← Book details Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 50

Sashe 32

Ana Zaton Wuta A Makera Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

ANA ZATON WUTA A MAƘERA....🔥

✒️IBNATU-UMAR ✒️

Page 49&50
Banson koma miye kakeson faɗa...i hate you and i hate seeing your face tafaɗa tana nunashi. Murmushi gefen baki yayi yace wannan kuma karya ne. Magana zata kuma yi Humaira ta riko hannunta, kallonta tayi cikin ɓaci rai, girgiza mata kai Humaira. Kwace hannunta tayi tana komawa kujerar da take zaune ɗazu ta dauki Novel din da take karantawa ta cigaba da karatunta. Sit please cewar Humaira tana kallon Ruhaan. Zama yayi yana mata ya jiki ta amsa da Alhamdulillah. Kafin yace wani abu Asadullah ya shigo rike da parcel 📦 yace Amii ga sakon ki. Amsa tayi tana kallonshi da mamaki tace waya kawomin sako? Kuma asibiti for that matter. Buɗe ki gani mana cewar Humaira tana kallonta.Buɗewa ta fara ƙoƙarin yi, kallon Asadullah tayi tace sunan nan ya fita a bakinka sunanta Amira. Matsowa kusa da ita yayi ya daura hannunshi akan goshinta tayi saurin bige mai hannu tana hararshi.... girgiza kai yayi yace gashi kanki ba zafi balle ince kin samu matsala a brain dinki ne...karar faduwar kwallin da Amira dake hannun Amira yasa duk suka maida hankalinsu kanta. Kafin su farga damai ke faruwa ta faɗi kasa numfashin ta ya fara sarkewa kamar zata mutu, tsige cannula hannunta Humaira tayi ta sauka akan gadon da kyar saboda ciwon da jikinta keyi. Ɗago kanta Ruhaan yayi ya daura akan cinyarsa. Asadullah dahar zai fita nemo Inhaler ne ya tsaya ganin Ruhaan ya ciro Inhaler a aljihunsa yana ƙoƙarin samata a bakinta. Tsugunnawa Humaira tayi tana riko hannu Amira da hawaye ke fita ta gefen idanunta. Ganin ta fara maida numfashi tana lumshe ido, yasa Ruhaan sakin ajiyar zuciya. Daukarta yayi ya ajiye ta akan couch din dake dakin.
Kallon Humaira Asadullah yayi yace lay down please, jiri zai iya ɗibarki. Kwanciya tayi, tana rufe idanunta, jin an fisgi hannunta yasata buɗe ido. Bakida hankali ne, kalli yanda jini ke zuba cewar Asadullah a tsawace yana ƙoƙarin saida jinin dake zuba daga hannunta, saidai ya gyara ya mayar mata da drip din ya saki hannunta.
Kallonta Ruhaan daya dauki kwalin da Amira ta yardar. Miye kakeyi cewar Asadullah yana kallon Ruhaan dake shinshina wata powder daya lakata daga cikin kwalin. Rose powder, yafaɗa yana karewa kwalin kallo. Amsa Asadullah yayi yace yes and so, kamshin rose nima naji. Girgiza kai yayi yace Amira is allergic to rose. So someone sent it deliberately. Eh da gangan aka turo yafaɗa yana dauka pics and letter din da suka zube a kasan dakin. Pictures din accident site ne, da kuma pics din Humaira da Ammi dasu Zayn. Buɗe letter yayi ya fara karantawa kamar haka "This is a warning, abinda kike ƙoƙarin bincikowa karki fara, rayuwarki da rayuwar duk wani wanda ke tare dake tana cikin hatsari a yanzu haka" kallon juna sukayi shida Asadullah. Kallon Humaira yayi yace idan ta tashi kice mata nina tafi da sakon, yafaɗa yana ficewa da rinannun idanunsa.
Brother waitt, cewar Asadullah dan a yadda Ruhaan ya fice cikin ɓacin rai baison kuma mai zaije yayi ba.
Duk abinda suke faɗa Humaira najin su, amma ita abinda ya bata mamaki shine, miye Amira takeyi so dangerous haka?
Gabaki ɗaya ta kasa sukuni, a haka bacci ya dauketa.
Koda Amira ta buɗe idanunta Magrib tayi, cikin sauri ta sauke kafafunta daga kan kujerar tana recalling abinda ya faru. Duba sakon tayi ko sama koh kasa bashi a dakin.
Mai kike nema, cewar Humaira da motsin Amira ne ya tada ta. Nothing much tafaɗa tana ƙaƙalo murmushi. Stop lying Amii, miye kike yi? Mutanen nan are very dangerous da gani. Amiii mun haɗu da juna bayan shekaru 18 i don't want to loose you. Kibar duk abinda kikeyi dan girman Allah. Huci ta furzar tana daura hannuwanta a kugunta.
