← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 50

Sashe 50

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Toh mu haɗu a next page....🗞️🗞️
ANA ZATON WUTA A MAƘERA.....🔥
✒️ IBNATU-UMAR ✒️
Page 75&76
Bayan wata hudu.
Zuwa yanzu cikin Ameera ya shiga wata bakwai sai kuma yanzu ne take laulayi, kuma bata iya bacci saida Humaira.
Dare nayi zata dauki pillow ta wuce sashen. Shi kuma Yarima sai dai yazo wajen Ruhaan. Wai idan batajin kamshin Humaira ba zata iya bacci ba.
Tun Ruhaan naji haushi yana mita, har ya hakura Yarima ne ke bashi hakuri.😂🤣
Suna bacci Ameerah ta farka ta tashi Humaira dake gefenta. Sister! Sister tafada kamar tayi kuka. Amiii cewar Humaira tana miƙewa zaune. I want ice-cream please tafaɗa tana ɓata fuska. Sauka tayi ta buɗe freezer din tana addu'ar Allah yasa Du'a bata dauke ice-cream ta tafi sashen Mama Fulani dashi ba. Dan kullum a cen take kwana.
Buɗe freezer tayi kuwa taga wayam. Na shiga uku tafaɗa kamar tayi kuka, akan Ice-cream dinnan Ameerah saita hanata bacci.
Ganin ta dade yasa Ameera ta biyota. Ice-cream dinfa tafaɗa tana tsareta da ido. Amii babu fah? Zama Ameerah tayi ta fashe da kuka. Nashiga uku cewar Humaira tana dafata, kiyi shiru bara in kirasu su siyo kinji? Tafaɗa tana daukan wayarta data kunna haske dashi, maimakon ta kunna bulb.
Hi Babyy cewar Yarima dake aiki a laptop dinshi. Hi tafaɗa cikin damuwa. Mai yafaru yafaɗa yana ajiye laptop din.
Amii keson ice-cream kuma wanda ka siyo mata jiya sun ƙare. Nafi tunanin ma su Ammi ne suka shanye tafaɗa kamar zatayi kuka. Relax few mins.... wannan babyn idan mace ce dole a mamata takwara idan ba haka bazan yadda ba cewar Yarima yana hararar Ruhaan. Murmushi Ruhaan yayi yace ai dole. Gwamma dakasan abinda ya dace an hanata jin dumin mijinta kuma an hanata bacci, wannan babyn halin ubansa yayi.
Kai dai ka faɗi gaskiya an rabata da jarababbe dai cewar Ruhaann yana dariya.
Tashi muje cewar Yarima yana hararashi.
Binshi Ruhaan yayi a baya yana murmushi.
Dariya Humaira dake jinsu kawai takeyi kafin tace Yallabai! Ohh ashe baki kashe ba cewar Yarima yana saka wayarshi jikin phone holder din dake motar.
Yanzu zamu siyo, Allah yasa mu samu inda yake a buɗe. Ameen drive safe Please.
I will, am not tried of seeing your beautiful face. I love you byee tafaɗa tana murmushi. I love you more baby yafaɗa yana kashe wayar.
Ice cream suka jido kamar hauka, sannan suka koma masarautar.
Baki sake Humaira ke kallonsu ganin ledoji a hannunsu, tace don't tell me...yes it is cewar Yarima yana murmushi.
Amii wani flavour kike so Yarima yafaɗa yana fiffito mata da Ice creams din. Zaɓa tayi ya saka sauran a freezer.
Ya masu sallama, godiya Amira tamai. Nifa toh? Am i invisible? Cewar Ruhaan yana kallonta. Fada kake min? Tafaɗa a tana ɓata fuska. A'a wasa yake muje-muje cewar Yarima yana jan hannun Ruhaan.
A kwana a tashi ba wuya.
Ameera ta haifi yarta mace, kamarta sak da Humaira. Kowa abin ya bashi mamaki.
Ruhaan dai yace wayau Humaira tamai suna kwana da Ameerah dan a haifi mai kama da ita.
Huduba yamata da Aisha Humaira kamar yadda yayi alƙawari. Daga Yarima har Humaira abin ya basu mamaki dan sun dauki zancen gabaki daya wasa.
Bayan wata biyu da haihuwar Amira tayi resuming aikinta.
Ya zamana itada Adamawa sai dai weekends. Haka ma Humaira dan saboda Ameerah ta dauki hutu.
Gabaki ɗaya kullum a gajiye suke komawa gida idan sun tashi aiki. Musamman Humaira har yar rama saida tayi.
Shiryawa sukayi itada Humaira dan zuwa ganin Ammi a prison.
Koda sukaje da kyar tazo ganinsu. Duk da abinda Ammi ta masu saida Amira ta tausaya mata.
Ammi why? Just why? Shiru Ammi tayi tana kallon Ameera tace na dade ina harkar safarar kwaya. Mahaifinku keson batamin, shiyasa na kawar dashi. Daga baya kuma naga kunason kawomin cikas sai na jaki a jiki sannan na cigaba da aiwatar da nufina....Enough Ameerah ta faɗa tana hawaye. Jan hannunta Humaira tayi kawai suka fice. They decide to leave everything as there past.
