← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 50

Sashe 28

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

Mukhtar ne ya buɗe mata mota ta shiga baya, ya buɗe gaba ya zauna , sabon driver dayayi hiring yaja motar.
Ma'am Mohammed yayi resigning shiyasa nayi hiring wani driver. Good tafaɗa tana duba wayarta ba tare data Kalli inda yake ba.
Ina muka nufa? News Buzz koh Company.
News...no muje company, i need to see how things are going dan Hamdiyya ba abun yarda bace.
Murmushi kawai Mukhtar yayi baice mata komai ba, koda driver yayi parking. Saukowa yayi ya buɗe mata, kallonshi tayi na 3sec ta dauke idanunta akanshi.
Ciki suka nufa tana tafe Mukhtar na bayanta. Wannan sabon driver, ina kasamo shi? Daya daga cikin securities din kine yafaɗa yana tsayawa. Card Amira ta saka yayi scanning lifter ta buɗe wacce aka rubuta C.E.O a sama, ta gefen inda Amira ta shiga Mukhtar ya danna botton itama ta bude zai shiga kenan saiga Hajiya Hamdiyya. Baya ya matsa yana sauke idanunshi ƙasa yace Good Morning ma, Mukhtar kenan tafaɗa shigewa cikin lifter itada sectary dinta, har lifter zata rufe Hajiya Hamdiyya ta danna botton ta kuma budewa kallonshi tayi tace shigo. But Ma..just come in tafaɗa tana kallonshi.
Shigowa yayi yana sauke idanunshi kasa, Amira ta gama Iddan kenan tafaɗa tana kallon shi, refrain from asking me about Miss personal life please. Mukhtar kenan kana pretending kamar nida Amira kake serving bayan ba hakan bane. Murmushi gefen baki yayi yace Aikina shine kula da tsaron iyalan marigayi, kuma ina kokarin sauke nauyin daya hau kaina. Miss bata taɓa tambayata akan kiba, so i will like it if you will do so. Lifter ce ta tsaya a floor din da Hajiya Hamdiyya zata fita, kallonshi tayi tace meet me in my office later. Okay Ma'am yafaɗa yana sauke kanshi kasa.
Zakiyya kina ganin Mukhtar zai yi accepting offer dinnan kuwa? Ma'am shima mutum ne fah, yanada desire, kudii dole zaiyi tempting dinshi. Shikenan bari yazo muji tafaɗa tana zama akan kujera office dinta.
Office din Amira ya shiya harta zauna ta sa Isma'il (sectary dinta na A.K Group) ya kawo mata files din da take buƙata dan tanason barin nan bayan lunch ta nufi News Buzz da take da aiyukan da sukafi na nan. Balle botton din inner suit dinta tayi tana naɗe hannun rigar. Kallon Mukhtar tayi tace naga ka dade. Sorry Miss... it's fine dama ce maka zanyi kasa Faith ta haɗa min duk wasu important files na News Buzz kafin lunch zanzo, kuma Aminullah, Ishaq da Michael su kasance a meeting hall dinmu by 2pm.

Toh mu haɗu a next page 📄📄📄

ANA ZATON WUTA A MAƘERA...🔥
✒️IBNATU-UMAR ✒️

Page 45&46
Aiki ta tarar da yawan gaske fiye da yadda tayi tsammani saboda tana aiki daga gida ma. Ruwa ta sha, ta , jujjiya wuyanta daya ƙage, ajiyar zuciya ta sauke, ganin ta gama aikin. Kallon agogo tayi taga biyu saura minti uku. Alwala ta daura ta fito ta shiga dakin dake office din ta saka dogon hijab dinta tayi sallah.
Bayan ta fito, gyara fuskarta tayi ta fito, cikin sauri Ismail yabi bayanta yana kiran wayar Mukhtar dan ya sanar mai cewa Amira ta gama. Tana saukowa a lifter taga Hajiya Hamdiyya na shirin fita. Dakatawa tayi ta dawo ta tsaya tana karewa Amira kallo. Wucewa Amira ta sakai za tayi dan koh mai kama da Hajiya Hamdiyya batason gani balle ita. Kin kashe aure kinji dadi koh? Ko da yake ba yau kika saba ba, bata kulata kawai ta wucewarta duk da maganganun Hajiya Hamdiyya sun mata zafi amma ba wanda ya isa yace hakan idan ya kalleta, yi tayi kamar ma ba da ita Hajiya Hamdiyya ke magana ba.
Kallonta Mukhtar yayi yace Miss idan kin gaji, muje gida kawai ki huta karkiyi stressing kanki da yawa. It's fine i can do it tafaɗa tana ballo magani ta buɗe gorar ruwa ta sha. Koda suka isa News Buzz already su Ishaq suna jiranta a meeting hall din da tace.
