← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 50

Sashe 39

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Toh mu haɗu a next page 📄📄📄

ANA ZATON WUTA A MAƘERA....🔥

✒️IBNATU-UMAR ✒️

Page 59&60
Koda isa Adamawa, motocine na alfarma sukazo daukan su. Dan ansan da zuwa Yarima Asadullah amma baice ma kowa da baki yake tafe ba.
Sashen Sarauniya Zaituna (maman Asadullah) aka sauke su Amira, Humaira da kuma Ammi. RUHAAN dasu Zaid kuma suka tafi sashen Yarima. Da fara'a Sarauniya Zaituna ta tarbe su, tana tama Asadullah faɗan bai gayamata da baki zaizo ba. Sallah sukayi, aka kawo masu abinci da kayan marmari. Basu wani ci abincin ba, Ammi ce ma taci ba laifi. Sai kallon Ammi Sarauniya Zaituna take. Mika mata hannu tayi tace zo yan mata ya sunanki. Murmushi tayi tace Khadijah, wani irin yanayi sukaga ya bayyana a fuskar Sarauniya Zaituna. Aika daya daga cikin kuyanginta tayi tace su kira mata Gimbiya Fadima (kanwar Yarima Asad).
Bata kai su Humaira ba, amma bazasu girme mata sosai ba. Sashenta ta tafi dasu koh zasu dan sake.
Tana tama Ammi wasa. Wayarta Amira ta ciro a jaka ta kira Ruhaan. Kuna ina wai? Bafa kwana zamuyi b, gashi har karfe 2 saura. Muna hanya Madam yafaɗa yana kashe wayar. Mai suka ce wai? Humaira tafaɗa tana kallon ta. Suna hanya cewar Ameerah tana gyara zaman veil din datayi rolling.
Sallamar Yarima yasa duk suka zubama kofar ido. Wani irin kwarjini ya masu saboda Alkyabbar ya daura akan shaddar jikinsa. Ga wani irin kyai data mai. Hammaa cewar Fadima tana rungumeshi. Cirota yayi a jikinsa yace kewai bakisa kin girma bane. Kai Hamma tafaɗa tana ɓata fuska..woww tafaɗa ganin su Zayn tace Masha Allah yarannan masu kyau wallahi. Tafaɗa tana shafa fuskar su, dariya ta basu ai kuwa duk suka kwashe da dariya harda su Zayn din. Ɗagowar da zatayi suka haɗa ido da Ruhaan dake tsaye a bayan Yarima Asadullah. Innalillahi tafaɗa tana kallonshi da mugun mamaki. Waye wannan Hamma? Tafaɗa tana nuna Ruhaan. Murmushi Yarima yayi yace best best friend dina ne. Amma Hamma he looks like...kallon da Yarima ya mata yasa ta haɗiye sauran zancen nata. Kutashi muje wajen Mai Martaba yanzu yana sashen shi. Lokacin lunch dinshi ya kusa yafaɗa yana kallon agogon hannushi. Har suka fito ta rakasu mota mamaki bai bar Fadima ba. Taso share zancen amma ta kasa, ta fito dan zuwa wajen mahaifiyarta ta gaya mata abinda ta gani.
Yarima ne ya fara shiga, ya sanar ma da Mai Martaba da baki yake tafe. Ka shigo dasu mana Yarima. Komawa yayi ya shigo dasu, yana gaba rike da hannun Zaid da Zayn. Humaira na binshi a baya sai Amira sai da Ammi sai Ruhaa.
Idanunshi na sauka akan su Zayn ya ajiye glass cup din ruwan dake hannushi. Da mugun mamaki yake kallon fuskar Humaira. Mamaki bai kusa kashe shiba sai da yaga Ruhaan. Duk yadda yaso karya nuna wani abu, amma saidai ya gagara boye hakan akan fuskar shi.
