Sashe 30
Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Page 47&48 Sosai hankalin Daddy ya tashi da Mukkaram ya gayamai abinda ya faru. Tura yaran dake parlourn shi yayi wajen Nannies. Ya nufi asibitin dama Mukkaram nacen. Kusa da Humaira dake motsa bakinta Yarima ya matsa yana kasa kunne dan yaji mai takeson cewa...Amiii..Amiii..Amiii Kallon Usama yayi yace ina sister ta da'a kawo su tare? Tana next room Dr. M yasa mata drip, babu wani abu ita gaskiya. Shock ne yasa ta suma. Dakin ya shiga da sallama, da mugun mamaki yake kallon Ruhaan dake zaune akan couch din dakin yana waya. Kashe wayar Ruhaan yayi ganin Asadullah shima. Murmushin fuskarshi ne ya faɗaɗa yace Asadd. Tun yaushe kake Nigeria? Cewar Yarima yana daure fuska. Sosa keya Ruhaan yayi yace i wanted to comee....saurin katse shi Yarima yayi yace save your explanation to yourself. Haba Bro cewar Ruhan yana dafa shi. Are you on a mission? Cewar Yarima yana kallon Ruhaann. Self Mission ne wannan cewar Ruhaan yana kallon Amira. Amii? Kasan Amii wai? Don't tell me....kallon Yarima yayi da mugun mamaki yace taya kasani. I will explain later nan ba wajen maganar nan bane. Kallon Amiraa data mike zaune Yarima yayi yace Amii ya jikinki? Murmushi tayi dan ta gane shi tace da sauki. Kallon Ruhaan daya haɗe rai tayi ta kara fadada murmushi tace Thanks Dr. Amii ai ba ninayi treating dinki ba gashicen wanda yayi treating naki. Forget about him, My sister tafada tana ƙoƙarin saukowa daga gadon. Cire drip din tayi dama ya kusa karewa. Ta nufi kofar waje.Bin bayanta Yarima yayi ya rakata dakin da Humaira take yi, da kyar ta karasa kusa da gadon tana fashewa kuka ganin halin ,da Humaira take dake ciki. Rungumeta tayi tace am sorry Sister, nice na ja maki, ji tayi gabaki ɗaya ta tsani kanta. Amii stop crying cewar Yarima yana dafa kanta, do you think your sister will be happy to see you like this? Girgiza mai kai tayi yace good now wipe your tears yafaɗa yana sa hannu cikin aljihunsa ya ciro handkerchief yaji babu. Na gaba aljihun Ruhaan ya zaro ya mika mata, baki sake Ruhaan ke kallon ikon Allah. The kidss tafaɗa a zabure tana mikewa. Kallonta Ruhaan yayi tashin hankali na bayyana a saman fuskarshi what happened to them? Bai shafe kaba tafaɗa tana ratsa wa ta gefen shi zata wuce. Wrist dinta ta ya ruko ya dawo da ita gabanshi idanunshi na kadawa i said what happened to them yafaɗa yana kallon cikin idanunta. Dauke nata idon tayi ta kalli gefe, tana jin wani irin zafi na ratsa ta kamar taji mugun ciwo a wrist dinta, ganin tayi banza dashi yace stop trying my patience Imann yafaɗa yana ƙoƙarin danne ɓacin ranshi. Aucchh tafaɗa tana fashe da kuka,tana yarfa hannu. Am sorry yafaɗa yana duba wrist din, kamar taji ciwo fah cewar Yarima yana kallon wrist dinta. Straight wajen X-ray Ruhaan ya tafi da Ameerah sai maganganun banza take gayamai. Da kanshi ya duba result din ya kalleta yace Imaan! Kallonshi tayi ta watsa mai harara tace miye? You can't draw again yafaɗa yana jin wani irin ɗaci a ranshi. A firgice ta kalleshi tace what? Am sorry yafaɗa yana kallonta. Juyawa tayi kawai ta nufi hanyar komawa dakin da Humaira take tana son comprehending abinda Ruhaan ya gaya mata. Mukkaram daya shigo