Bayanin abubuwan da suka faru a boye bayan bata Company suka mata.
Ba wani movement tsakanin Hamdiyya da Sa'ad Wambai? Babu Ma hasali ma kamar fada suke yanzu cewar Ishaq yana mika mata tab dinshi. Kallon video tayi ta miƙa mai tab din tace Ishaq, Aminullah, Michael da Haroun. Ina son ku bani aron hankalin ku. Ina son kumin binciken accident da mukayi da Ummi 18 years ago tafaɗa tana kallon su. Kallonta Mukhtar yayi yana saka abubuwa da dama a ranshi. Yes Ma'am. Amma zai dan dauki lokaci duba da cewa an dade da yin accident din. I know just get all you can tafaɗa tana kallon chain din da Abbee ya samata a wuyanta randa zai tafi Australia.Gabaki daya ta rasa gane miye a tattare da wannan chain din....saurin mikewa tayi tunawa da tayi cewa Humaira ma nada chain din. Kallonta duk suka yi ganin yadda ta zabura lokaci ɗaya, basarwa tayi ta koma ta zauna. Zaku iya tafiya amma Aminullah da Haroun ku jira tafaɗa tana kallonsu. Fita Mukhtar yayi shida Michael da Ishaq.
Aminullah and Haroun listen to me carefully tafaɗa tana mikewa tsaye. Inason ku bincika mim duk waɗanda Abbee yakw hukda dasu dayana raye. Ina son sanin komai da komai akansu da iyalansu da kuma irin hulɗar da suke da Abbee. Sannan Mahmud included. Yes Ma'am suka haɗa baki waje faɗa. This should be a secret between us koh Mukhtar banson ya sani. And you should report very single detail to me tafaɗa tana kallonsu. Yes Ma'am suka faɗa. But Ma'am cewar Aminullah , go on tafaɗa kallonshi. I understand idan kika ce mu binciki Mahmud duk da kasancewar shi ex husband dinki. Amma binciken Abbee da mutanen sa kina ganin Mukhtar bazai gane ba. I know siyasa na zaɓe ku, bakuda surutu and you are the most suitable candidates for this job. Amma it seems i made the wrong choice tafaɗa tana jefan shi da wani irin kallo, Sorry Ma'am yafaɗa yana risunawa. Card ta ajiye masu ta cewa duk wani abu da kuke bukata na kudi dangane da aikin nan dana baku kuyi using card dinnan.Tana gama fadar haka ta fice daga hall din dan tanada aikin yi da yawa a nan ma.
Humaira POV
Seminar dinsu na likitoci taje. Wajen awa biyu sannan aka tashi. Koda ta fito Mota ta wuce straight remote control din Mercedes dinta ta danna, buɗe motar tayi har zata shiga taji an kira sunanta. Dr Aisha Humaira. Hade fuska tayi ganin waye, shima haɗe rai yayi yace baki iya gaisuwa bane. Rolling eyes dinta tayi tace ai baka koya mim ba. Kee yafaɗa yana cige lips, miye tafaɗa tana kulle kofar motar ta jingina a jiki. Kallon agogon dake daure a hannunta tayi tace minti uku gareka ka faɗi abinda yasa ka tsayar dani ina aiki a asibiti. Kwafa yayi yace angaya maki ni banda aikin ne, shiru tayi ba tace mai komai ba idanunta na kan agogon minti uku nayi ta buɗe motar ta, ta shige ta wuce ta barshi a wajen. Mamaki ya hanashi magana, Asadullah cewar Usama yana ƙarasowa kusa dashi. Kasan kanada operation yanzu amma.ka tsaya a nan, kaida waye cewar Usama yana kallon motar Humaira data wuce. Ina ruwanka dan sa ido yafaɗa yana yin gaba. Yarimaa ka jira ni, chak Asadullah ya tsaya ya juyo ya kalli Usama kamar ya rufeshi da duka, bance karka ƙara kirana Yarima ba? Murmushi yayi yace idan ba haka nace ba ai bazaka jirani ba. Yafaɗa yana yin gaba. Tsaki Asadullah yaja ya nufi motar da suka zo da ita.
Parking tayi cikin gaggawa ta sauko, office dinta ta nufa koh zama ba tayi ba ta ɗauki lapcoat ta sauko cikin gaggawa dan saura mintina kaɗan ya rage time din daya kamata ta shiga OR din.
