← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 50

Sashe 38

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

gefe. Sister na nemanki fah, yafaɗa yana leka fuskarta. Karka ƙara min maganar ta. Uhmm okay bazan yiba, amma bari na gaya maki wani abu Amira. Koh miye Humaira tayi bazata yi abu dan ta cutar dake ba. Zata iya sadaukar da rayuwarta akan ki. Bansam mai ya haɗa kuba but meet her and talk to her. Kinji yafaɗa yana kallonta. Ganin tamai banza yasa ya bata waje. Tashi tayi ta shiga cikin gidan, Daddy dake parlourn ta gaisar sannan ta wuce sama. Ina ta nemanki, ina kika shiga? Cewar Humaira tana kallonta. Banza tayi da ita ta dauko bathrob ta shiga bayi ta banko kofar. Toshe kunnuwanta Humaira tayi tana murmushi. Wanka tayi ta fito, tana shiryawa. Amii cewar Humaira tana riko hannunta. Miye cewar Amira cikin jin haushi. Am sorry tafaɗa tana rike kunnuwanta. Sorry for your...shush listen to me please cewar Humaira tana mikewa tsaye. Ban jiba samun bayanan nan ba, duk nasan cewa this is not an excuse tunda tare muke kwana kuma tare muke tashi. But i can't risk your life Amiii, i did everything to protect, idan wani abu yasameki bazan iya yafe ma kaina ba. Just shut up cewar Amira a fusace. Do you think you're my mother or what? Am your twin sister? Rana daya aka haifemu, bafa ke kika haife niba. I deserve to know everything and we are supposed to share our pains and burden. Selfish woman tafaɗa tana ficewa daga dakin. Huci Humaira ta furzar ta dafe kanta daya fara mata ciwo, Subhanallahi tafaɗa jin ciwon na karuwa. Saurin dawowa Amira tayi ta kalli Humaira tace stop faking sickness dan bazan hakura ba. Ganin ta mata banza yasata tsugunna dai-dai ita tace Sister are you ok? How will i be okay? when my sister has a terrible temper tafaɗaa tana murmushi. Hararata Amira tayi tace don't do that again. Toh kiyi hakuri tafaɗa tana kallonta da murmushi. Shikenan na hakura tafaɗa tana dungure nata kai. Innalillahi Wa Inna Ilayhi Raji'un cewar Humaira tana kallon Amira kaina fa ciwo yake. Sannu tafaɗa tana ballo magani ta bata ta sha. Washe gari da yamma sai ga Issy tazo wajen Humaira. Ciki Humaira ta shigo da ita suna hira. Amira na ganinta ta haɗe rai. Murmushi Issy tayi tace Bestt kinsan mai? Sai kin faɗa cewar Humaira tana kallon Amira dake zaune a gefen su tana aiki a laptop. I missed those days da muke hanging out tare. Let's do it again kisa rana. Toh tafaɗa suna cigab da hirarasu. Magrib nayi Issy tama Amira sallama ta tafi. Shigowa Humaira tayi daga raka Issy tace Amiii...uhmmm cewar Amira tana haɗe rai. Murmushi tayi tace miye kuma ya faru? Let's do it again kisa rana, yenyenyenyenyenyenyen 🙄 tafaɗa tana hararar Humaira. Dariya tayi tace na shiga uku ni Aisha. Amii idan nayi aure ya zakiyi? Zaki iya mutuwa koh? Kallon banza ta mata tace ni ba wannan nake nufi ba. Amma idan Issy dinnan tazo sai ki dena kulani sai ta tafi kuma kizo kinata wani shishige mun. Murmushi tayi tace stop being jealous. Issy daban ke daban kinji my girl tafaɗa tana jan kumatunta. Zakiji hang out? Cewar Ameera tana kallon Humaira. Idan bakya so bazan jeba, shikenan? Cewar Humaira tana murmushi. Eh karki je, zan fara tsanar Issy idan kina nuna mata wannan son. It hurts and i don't like it. It's fineee, relaxx cewar Humaira tana rungumeta. Dole tayi wani abu dan gyara ALAƘAR issyy da Ameera. Weekend suka shirya zuwa Adamawa kwata-kwata basu gayama Daddy abinda zasu jeyi a cen, illa Seminar da Humaira tace zata Amira kuma zata rakata. Sun fito suna breakfast sukaga su Zayn sun sauko an ci gayu. Sun sha shadda Navy Blue abinsu sai maiko take harda hular su. Ammi ma ta saka doguwar riga irin shaddar dasu Zayn suka sa. Ta rataya yar karamar gucci bag dinta. Da mamaki Amira da Humaira suke kallonsu. Dan weekend basa tashi da wuri. Good Morning Mammi, Good Morning Mommy suka haɗa baki wajen faɗa. Ina zaku haka? Cewar Humaira tana kallonsu. It's a secret cewar Zaid yana zama kan kujerar. Nanny please help us with the food cewar Zayn. It's fine Jamila zan zuba masu ki huta kema cewar Humaira tana serving dinsu Zaid. Kusan a tare suka gama, suka fice waje. Kallon Ruhaan dake sanye da yadi mai laushin gaske Amira tayi tace Good Morning. Morning Baby Girl yafaɗa yana murmushi. Har kun shirya cewar Asadullah yana kallon su Zayn da suka fito. Yes Uncle Asad cewar Ammi. Wai binmu zasuyi? Cewar Humaira tana kallon su. Eh binmu zasuyi cewar Asadullah yana kallonta. No way suka haɗa baki itada Amira wajen faɗa. Kaine ka haɗa komai kenan? Tafaɗa tana hararshi. Kayan jikinku ina kuka samo su? Uncle Asad ne ya kawo cewar Zayn yana turo baki. Kuma Uncle Moh yamana alƙawarin zuwa Adamawa cewar Ammi. Badan sunso ba haka suka hakura suka tafi dasu. Koh a Airport duk inda suka wuce sai an kalle su. Ruhaan ya dauki Zaid, Asadullah ya dauki Zayn. Sai Ammi ta ruko hannun Amira da Humaira. Uncle Asad yanzu gidanku zamuje. Murmushi yayi yace masu eh. Amma Ammi tace wai gidan ku palace ne kato kamar haka cewar Zayn yana buɗe hannuwansa. Murmushi yayi yace kamar haka dai yana buɗe hannuwansa. Woww your mom and dad live there? Cewar Zaid. Gyaɗa mai kai Asadullah yayi. Kallon Ruhaann dake gefenta Amira tayi tace are you sure about this? Idan bazaki iya ba...girgiza mata kai yayi yace karki damu. Nima inason ganin tushen Ammu na. Ina son ganin Mahaifina duk da fushin danake dashi. Ina son ganin ahalina...katabbata? Kalli cen yafaɗa yana nuna mata window dake gefenta. Juyawa tayi ta ƙalla kawai ya daura kanshi akan kafaɗarta, ya lumshe idanunsa. Ɗagani dallah tafaɗa tana tureshi, amma koh gezau baiyi ba.Harta gaji ta kyaleshi.
Chapter 38 · 0% Book details