yanzu Amira ta kalli, yawwa Mukkaram ina su Zayn? Suna gida ki kwantar da hankalinki. Whatt!! Babu abinda ya samesu? Mai kwa zai samesu tuntuni driver ya dawo dasu gida. Ammi fah? Tare da ita suka dawo ai. Nan ta fara bashi labarin abinda ya faru. Tsaki Mukkaram yaja yace Allah idan pranking dinki Ammi tayi yau saina zaneta. Gaban gadon da Humaira ke kwance ya nufa yace Sister Allah ya baki lafiya, Ameen duk suka amsa. Kallon Amira Daddy yayi yace Amira koh zamuje dake gida ki huta kema bakya jin dadi. Am fine Daddy bazan iya barin sister ita kaɗai ba. Toh muje koh wanka ne ki samu kiyi kici abinci sai Mukkaram ya dawo dake. Nan ma taki, da kyar ta yadda bayan Daddy ya lallasheta,suka tafi gida. Kallon Ruhaan Asadullah yayi yace ina kasan Amirah? And which kids are you guys talking about? Murmushi Ruhaan yayi yace she was my wife. Was?? Cewar Asadullah yafaɗa yana kallon Ruhaan. Yeah cewar Ruhaan yana gyaɗa kanshi. Why don't you tell me ina kasan su? Nasan ka sarai Aliyu, mata basa gabanka, there must be a reason, tell me what is going on? Are you on a Mission? Girgiza kai Aliyu yayi yace ko daya. Huci ya furzar yace kasan i don't even know why am doing this, Abbaa asked me to protect them and keep them safe. Abbaa? Babanka dai? cewar Ruhaan cikin mamaki. Gyaɗa mai kai Aliyu yayi ba tare dayace komai ba. Am confused, nima ina cikin ruɗani Asadd bansan mai yake faruwa a rayuwarsu ba. Da fari na dauka abinda ya samu yar mu Du'a saboda nine, ina ganin zaman AMIRA tare dani ne yasa rayuwarta cikin hadari. Shiyasa na rabu da ita. Amma yanzu na gane cewa the danger revolve around us. Ni, Kai, Amira da Humaira, miye Alaƙar dake tsakanin mu? We need to figure this out, cewar Asadullah yana dafa kafaɗar Ruhaan. We have to, Ruhaan yafaɗa yana kallonshi. Tsare-tsaren suka fara ta yadda zasu fara wannan aikin. Gashi spare key din studio dina ne, mu haɗu a cen gobe da karfe 8:00pm. Tafiya Ruhaan yayi yabar Asadullah a wajen Humaira. Koh abinci bata wani ciba ta dawo asibitin. Washegari da safe Humaira ta tashi, Aliyu ne ya dubata yaga batada wata matsala amma still zata zauna a asibiti na kwana uku saboda head injury yafi karfin wasa dole ayi monitoring dinta. Amii cewar Humaira tana shafa fuskar Amira are you okay? Hawayen daya zubo mata Amira ta share tace i should be asking you, why did you do that? Tafaɗa cikin fushi, faɗa sosai ta fara ma Humaira. Murmushi Humaira tayi tace that's how you thank someone that saved your life? I never ask you to do that cewar Amira da idanunta cike da kwalla. Am sorry cewar Humaira tana rike kunnuwanta. Rungumeta Amira tayi ta fashe da kuka tace don't do that again, you sacred me sister. Na dauka na rasaki, i don't want to loose you again. Please karki kuma tsoratani haka. Amii your wrist tafaɗa tana riko hannun Amira. Murmushi tayi mai ciwo tace bazan kara iya zane ba sister. Amma yana warkewa jiya yama fi haka kumbura. What do you mean? Tafaɗa a firgice dan tasan yadda Amira ke son zane. Bayani Asadullah yamata. Rungume juna sukayi suka fashe da kuka, da kyar Humaira ta tsaida nata kukan ta lalashi Amira. Kallon Asadullah daya tsaya kallonsu Humaira tayi tace lafiya malam? Haɗe rai yayi yayi kwafa baice mata