Wanke hannunwanta tayi, ta daga su sama. Kofar OR dince tayi sliding, shiga tayi wata ta taya ta saka gloves. Kallonta tayi tace Dr din yazo? Eh Dr gashi cen tafaɗa tana nuna mata Dr Aliyu dake sanye da mask, hakan yasa bata ganeshi ba. Gaisuwa suka ma juna irin nasu na likitoci. Suka fara aikin da zasuyi. Scalpel yafaɗa yana mike ma Nurse din hannunshi, kallonshi Humaira tayi kamar tasan muryar amma ta rasa tuna inda ta sanshi, basar da abin tayi suka cigaba da aikin dake gabansu. Sai wajen 5 suka fito. Wanke hannunta tayi ta juya zata fita taga yazo ya wuceta. Youu!! Tafaɗa dan tsantsan mamaki, juyowa yayi yana kalle-kalle kamar baison da shi take ba. Mr Stalker am talking to you tafaɗa tana wurga face mask din data cire zuwa cikin dutsbin.
Kallon sama da kasa ya mata, yace nine stalker? Toh wa nayi stalking yafada yana kallonta. Karka raini min hankali am i neurologist and a psychologist as well. So whatever game you're trying to play with me, don't do it. Tana gama fadar haka ta wuce shi cikin bacin rai.
Wayarta ta ciro ta kira Amira, Hi sister tafada tana hamma daga jin yadda take magana ba karamin gajiya tayi ba. Baki iya amsa sallama na sai Hi? Oh sorry Wa'alaikumussalam tafaɗa tana murmushi. Are you angry? Cewar Amira dake haɗa kayanta cikin handbag dinta dan itama gida zataje. No am not, why will i? Murmushi tayi tace daga tambaya 😂, ko ma miye zaki gayamin ai. Forget that, kin koma gida ne? A'a yanzu zan tafi tafaɗa tana nufar kofar fita. Okay nima zan taho, bye.
Koda Amira ta isa gidan, Humaira bata dawo ba. Wanka tayi, tayi sallar Magrib sai lokacin Humaira ta shigo.
Bayi ta wuce straight tayi wanka, itama ta dauro alwala.
Kallon Humaira data gama shiryawa Amira tayi tace Sister. Ya akayi? Cewar Humaira tana taje kanta. Kin tuna wannan chain din da Abbee ya bamu? What about it? Ina naki inason ganin abune tafaɗa tana ciro tata a wuyarta. Janyo bedside drawer Humaira tayi ta dauki chain din ta miƙa ma Amira.
Kallonsu ta tsaya yi, sai kuma tayi kokarin hadasu. Sister lookk! Juyowa Humaira tayi dan ganin mai Amira take magana akai. Key 🗝️ it's a keyy, mukulli ne tafaɗa tana nuna ma Humaira. Yes, i know tafaɗa tana dariya😂. Kallonta Amira tayi tace yaushe kika sani? A gabana ya rabashi yasa su a jikin chain a week to kafin ya bamu i guess tafaɗa tana tunani. Toh mukullin miye? Yace maki wani abu about it? No baice min komai ba. Kuma kinsan niba irin ki bace ban tambaye shiba tafaɗa tana murmushi.
Sisterr tafaɗa tana ɓata fuska, daiya kuma tayi tana jan kumatunta tace am just kidding. But he was on a phone call that day, gyara zama Amira tayi ta nutsu tana sauraren Humaira....wayarta da tayi ƙara ne ya katse masu maganar da suke yi. Mammi help, Mammi help cewar Ammi cikin ruɗewa. Hannunta daya fara rawa ta dafe tace Ammi what happened? Sun tafi da Zayn. Whatt!! Tafaɗa a zabure tana mikewa, kuda waye? Waye ya dauko ku a school? Hijab kawai ta zara ta fice a mota Humaira na kiranta koh tsayawa ba tayi.
Mukullin Mota itama ta dauka ta bi bayanta.
Hanging wayarta tayi a jikin phone hanger dake motar ta fara kiran Mukhtar. Mukhtar kaje school din su Zayn right now!! Miss what happened yafaɗa cikin tashin hankali, i don't know kaje kawai. Ganin hold up yasa ta yanke wa, tabi ta hanyar construction road. Kiran Humaira dake shigowa ta dauka, wai mai ya faru, Ina zaki? Zayn...bansan mai ya sameshi ba but Ammi ce ta kirani.
But yanzu mu kayi waya da drivern su yace ya ajiye su a gida. Whattt tafaɗa tana faka motarta. Yes ki jirani ganin nan ina karasowa ina ganin ki. Trailer ce ta taho da gudun gaske tana nufar motar Amira. Amii start your car fastt! Cewar Humaira data hango trailer data nufota. Buttt...just the fucking car Humaira ta faɗa a tsawace. Jikinta na rawa Amira ta kunna motar ta taka ta da gudun gaske, Amii listen to me carefully trailer bayan mu ke take bi. Just drive straight 60km away zamu fita ta kan main road. Tsaki Amira taja tace koma waye mai aiko trailer nan dakiki ne, na tsani maimaita aji wallahi. Karki kashe wayarki, trailer nan looks familiar cewar Humaira gabanta na faduwa. Gudu suke sosai a mota, haka shima driver dake tuƙa trailer.
