥
BY IBNATU-UMAR 🖋️
Chapter 5 · 0% Book details