Sister listen to me carefully, abinda nasa a gaba yanzu na fara, wallahii sai dai ni in ga bayansu koh kuma su suga bayana. Amma dole insan abinda ya faru da Ummii. Ba accident mukayi fa, deliberately motar nan ta bige mu 18 years ago. Sai nasan waye ya aiko, kuma kan wani dalili ya aiko. Sannan idan ban nemo suba, su zasu kashe mu a banza muna kwance. Kuma ni Abbii bna fidda ran su suka kashe shi ba. Nasan ba accident bane Amii, amma stop whatever you're doing. Da mugun mamaki take kallonta tace kin sani fah sister? Yes i know tafaɗa itama tana kallon Amira. Taya kika sani? Abbii ne ya gayamin. Matsowa tayi kusa da ita tace mai yace maki? Bazan faɗa maki ba tafaɗa tana kallonta. Sisterrr please. Naji zan gaya maki amma kimin alƙawari bazaki sa rayuwarki a hatsari ba, kuma koh mai zakiyi sai kin gayamin nayi approving tukunna. I promise tafaɗa cikin sauri. Zan baki file din, file ne akan bincike da Abbi yayi.
Ina parcel dinnan tafaɗa tana kallon Humaira. Ruhaan took it. Why? Tafaɗa tana ɓata rai, bansani ba nima haka kawai yace ince maki shiya dauka. Wayarta ta dauka, for the first time after 6 years tayi dialing number shi na Nigeria.
Ruhaan ne zaune a studio dinshi, shida Asadullah. Kallon hotunan da Ruhaan yayi pining jikin board Asadullah yayi yace wow, you have really gone far.
Amma wannan Sa'ad Wambai din ba shine yaso yin maja da company dinsu Amira ba kwanaki? Yeah shine cewar Ruhaan yana kallon hoton Sa'ad Wambai dake cikin board din. Amma naga hotonshi cikin makusanta Alhaji Abdulkarim Kurfi (Abbii)
Yes, suna haɗuwa sosai dashi, kuna suna yawan waya.... maganar sace ta katse jin karar wayar a jikinsa. Ciro wayar yayi yana kallon sunan dake yawo akan wayar. Mamaki ne ya hanashi motsi, har sai da kiran ya kusa katsewa sannan ya dauka. Yasa wayar a kunne shi. Ruhaann tafaɗa cikin ɗaga murya, murmushi yayi ba tare da yace komai ba. Do i sound like a mad person to you ina maka magana kana min dariya? I didn't laugh yafaɗa yana murmushi. Koma ina kake kazo ka kawomin abuna daka dauka. Kizo ki amsa idan kin matsu yafaɗa yana kashe wayar. Da mugun mamaki take kallon kafin ta kwalla ihu tace how dare him? Nizai kashe ma waya? Ni Amira tafaɗa a fusace, address din studio dinshi ya tura mata. Wullli tayi da wayar tana jan tsaki. Murmushi Humaira tayi tace what happened? Ruhaan i will just kill him tafaɗa tana dafe kanta. You can't do that, you won't do that tafaɗa tana zaro. Smirking 😏 tayi tace and what made you think i can't do that? Causee... tafaɗa tana murmushi. Cause what cewar Ameerah tana kallon Humaira. You still love him. Pillow din dake kan couch din ta dauka ta jefi Humaira dashi. Auchh Amiii kaina na ciwo fah? Serves you right! Banson shi, banson shi, natsane shi tafaɗaa tana nuna Humaira da yatsa. Okay calm down tafaɗa tana murmushi. Huci ta furzar tana safa da marwa. Tagumi Humaira tayi ta tsaya kallonta, zakije ne? Cewar Humaira tana haɗiye dariyarta. I don't have a choice but i can't stand him tafaɗa kamar zatayi kuka.
Yanzu Mukkaram zai zo sai ya kaiki kuje ku dawo cewar Humaira.
Better Amira tafaɗa tana shiga bayi, ta dauro alwala tayi sallah.
Tana idarwa Mukkaram na shigowa. Yawwa Mukky please ka kai Amira ta amso sako, cewar Humaira. Tom sister idan ta shirya sai muje. Cire gyalen abayar dake jikinta tayi, ta saka hijab. Ba Humaira ba daidai da Mukkaram sai da yayi mamakin ganin Amira zata fita da Hijab. Miye kuke kallona tafaɗa tana haɗe rai. Babu cewar Humaira tana murmushi. Don't smile like that it's creepy cewar Amira tana hararar ta. Kowa ne irin ki mara fara'a cewar, idan ba nafiki fara'a cewar Ameerah. Let's ask Mukkaram cewar Humaira tana kallonshi, itama Amira ta kalleshi. Cikin sauri ya dauki wayarshi yace Amira ki sameni a waje mu tafi. Dariya suka fashe da ita.
Map Mukarram yasa na motarshi suka isa Studio din Ruhaan.
Kiranshi tayi har ya katse bai dauka ba, sai kuma ya biyo kiran. Ina waje tafaɗa a takaice. Bakida kafa ne? Ki shigo yana gama fadar haka ya kashe wayar. How dare he? Tafaɗa tana kallon wayar, dariyar dake cin Mukkaram ya rike dan yason itada Ruhaan ne.