Shiga tsakanin motar Humaira dake bin Amira a baya yayi daidai karshen titin maimakon Amira ta hagu sai ta mike. Gudu drivern ya ƙara ya nufi motar Amira, reverse Humaira tayi ta kure speed dinta zuwa karshe, ta shiga tsakanin trailer da motar Amira. Sisterrr cewa Amira tana zaro ido ganin yadda motar Humaira ke tumbling akan titi, sakin sitiyarin motar tayi itama motarta ta haɗe da bishiya.
Reversing drivern trailer yayi ya wuce da gudun gaske.
Sanda Mukhtar yayi tracking location dinsu, already Humaira taji jiki dan koh nunfashi ba tayi. Haka aka sasu a ambulance, dishi-dishi Amira ke kallon kan Humaira da jini ke zuba kamar an kunna famfo. Sis.te.rr tafaɗa tana rufe idanunta.
Cikin gaggawa aka amshe su, aka shiga dasu cikin asibitin su Humaira dake nan ne yafi kusa dasu. Dr Aliyu daya fito zai tafi ne yaga an shigo dasu, kallon fuskar yayi kamar ta Humaira, har zai wuce sai kuma ya dawo zaro manyan idanunshi yayi ganin ita dince da gaske, Keee yafaɗa yana bubbuga fuskarta. Kallon Nurse dake kallonshi yayi a fusace yace zaki kawo kayan aiki koh kuma sai ta mutu kin tsaya kallona. Gloves ya saka ya amshi clipper ya aske gashin Humaira dake gefen kunnenta na dama. Allura ya mata sannan ya fara dinke wajen. Handkerchief Usama ya ciro yana goge ma Asadullah zufar dake keto mai, koh ta miye ohho? Cewar Usama cikin mamaki, dan ba yau Yarima ya saba treating accident patients ba.
Yarimaa bata numfashi fa cewar Usama yana kallonshi cikin mamaki. Whatt!! Yarima ya faɗa cikin tashin hankali, she can't die, she must not die yafaɗa yana haɗe hannunshi biyu waje ɗaya ya fara compressing chest dinta...1,2,3....1,2,3... Kusa mata oxygen yafaɗa yana kallon Usama. Buttt Yarima akwai...kasa mata nace yafaɗa a tsawace. Nan take suka fara aiwatar da abinda ya sasu. Please 🥺, Please 🥺, Please Aishh 🥺. Yafaɗa yana cigaba da abinda yake. Ta dawo stop, stop, stop Yarima cewar Usama ganin kamar Yarima ba'a hayyacinsa yake ba. Sauka yayi ya dafe bangon dake gefensa saboda jirin daya fara dibansa. Amira da'aka sama ruwa ce ta buɗe idanunta dishi-dishi take ganin Ruhaan a gefen gadon da take. Tashi tayi duk da jirin dake dibanta ta fincike drip din, tace fitaa, waya kawo ka nan? Tafaɗa tana jan kwalar rigarshi, Ka fita na..ce tafaɗa tana sumewa a jikinshi. Murmushi yayi ya dauketa ya mayar da ita kan gadon ya maida mata drip din.
Tsayawa kallonta yayi, yana kallon wrist dinta daya kumbura.... wayarshi data fara ringing ne ta katse mai tunanin da yake. Dauka yayi cikin tsantsan ɓacin rai ya fara magana. Miye amfanin ka idan har hakan zai faru da Amira a karo na uku? Kana yin mai? Save your apology i don't need it. Idan wani abu ya samu Humaira koh Amira wallahi...sai kuma yayi shiru yana dunkule hannunshi. Bakasan mahimmancin su a cikn rayuwata bakoh? Shut upp and stop apologising. Ina san sanin wani dan iskan ne ke wannan jahilin aikin. Not once or twice but thrice!!
Sawa Dr Aliyu yayi akayi moving Humaira zuwa daki.
Zama yayi akan kujera gefen gadon yana kallonta, wipes ya dauko ya goge jinin daya ɓata fuskarta. Hannunta ya riko ya goggoge shima.
Kallonshi Usama ya tsaya yi da mugun mamaki ganin abinda yakeyi, Mamakine ya kusa kashe shi a sanda yaga hawaye na suntiri akan fuskar Yarima.
Toh mu haɗu a next page...📄📄📄
Chapter 28 · 0% Book details