Durkusa duk sukayi suka gaishe shi. Hannu ya miƙa ma Ammi dake gaba, murmushi tayi ta kalli Yarima tace Uncle Asad can i touch the King? Murmushi yayi ya gyaɗa mata kai. Kama hannun da Mai Martaba ya mika mata tayi ta mike tsaye. Zaunar da ita yayi akan jinyarsa yace ya sunanki. Khadijah tafaɗa tana murmushi. Murmushi yayi ma kyan gaske. Why are you smiling? Tafaɗa tana kallonshi. Murmushi yayi yace you remind me of someone. Who? Tafaɗa da curiousity. A very good friend of mine yafaɗa yana murmushi. Tana ina toh? Nima bansani ba,nima neman Khadijah nake yafaɗa yana kallonta da idanunsa da suka fara chanza launi. Why did you loose your friend? I let her go. I won't loose Zayn, i will always hold his hand. Tafaɗa tana riko hannun Zayn dake gefen su. Look for her and apologize tafaɗa tana mai murmushi. Khadijah hakuri bazai iya goge lafin taba. Does she love you too? Gyaɗa mata kai yayi. This much tafaɗa tana buɗe hannuwanta. This much yafaɗa yana buɗe hannuwansa. Zaro ido tayi tace that's much, you should forgive her. What happened though? Tafaɗa tana tsareshi da Ido. Adults matters yafaɗa yana jan hancinta. Dariya tayi tace it's fine i can talk to her for you. Dariya yayi yace yaro yaro ne. Sai a lokacin ya tuna dasu Yarima.
Ƙara gaishe shi sukayi, ya amsa cikin kulawa. Yarima ne yace Abba ban maka bayanin bakin naka ba. Nuna Humaira da Amira yayi yace sune.... Khadijah Amira da Aisha Humaira Abdulkarim Kurfi cewar Mai Martaba. Mamaki ne ya bayyana asaman fuskokin su amma banda Humaira, idan dai yayi aiki wannan ƙungiyar she expects more from him.
Yarima shiga ciki da yaranan yafaɗa yana kallon su Zayn. Cikin parlourn Mai Martaba ya shiga dasu, ya kunna masu cartoon ya fito.
Wata safe yasa ya Yarima ya dauko mai.
Wannan safe din tana da mukulli, wanda muka yishi mu huɗu. Dani da Abbanku, da Alhaji Jikamshi da kuma Alhaji Mamman Oil. Mukulli ɗaya ne a zahiri amma a ba ɗini pieces biyar ne da mukulli. Biyu na wajen Abbanku, na wurina na hannun Yarima, biyun karshen ɗaya na hannun Alhaji Jikamshi da Mamman Oil. Amma mai 3 din na iya buɗe safe din. Biyun na wajen Abbanku daya na wajena.
Kallon juna Humaira da Amira sukayi dan tabbas Abbi ya basu nashi, hannu Amira tasa a cikin veil dinta ta ciro Sarkar, ta miƙa ma tace wannan ne? Murmushi yayi tace tabbas shine. Amira, Humaira da Yarima ne suka bashi. Yanzu kenan wannan uku zasu iya buɗe safe din? Cewar Amira tana kallon Mai Martaba. Murmushi yayi yace tabbas zai buɗe, amma bazan baku safe dinnan ba koh kuma abinda ke cikinta, har sai ku hudun kun kasan mahaɗin rayuwar juna. Kallon rashin fahimta duk suka bishi da shi, Ruhaan ne yace bazai yiwu, you are not to decide for us! Murmushi yayi yace Kanada fikira da saurin fahimta. Amma kasani ni Mohammed Ruhaan Lamido bana magana biyu. Kallon juna Amira da Humaira sukayi dan sai yanzu suka gane mai yake nufi. Amma Abba....dakata Yarima cewar Mai Martaba yana haɗe rai. Shiru Yarima yayi yana kallon mahaifin nashi. Nan gaba kadan zaku gane dalilina nacewa hakan. Kallon juna Humaira da Amira sukayi suna magana ta ido. Girgiza mata kai Amira tayi, dauke kai Humaira tayi tace na yadda. Murmushi yayi yace you are indeed your father's daughter. Allah yaji kan rai, idan ya maida abu objective dinshi, ikon Allah ne kawai ke sawa ya sare. Butt Sisterr...no but's Amii, idan zan bada rayuwata dan gano gaskiyar abinda ya faru da Abbi zanyi. I should be hesitating not you, kinsan Ruhaan, kuna ma da ya'ya a tsakanin ku. Ba haka bane am worried about you! Kullum fada kuke da Yarima, you can't even stand him. It's fine tafada tana kallon Yarima.