Da wuri Ameerah ta tashi aiki yau Friday, hakan ya sa ta nufi asibitin Humaira.
Dauke da Humaira a baby carrier. Tayi wayau sosai. Knocking tayi amma shiru, duk tunaninta Humaira nada patient ne. Buɗe kofar tayi a hankali amma ga mamakinta taga tana bacci. Murmushi tayi ta tura kofar a hankali ta zauna a gaban Humaira tana kallon yadda fuskarta ke wani irin sheƙi. Baby Humi ce tadan ja hancin Humaira da tiny hands dinta. Buɗe ido tayi tana kallon su da murmushi. Bacci dai sister cewar Amira tana kallon Humaira. Bazaki gane bane na gaji tafaɗa kamar zatayi kuka.
Sisterr amma baccin nan baiyi yawa ba kuwa? Shiru Humaira tayi tana tunani kafin ta saurin kallon Ameerah. Murmushi tayi tace yes we are thinking about the same thing. Janyo drawer gabanta tayi ta dauko PT strip ta shige bayin dake office din.
Tsaye Ameera tayi cikin kosawa, knocking toilet din tayi tace ya ake ciki ne wai? Am coming Amii tafaɗa tana kurawa lines din ido.
Fitowa tayi ta rungumeta tace it's... Ihu Amira tayi suka kara matse Baby Humi dake tsakiyar su. Ganin ta fara koke-koke yasa suka saki juna. Ke mahaukaciya it's negative cewar Humaira tana kallon Ameerah. Wallahi nidai ban yadda ba, ki kuma wani. Share kawai Humaira tafaɗa tana buɗe file din gabanta.
Subhanallahi ina da operation by 2 tafaɗa tana kallon agogo dake nuni da karfe 4.
Ina zuwa Amii tafaɗa tana ficewa cikin sauri. A bakin kofar OR din ta ci karo da Yarima yana cire facemask. Saurin mai kike yafaɗa yana rikota. Opera.... it's fine, i have taken care of that. Butt... Nina hana su tashe ki, banson a takura min baby na yafaɗa yana kashe mata ido. Ammaa...ba wani abu karki damu kinsan ba'a san masu juna biyu suna wahala da yawa. Nifa banda komai, we just checked tafaɗa tana ƙoƙarin maida kwallarta.
Murmushi yayi ya riko hannunta zuwa office dinshi dake asibitin.
Munyi shekara biyu da aure? Yafaɗa yana kallonta. A'a but an kusa. When did we consummate our marriage? About a year tafaɗa tana kallonshi. Miye na damuwa toh Aishh? Baka damu ba? Tafaɗa tana kallonshi. Idan zamu shekara ɗari tare bazan damu ba Aishaaa.
Just do what makes you happy! Kinji yafaɗa yana shafa cikinta, gyada mai kai tayi. Murmushi yayi yace mai yasa kikeson cikin toh ke? I want to a mini you tafaɗa tana ɗage mai gira.
You have it already yafaɗa yana ɗaukanta ya ajiye akan gadon marasa lafiya. Key ya saka a kofar.
Hannunshi yasa ya yaye rigar dake jikin sannan yayi loosing belt din suit din wandon suit din datasa. What are you doing? Tafada tana zaro ido! Looking for a mini me yafaɗa yana kunna scanning machine din. Yawo yake dashi akan marararta a hankali. Saurin kallonshi tayi tace what is that? A baby yafaɗa yana mata murmushi. We are pregnant yafaɗa yana dariya. Weee cewar Humaira tana murmushi. I think it should be about 2 months. Nifa daman na zargi haka daga sanda kika fara wannan baccin naki yafaɗa yana murmushi.
Koda ta gayama Ameerah murna tayi sosai, suka rungumeta juna. A'a nidai kiyi hakuri Amii kisake ta mai kama dani takeso bamai kama dake ba. Yarimaa cewar Amira tana murmushi.
Bayan wata bakwai Humaira ta haifi yaranta maza yan biyu kamar su ɗaya sak da ubansu. Arman da kuma Aman
Murna sosai wannan ahalin sukayi.
Zuwa yanzu idan Humaira da Amira sukaga dumbin rahamar da ubanjin ya masu, suna ganin abinda ya faru a baya bakomai ba.
Mahmoud ya rasa komai nashi a gobara, hakan yasa ya haukace tuburan, yana bin bola da kuma tsince tsince a titi. Idan ka ganshi sai ka rantse ba shi bane.
Halin da Mahmud ya shiga ne yasa Nisa ta nustu ta koma ga Allah.
Sannan tasha zuwa News Buzz da kuma A.K Group dan neman yafiyar Ameerah amma ba'a bari ta shiga.
Ta samu aiki a wani babban restaurant dake Abuja.
Bayan shekara biyar.