Muje tafaɗa tana hararar Mukkaram dake dariya. No kije zan jira ki a nan. Wani mugun kallo ta jefeshi dashi sannan ta sauka ta rufo mai kofar.
Doorbell ta danna, buɗe mata Ruhaan yayi yace come in. Ni bazan shigo ba, kabani abuna in tafi. Kiyi ta jira yafaɗa yana shigewa ciki. Turo baki tayi, ta shigo ta tsaya tana kallon studio din. Hotunan mutanen da ta gani yasata sakin baki tana kallon ikon Allah. Idan kin gama kalle-kalle kishigo yafaɗa yana zama akan couch din. Shigowa tayi yace waittt yafaɗa da karfi...tsayawa tayi room slippers ya dauko a shoerack din dake gefenta ya ajiye mata. Change your shoes, rolling eyes tayi sannan ta chanza takalmin.
Zama tayi akan couch din tace banda time fah. Plus i don't like staying alone with strangers. Murmushi yayi yace i wanted to talk to you. Kuma this is the safest place,nasan da cewa da banyi haka ba bazaki zoba. Shiyasa ban aika maki da abinki ba, nace kizo ki karba. Imaann you should be careful please yafaɗa cikin seriousness. Stop pretending to care tafaɗa kwalla na taruwa a idanunta. Tsugunnawa a gabanta ya riko hannuwanta dake rawa. Ajiyar zuciya ta sauke, sai kuma tayi saurin fisge hannunta tace don't touch me again. Sorry my bad yafaɗa amma still yana tsugunne a gabanta. Yace your burden let's share it, put here yafaɗa yana miƙa mata tafin hannushi. I don't trust you, tafaɗa tana kallonshi. I know but...no but's i gave you my trust, my heart, my soul and body but what did you gave me in return. Butulcii!! You snatched away my right to see my dead daughter. I hate you for that and i will forever hate you tafaɗa tana hawaye. Wallahi ban tsaneka saboda ka sake ni ba tare dana maka laifin komai ba, saboda nasan aure rai gareshi, idan lokacin yin shi yayi za'a yi. Haka zalika idan lokacin mutuwarshi yayi zai mutu. I hate you for one reason, My Du'aa! Tafaɗa tana lumshe idanunta, hawaye masu zafi na fitowa. Share mata hawayenta yayi, kallonshi tayi tace don't touch me again. Ji take kamar ana watsa mata ruwan zafi. Okay I won't but koma miye i can explain but first you have to agree to share your burden with me. Idan kin yarda shikenan. What will you explain? Tafaɗa tana kureshi da ido. Duk wani misunderstanding din dakike dashi. I don't trust you, tafaɗa tana kallonshi. You do! Idan da baki yadda dani ba bazaki haifi yaran mu ba. Stopeettt! Tafaɗa cikin ɗaga murya, you don't deserve to be a father. Runtse ido yayi yana jin zuciyarsa na ƙuna duk abinda Amira take mai bai taɓa jin haushi ba koda na sakanni ne, sai yau sosai maganar ta shige shi. Jan hannunta tana cemai ya saketa yaki har saida ya kaita dakinshi, ya wullata kan gadon. What are you try to do tafaɗa tana kallonshi. Buɗe wardrobe dinshi yayi ya ciro wani album ya wulla mata yace kallii ki gani! Kalla yafaɗa a tsawace. Buɗe album din tayi ta fara kallon pics din. Duk hotunan shine yana Karami. Haɗe rai tayi tace mai zanyi dasu? Gabaki ɗaya yarinta none of my parents were there for me. I know how it feels, kina tunanin zan bari ya'ya na suyi experiencing kala wannan rayuwar? Ke kinsani burina nane in bama ya'yan mu duk wata kulawa da kuma gata. Why will you say that to me? I don't deserve to be a Father? Meerah am disappointed in you. Na dauka koda ace i don't deserve to be a Father, tunda har na riga na zama uban ƴaƴan ki. You will encourage me, but you're here accusing me and insulting me!
Komai zaka ce kace i said what i said and am not sorry about that...kuma bazan taɓa manta ka hanani ganin gawar Du'a ba. Stop it for goodness sake, Dua is not DEAD!! Yafaɗa yana naushin mirror dake dakin nan take ya fashe. Toshe kunnenta tayi, tana, zaro ido bata taɓa ganin Ruhaan ya birkice kamar yau ba.
Mai kace tafaɗa tana saukowa daga gadon, Du'a bata mutu ba tana ina tafaɗa tana riko collar rigarshi. Ashe bakada imani? Uwa zaka raba da yarta. Tafaɗa tana fashewa da kuka. Talk to me tafaɗa a tsawace! Nima bansan inda take ba yafaɗa a sanyaye.
What happened 6 years ago? Talk to me tafaɗa tana kallon shi.
Toh mu haɗu a next page 📄📄📄
Chapter 32 · 0% Book details