Taya kake tsammanin zamu yadda dakai? Cewar Ruhaan yana kallon Mai Martaba. Bakuda wani zabin cewar Mai Martaba.
Amma Abba maganar Hamida fah? Kun tsayar da magana da Uncle fah. Namji ai mijin mace huɗu ne Yarima, cewar Mai Martaba yana murmushi. Shikenan Yarima bayan sallar La'asar za'a daura auren ku. So soon cewar Humaira tana kallon shi. Why? Are you planning to play games with me? Murmushi ta ƙaƙalo tace a'a, amma deep down abinda ta shirya kenan. Butt dole sai da waliyi, kuma Daddy ne waliyin mu a yanzu. Indai Ibrahim ne yanzu haka yana cikin garin nan.
Masaukin baki Mai Martaba yace Yarima yakaisu Humaira. Kallon ta yayi baya ya rakasu yace you can change your mind, zamu iya bin wasu hanyoyin. It's fine bana magana biyu tafaɗa tana wucewa ciki. Sisterr are you sure cewar Ameerah tana riko hannuwanta. Amii it's fine indai hakan zai kawo karshen wannan sarkaƙiya am wiling to do it, besides Yarima is not a bad person barshi da jin kai kawai. Kallon ta Amira tayi ta rungumeta tace express your pain nasan bakya son abinnan just tell me atleast am your sister tafada tana shafa bayanta. Am scared cewar Humaira tana ƙara rungume Amira. I know it's fine cewar Ameerah cikin damuwa. Kuma gashi kamar yanada budurwa cewar Amira cikin kishi. Murmushi Humaira tayi taja hancinta tace Amii ki rage kishi. Idan ma zai aureta ban damu ba. Besides bawai na damu dashi bane balle wacce zai auro. Nidai gaskiya bazai ƙara aure ba indai ya aure ki cewar Ameerah tana kallon Humaira kamar zatayi kuka.
Manyan kaya Mai Martaba yasa ka kawo ma Ruhaan da Asad. Bayan sallar La'asar aka daura aure Aisha Humaira Abdulkarim Kurfi da Aliyu Asadullah Mohammad. Sai kuma Khadijah Ameerah Abdulkarim Kurfi da Mohammed Ruhaann Mohammad. Akan sadakai miliyan ɗaya each.
Kowa yayi mamakin auren Yarima, musamman wadanda suka san akwai baiko tsakaninshi da Hamida.
Jakadiya Mai Martaba ya aika yace takaisu Amira wajen Mama Fulani.
Kunyarta suka dinga ji, sun kuma rasa dalili, kuma basu san wacece ita ba.
Ita kuma sai jan su take, gashi sunyi mamakin mugun kamar da take da Little Ammi. Ita kanta Mama Fulani tayi mamakin kamarta da Ammi.
Sai wajen biyar na yamma Yarima ya samu kanshi dama Ruhaan guduwa yayi ya barshi.
Zama yayi a garden din bayan Masallacin yana so ya gane wani irin feelings yake ji a tattare dashi. One thing is for sure, he is happy he got Amira back. Amma baisan maiyasa ba acen kasan ranshi yake jin ba dadi. Kiran Ammi daya shigo wayarshi ya kalla da murmushi a fuskarshi. Tun daga da Ammi ta gayamai komai, kullum sai yaje gidan ya gaishe ta da safe. Yasan saboda bata ganshi bane yasa ta kira.
Ammu Good Afternoon yafaɗa a tausashe. Amsa gaisuwar tayi tana tambayarshi ya aiki. Ammu ina Adamawa, tareda Mai Martaba. Shiru yaji tayi harya dauka ta kashe kiran ne, sai da ya duba wayar yaga ashe tana jinsa. Ammu bakiso naje bane? A'a Mohammad ni bazan hanaka neman mahaifinka ba. Amma kayi taka tsan-tsan nan ba wajen zaman kabane. Dai-dai da abinci idan ba daga wajen Mama Fulani ya fito ba ban yadda kaci ba harka dawo, Kajini? In Sha Allah. Ammu i just got married. Whatt?? Tafaɗa cikin mamakin abinda ya hau kan Ruhaan yau.