Zaid, Zayn, Du'a, Humaira da kuma Aman da Arman suna wasa abinsu, Ameerah da Humaira ne suka fito zasu fita lunch dates su Yarima na jiransu. Mammi cewar Aman yana nufo Ameera da gudu. Zan biki please yafaɗa yana taɓe baki, kaii, kaiii amma na dauka na faɗa maku zamu fita kuma badaku zamu ba cewar Humaira tana tsareshi da ido.
Toh ai ni ya tambaya koh cewar Ameerah tana shafa curly hair dinshi. Zokaji tafaɗa tana daukanshi suka matsa gefe. Magana tamai, ta saukeshi ya juya da gudu ya koma wajen yan uwansa.
Ba'a ma yara faɗa fa! Cewar Ameerah tana shiga motar. Ai naga mu haka aka raine mu cewar Humaira tana harararta.
Ba wanda ya kuma cewa wani ƙala har suka isa wajen.
Ciki suka shiga suka samu su Ruhaan ,sukayi placing order.
Nisah ce ta ajiye masu abinci, tana ɗago idanunta suka haɗa da Ameerah data zuba mata ido.
Meeraahh.....tafaɗa tana kallon Ameerah da mamaki. Na dade ina nemanki.... please cewar Ameerah tana ɗaga mata hannu. It's my sister's birthday lunch. Do not ruin it. Nasan mai kike cewa, kije nina yafe maki tuntuni. Godiya Nisah ta maga tabar wajen cikin dumbin nadama da dana sani.
They had lots of fun kafin su koma gida.
Auren su Humaira is what many people envy and dreamed of. Duk da suna samun ups and downs kamar kowani aure amma they settle it calmly.
Duk yadda Ameerah taso Humaira tayi joining A.K Group taƙi. Hajiya Hamdiyya kuwa duk tsanar data daurama Ameerah ta bari a yanzu dan taga Ameerah ma batada lokacin ta.
Dama kishi take da Ameerah saboda Abbee da kuma dukiyarsa.
Tsaye Ameera take a balcony tana kallon su Zayn dake basketball a kasa.
Coffee cewar Humaira tana miƙe mata. Amsa Ameerah tayi, tayi sipping kaɗan ta miƙa mata.
Amii tunanin mai kike yi? Uhmm DUNIYAR MU tafaɗa tana murmushi.
Kallonta Humaira tayi tana jiran karin bayani. Mun taso tamkar HANTA DA JINI amma muka rabu. Na kulla ALAƘA da mutane da dama amma sunci amanata. Na haɗu da mutane kala-kala a rayuwata GAGGARARRU, masu kirki da masu ha'inci. Na haɗu da Ruhaan we are like TWO SOULS WITH ONE HEART (RUHI BIYU ZUCIYA DAYA) shima muka rabu. A sanda na gane kashe Abbe akayi na dau aniyar FANSA. Gabaki daya ba wanda nake zargi sai Hajiya Hamdiyya amma Ammi...shiru tayi ta kasa ƙarasa zancen dan har yanzu abin na kona mata rai.
Wannan shine ANA ZATON WUTA A MAƘERA SAI GATA A MASAKA cewar Humaira tana dafata.
Amma yanzu gashi komai ya wuce. We have the bestttt husbanda. Lovely kids and a good family. What else do we need Amii? Sai dai mu cigaba da gode ma Allah da kuma taimakon na ƙasa damu.
Kuma rokeshi yabarmu mu tsufa da yaran mu tafaɗa tana tunawa dasu Abbe. Rungume juna sukayi suna tunanin rayuwarsu ta da.
Are we not part of the family cewar Ruhaan yana kallon su. Juyawa sukayi suka kalli Ruhaan dake tsaye shida Yarima. Rungumeshi Ameerah tayi tace of course you're. Won't i get a hug cewar Yarima yana kallon Humaira rungumeshi tayi tana murmushi.

Toh a nan zan tsaya da rubuta wannan littafi. Kuma ina fatan duk wanda ya karanta ya dauki lesson ɗaya zuwa biyu.
Alhamdulillah, Alhamdulillah, godiya ta tabbata ga Allah daya bani damar fara rubuta wannan littafi cikin Sa'a yakuma bani damar gamawa lafiya, duk wanda na ɓata ma rai a ta dalilin rubutun wannan littafi yayi hakuri, dan Adam ajizine, Allah ya yafe mana baki daya,Ina godiya ga dukkan fans dina na boye da kuma na zahiri, without you it would have never have been possible ❤️🫂. Nagode kwarai da soyayyar dakuka nunamin da kuma littafin nan. Allah ya barmu tare.Kura-kuran danayi ina neman afuwa, Allah yabar zumunci 😍. Duk wanda yason ya karanta wannan littafi ya amfana da wani abu a ciki, ko kuma ya nishaɗantu, yasa ni a addu'ar sa Allah ya biyamin bukatuna pls. Mun gama ANA ZATON WUTA A MAƘERA sai kuma mun haɗu a littafi na na gaba ina fatan lalitar ku a cike take dan paid book zan yi.
Bissalam,
Taku har kullum.
✒️IBNATU-UMAR ✒️
Chapter 50 · 0% Book details