komai ba. Amii zo muje ki karbo mata magunguna, idan taci abinci sai ta sha. Whatt? Mai kace? Cewar Humaira tana zaro ido? Murmushi yayi yace don't tell me tsoron shan magani kike? Not that tafaɗa tana hararshi. What did you just call her? Amii yafaɗa yana rungume hannuwanshi a kirji. Don't call her that, only i can call her with that name she is my sister not yours tafaɗa tana haɗe rai. Dariya yayi harda kyakyatawa, baki sake take kallonshi dama ya iya dariya? Take tambayar kanta. Ke wai anya kanki bai samu matsala ba? Amii muje yafaɗa yana kallon Amira. Murmushi tayi ta bishi, baki sake Humaira ta bisu da kallo. Roarr! Hasbinallahu Wani'imal Wakil tafaɗa tana dafe kirji, Mukkaram you scared me, tafaɗa tana kallon Mukkaram da bata san sanda ya shigo ba har ya zauna gefenta. Murmushi yayi yace naga kin tafi tunani shiyasa. Hararshi tayi tace ka cigaba, Tea ya haɗa mata, bayan ya kawo mata bowl tayi brush. Sipping tea din tayi a hankali, ta dago idanunta ta kalli Mukkaram tace Muky ina son sanin details din trailer nan data so bige motar Amira. Waittt dama ba accident bane, cewar Mukkaram yana kallonta da mamaki. Stop pretending nasan kasan ba accident bane. Murmushi yayi yace oya you don catch me. Amma da gaske bansan bake aka so attacking ba. Waittt tafaɗa tana ajiye tea din akan table din daya daura mata plate din chips tace Ammi ce ta fara kiran Amira tace wai an tafi da Zayn....... Shiru yayi bayan ya gama jin labarin data bashi, yace don't worry sister. Ki warke tukunna koma miye mayi daga baya. Butt Mukk...no but's karki damu, ki barmin komai. If you insist tafaɗa tana dauka tea dinta ta cigaba da sipping a hankali. Amira ce ya shigo dauke da magungunan da Aliyu ya bata. Sister bara na zuba maki abinci, no banjin yunwa Amii na sha tea. No but sister....ki bari anjima cewar Humaira. Ballo mata maganin tayi ta bata, amsa Humaira tayi ta haɗiye tana ɓata fuska. Waya Mukarram ya miko mata, waye tafaɗa tana kallon wayar, Hello Sweetheart tafaɗa tana murmushi. No, am so sorry baby wallahi ba haka bane, okay tom i will be waiting for you, Thanks Love Baki sake Amira ke kallonta, kehh tafaɗa tana murmushi ganin yadda Amira ke kallontam Sweetheart, Baby, Love cewar Amira tana irga sunayen da yatsun hannunta. Zaro ido tayi tace were you speaking to your boyfriend? Dariya tayi tace o boy! Boyfriend?? No way tafaɗa tana gyara zaman pillow dake bayanta. Then who were you talking to? Koma waye ai zaki gani since the person is coming here. Harararta Amira tayi tace i won't ask again. Kafaɗa Humaira kawai ta ɗaga batace mata komai ba. Juyowa tayi tace butt... dariya Mukkaram ya fashe dashi yace na dauka kince bazaki kuma tambayar taɓa. Haɗe rai tayi ta zauna akan kujerar ta ciro wani Novel daga cikin jakarta tana karantawa. Kamar bayan minti talatin, wayar Mukkaram tayi ƙara, ya fita waje. Bai jima ba ya dawo shida wata budurwa mai kyan gaske. Rike da bouquet 💐 da kuma gift bag dayan hannunta. Kwalla ne ya taru a idanunta a sanda taga Humaira tace Besttt Innalillahi Wa Inna Ilayhi Raji'un....na shiga uku Humaira kece haka tafaɗa tana riko hannunta. Murmushi Humaira tayi tace cry cry don't cry it's fine nama ji sauki tafaɗa tana hugging dinta.