Amira fah? Kanada hankali kuwa Ruhaan? Waka aura? Dariya yayi yace Ammu yanzu wace tambayar zan fara amsa maki. Banason iskanci fah Mohammad! Am sorry Ammu karki damu, ni dan mace ɗaya Allah yayi ni, it's Amira. Da yaushe? Allah mai iko, ɗazunnan fa mukayi waya da ita. Wai aure wasa ne a wajen ku? Ammu kiyi hakuri zanzo in maki bayani.
Brotherr! Cewar Yarima yana riƙo hannunshi, muje koh? Kallon hannun shi da Yarima ya rike yayi sannan ya kalleshi yace lafiyar ka? Am fine, just come with me yafaɗa yana janyo hannuwansa suka nufi sashen Mama Fulani.
Hii Granny yafaɗa yana jan hannun Mama Fulani. Kaii Ali bansan iskanci fa tafaɗa tana tureshi. Kai duk wani.... maganar tace ta maƙale ganin Ruhaan dake tsaye a bayan Yarima. Mikewa tsaye tayi tana kallon fuskar Ruhaan da wani kalar mix emotions tace Mohammad Ruhaan. Da mamaki yake kallon Mama Fulani. Ina kuma tasan sunana. No way, you look like someone i know cewar Mama Fulani ciki turancinta na asalin turawa.
Murmushi Yarima yayi yace Mama Fulani kinga kamar koh? Tabbas Yarima, wannan yaron jinin mune tafaɗa tana shafa fuskar Ruhaan. Cire hannuwanta yayi daga fuskarshi ya haɗe rai ni ba naku bane shine kawai abinda yafaɗa yana jan hannun Amira dake zaune suka fita waje. Kasan wata bishiya ya zaunar da ita, shima ya zauna yana lumshe idanunsa.
Jin tayi shiru batace mai komai ba yasashi buɗe idanuwansa ya kalleta. Miye yafaɗa ganin yadda ta zubamai fararen idanunta. Kimin magana yafaɗa yana matsowa kusa da ita. Mai kake so ince maka Ruhaann? Anything...Wifee yafaɗa yana murmushi. You are my wife once again and am not going to let go of you again. I don't trust that tafaɗa tana kallon cikin idanuwansa. You can take your time, but if you come to me, i will show you the most beautiful love ever yafaɗa yana mata murmushi. Muje yafaɗa yana mikewa tsaye, ina zamu? Tafiya zamuyi mana yafaɗa yana shafa gashin kansa. Tsaya tafaɗa tana shan gabanshi.Na dauka kazo kasan abinda ya faru shekarun da suka wuce? Na dauka kazo ka gyara ALAƘAR iyayen ka. Juyawa yayi ya fara tafiya. Stopp you coward ta fada cikin ɗaga murya. Juyowa yayi ya rike kafaɗunta yace yes am i coward and soo? Ammu ta kasa gayamin which means it's too bad. Banason binciko abinda zai... Stopeettt tafaɗa a hankali tana ƙoƙarin kwace kanta. You are hurting me tafaɗa kamar zatayi kuka. Sakinta yayi ya juya zai cigaba da tafiya sukayi ido hudu da Ammi dake rike da lollipop 🍭 dinta tana hawaye. Amm..wuceshi tayi ta nufi Amira data jingina da jikin bishiyar. Are you okay? 🥺 Murmushi tayi tace Ammi yaushe kika zo nan? Tun sanda Mr Handsome...no Mr Wickedness yafara bullying dinki. Stopeettt Ammi karki kuma cemai haka. But he...no but's Ammi muje tafaɗa tana riko hannun Ammi. Kamar bataga Ruhaan ba haka ta wuce shi.
Kamar yadda na faɗa muku da kunyi aure zan baku wannan safe din, toh gata. Amma inason ku kiyaye abu uku.
Toh mu haɗu a next page 📄📄📄
Chapter 39 · 0% Book details