← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 50

Sashe 8

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Zayn a plate. Gutsirar cake din yayo da fork ya nufi bakin Ameerah dashi Maaa haa yafada yana kallonta da murmushi bata musa ba duk da cikinta dake a cike, sai da taga Zaid bai da niyyar dena bata tace mai takoshi ta mashi fork din shima ta bashi ta kuma bama Zayn. Kallon Zaid tayi tace zata kaishi playground yasha iska, daukan littafanshi Zayn yayi ya biyosu, ajiye Zaid tayi suna harkarsu a gefe itama tana nata aikin a gefensu. Bayan sati daya. Zaid ya warware sosai ba inda baya shiga da kafarshi. Fitowa tayi da safe Zaid na biye da ita rike da hand bag dinta, kallon securities din dake sanye cikin baka da farar suit tayi kowannen su da tie banda wani bakon fuska data gani. Har za tamai magana sai kuma ta kyale shi. Buɗe mata motar yayi ta shiga, ta rasa mai yasa yake bata wani irin aura , ga wani irin kwarjini daya mata. Kallon Mukhtar dake tsaye yake mata bayabin cewa shine bodyguard dinta kuma driver dinta. A dan wannan lokacin taya ka samo shi? Tafaɗa tana tsare shi da ido Hajiya ce tayi recommending dinshi. Anty Mamiii tafaɗa tana kallonsa, sosa keya yayi yace sorry Miss. Gajeren tsaki taja tace its fine. Buɗe kofar Zaid yayi ya bata jakarta. Yace bye Maa be safe. Da mamaki Ameerah me kallonshi dan batason mai yasa ya tsuri tashi ya rakota ba yau. Lekawa yayi wajen drivern daya haɗe rai, Hi Uncle! Hi yafada yana murmushi, Uncle what's your name? Mohammad yafaɗa yana kallon Zayn, okay then i will call you Uncle Moh, saurin kallon Zaid tayi tace go inside, right now! Bye Mamii, Uncel Moh drive safe... Moh din da Zaid ya kira yasa gabaki ɗaya take jinta wani iri, gajeran tsaki taja, kallonta ta mudubi drivern yayi yace Ma'am are you okay? Jin tayi shiru yasa ya cire tsammanin samun amsa, yama manta ya tambaye ta sannan yaji muryarta cen kasa-kasa am fine. Murmushi kawai yayi ya cigaba da tuƙin sa har zuwa News Buzz. Saukowa yayi ya buɗe mata, tana tafe yana binta a baya har zuwa bakin office dinta ganin zai bita yasata dakatawa tace Malam lafiya? Ma'am am your bodyguard, Mr Mukhtra yace duk inda kika sa kafarki in sa tawa, wani mugun kallon tamai tace you can follow me to the toilet as well, ce kace hauka ne abin. Ka koma gida, idan zan fita zan kiraka am safe here. Ma'am but....hannu ta ɗaga alamar ya isheta. Sorry Ma'am yafaɗa yana juyawa ya fice, motar ya dauka ya koma gida kamar yadda ta bashi umarni. Parking yayi ya zauna a garden din gidan, balle botirin inner suit dinshi yayi, yana sauke ajiyar zuciya. Zayn dake wasa ne ya hango shi, laaa Zaid come and see yafaɗa yana leƙen shi. Shine nake gaya maka, he is Uncle Moh sabon drivern Ummiii. Mai yasa yake zaune kamar baida lafiya fah? Cewar Zayn yana leƙen shi, no i think he is hungry, muje mu kai mai abinci. Sauka ƙasa sukayi suka bubbuɗe warmers din dake dinning, suka zufa mai Irish da kidney sauce. Tea suka haɗa mai, mai kauri. Kallonsu Nanny dinsu tayi ta tambaye su inda zasu, Playground suka faɗa suka ficewa. Good morning Uncle Moh cewar Zayn yana kallon shi da murmushi, murmushi shima yayi ya amsa gaisuwar shi. Zama sukayi a gefe shi, Uncle Moh eat cewar Zayn yana mika mai plate din abincin. Murmushi yayi yace Nagode na koshi. Bata fuska sukayi, ganin basuji dadi yasa ya amsa yaci kadan ya mika mai, ya mashi tea din hannun Zaid shima ya sha rabin cup din ya mika masu. Thanks yafaɗa yana kallonsu da murmushi. Ciki suka mayar da kayan, suka fito waje sukai ta sashi magana, daga karshe ma cewa sukayi yazo suyi ball. Suna cikin ball din aka kira sallah, cikin sauri suka nufi tap din dake wajen sukayi alwala. Tsayawa yayi yana kallonsu sun bala'in birgeshi, alwala shima yayi yasa su a gaba suka nufi masallaci.
Chapter 8 · 0% Book details